ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

“No karka damu, base yabani hakuri ba, wannan ai besan yayi laifi yabada hakuri ba, da na fadi kafar zan take inga ta tsiya”

Kallon da Jalal yayiwa Ahmad ba karamin batawa Yusuf rai yayi ba, dan da’a waje ne wani civilian din yayi musu haka, seya gane shayi ruwane, shibe ma san daga Ina wannan mugun dan jiji da kan yake ba.
Abdallah yace
“Yusuf kabi a hankali, wannan da kake yabata hakuri, in yaso se ya hana abaka Auren nan, sirikin kane ka bishi a sannu, yayan Mahmud ne daze Auri kanwarku Nana, kuma babban Aminin Jawwad”
Yusuf yace
“wannan din”?
“Kwarai Shidin”
Jalila dai ta fice waje, Ahmad ya biyo bayan ta,
“Jalila wai me wannan mutumin yake takama da shine da yakewa mutane kallon basu isa ba??”
Jalila tace
“ba kallon mutane basu isa bane, haka yake, haka halayarsa take, ka lura ko Mahmud da yake kaninsa baya kulashi sosai, Yaya Jawwad da Abdallah kawai yake shiga shirginsu”

“Amma meye hadinki dashi da ze dinga kallonki haka?”
“Ba wani kallona da yake, kaika ga hakan, bani da Abunda Jalal ze tsaya kallo, A lissafin Rayuwarsa baya shiga shirgin mata, koda ‘yan uwansa ne, muna gaisawane kawai saboda Aminin Yaya Jawwad ne”

“Kai queen, duk taurin kai da dagiyar namiji, baze iya dauke kai akanki ba, Amma me ya kai Jawwad abota da wannan bahagon mutumin”. “Amintarsu hadin Allah ce”
“to shikenan, abar maganar ya gajiya,? naga kunshi ki yayi kyau, kamar in saceki in gudu”
Murmushi tayi tace
“Tabdijan kaida Daddy kuwa, inka gudar masa da ‘ya”
Haka suka cigaba da hira, ya rakata har kofar part din Anty fido, sannan ya koma.
Tana shiga part din tabi ta babban parlour, bakowa a ciki ta nufi makwancinsu, tana shiga Hanan ta kalleta tace “daga ina haka?”
“Naje cikin gida ne, Yaya Yusuf yasakani aiki” Hanan bata kuma cewa komai ba, Maimakon su kwanta suka zauna sukayi ta hira, seda suka raba dare sannan kowacce ta nemi guri ta kwanta.

Washegari yakama ranar daza’a fara biki, ranar ne za’ayi kamu, iya mata da yamma, ko Angwaye bazasu gurin ba, iya mata ne a gurin kamun, , a wani katafaren dakin taro,
karfe biyar na Yamma, Amare suka iso dakin taron sanye da shiga irin ta fulani, Suka fito a ainihin usulinsu na fulani, ‘yan matan ma, duk kayan fulani suka sa, se manyan iyaye da suka saka Atamfar anko na kamu, karshen haduwa kam sunyita ba’ a magana, Sunyi kyau, Amara kirjin biki ma wato Jalila tayi kyau, ammata simple make up, gashi anmata ado da gashin kanta, sosai kayan suka karbeta, Anyi raye raye, anci an sha, an lika kudi, anyi hotuna da ‘yan uwa da abokan Arziki, anyiwa Amare kamu, ba’ a tashi daga gurin ba se karfe goma na dare, motoci sukazo suka kwashesu zuwa gida. A motar Ahmad Jalila ta koma gida, Jalila banda motar Jalal bata taba hawa motar wani ba se Ahmad, suna tafe yana yaba irin kyawun da tayi. Da suka koma gida ma a idon Jalal suka dawo, Jalila tayi kyau se hirarsu suke ita da Ahmad.

Tunda suka koma, Jalila bata tsaya tabi takan kowa ba, ta tafi part dinsu, Mummyn Hanan ce tazo ta samesu a dakin da suke zama, tace “Kuyi maza kuzo, Uwar mijin Nana tazo, kuzo muje ku gaisa”
(wato Salma uwargidan daddyn Hanan)
Jalila najin haka tace “nima bari in biku”
Ko kayan basu canza ba, suka bi bayan Mummy.
Koda suka shiga masaukin da’aka bawa Maman Mahmud kamshin turare ne ya gauraye dakin, tana zaune akan kujera, Jalal na zaune a kusa da ita, se wasu ‘yan mata, da kuma Antyn Jalal tana salla, da alama hira sukeyi da Jalal, kamarta daya da dan nata Mahmud, haka kuma tana dan yanayi da Jalal din, suka shiga da Sallama, ta dago cikin fara’ a ta amsa, Mummy Hanan tace “to Hajiya Salma ga yaran naki nan, sune Amaren”
Ta kallesu daya bayan daya, ta kalli Nana tace “ga sirikar tawa nan, ita nasan ta ai”
Sukayi murmushi suka durkusa suna gaisheta.
Jalal ya kalli Jalila tayi kyau sosai, Se murmushi takeyi, Hajiya Salma tace “Jalila baki sanni ba ko?”
Jalila ta Kalle ta ta jinjina mata kai, Hajiya Salma tace
“ni na sanki ai, kamar ki daya da mamanki, Amma kuma kusan duk kamaninku daya keda Amaren”
Jalal ya juya harshe sukayi magana da Hajiya Salma.
Nan ta shiga yi musu Nasiha akan Aure, da mahinmancin biyayyar Aure. Tana cikin yi musu ne Maama ta shigo, ta kawowa Hajiya Salma Abinci, nan suka hadu aka cigaba da yiwa Amare nasiha, Jalila kam ta kame tana sunkuyar da kai sekace itace Amarya. Jalal ma yana kusada Hajiya Salma ake musu wannan fadan, ko a jikinsa, be kula Jalila ba haka itama bata kulashi ba, tsakanin ta da shi se kallo.
Jin da Jalila tayi Hajiya Salma tana bayani da manyan bakake, Mummy Hanan ba ruwanta suka dinga yiwa amare fada, da koyar dasu zaman takewar Aure, ba shiri Jalila ta mike zata fice, Maama tace “Ina zaki kuma?”
“Amm… Zanje inci Abinci yunwa nakeji”
Sosai Jalila ta bawa Hajiya Salma dariya,
Tace
“dawo ki zauna, ina da magana dake dama” shiko gogan har akayi aka gama ba inda yaje yana zaune, daga karshe ma Abincin da aka kawowa Hajiya Salma ya zuba yafara cin Abunsa.
Yadda Jalal yake wa Hajiya Salma kamar irin dan Autan nan nata, kuma ga dukkan alamu tanaji dashi.
Seda aka gama yiwa su Nana fada, Aka sallamesu amma tace Jalila ta tsaya, suka tafi Maama ma komawa tayi, dan Akwai Ayyuka sosai a gidan, Maama na fita Jalal yabi bayanta, yace dan Allah yanaso a bashi tea.

Ya rage daga Jalal se Mummyn Hanan, Jalal da Hajiya Salma.
Hajiya Salma tace “Jalila me dana yayi miki ne?”
Jalila ta kalleta da alamar bata gane ba.
Hajiya Salma tace
“ABDUL JALAL mana babban dana kuma ďan Auta, kince bake ba shi, me yayi miki ne? Ba laifinsa bane, nasani laifin Mummyn sa ne, Amma kiyi Hakuri, Daughter Jalal yana jin maganar ki fiye da yadda kike tunani, Jalila Taimakon Rayuwar Jalal kike, Jihadi kikeyi, Allah ne kadai ze biyaki, karki duba abunda mutane zasu fada, kedai kiyi dan Allah, duk yadda muke da Jalal bana masa fada, idan nayi masa fada se yafara gaba dani ko wayarsa na kira baze daga ba, Amma da yake Allah ba yadda baya lamarin sa, kinga dake da Jawwad, musamman ke yanajin maganar ki, ban san me kikayi masa haka yake jin maganar ki ba” tai maganar cikin zolaya, sannaan tace
“Naji dadin ganin cigaban da aka samu a rayuwarsa ta bangarenki, ko danginsa babu wata wadda yake sakewa da ita kamar ke, yana jin maganar ki dukda shirin naku na Tom and Jerry ne”

Jalila ta sunkuyar da kai, Mummyn Hanan tace
“gaskiya nima yadda na lura da shi, baya son. Mutane sam, mussaman ranar da suka je mana can Kaduna, Amma dukda haka a nutse yake”. Hajiya Salma tace
“Wallahi sister badan kaddarar Rayuwa da ta faru da shi ba, yarona mutumin kirki ne, ki tambayi Jawwad kiji, Wallahi banga abunda bazan iya mallakawa Jawwad ba saboda dawainiyar da yayi dashi ba”
Mummy tace
“ke kika haife shine?”
Hajiya Salma tai murmushi tace
“Dan ex-husband dina ne?”
Zare ido Mummy tayi “Haba dai, duk abun nan bake kika haifeshi ba?” sukayiwa Jalila nasiha sannan, Hajiya Salma ta sallami Jalila, sannan suka cigaba da hira ita da Mummyn Hanan.

Tunda Hajiya Salma tazo, duk abunda take bukata sedai ta kira Jalila, duk inda zatayi kuma seta kira Jalila, kamar dama can sun san juna, Mafi yawan tattaunawarsu akan yanayi na Rayuwar Jalal ne, Sosai Hajiya Salma taji kaunar Jalila a ranta, Jalila tanada biyayya, da girmama mutane, ga kuma namijin kokarin da take akan yaransu Jalal.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button