ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

“Haba Jalila meye kuma na damuwa? Allah ya baku zaman lafiya, karki damu kinji” jinjina mata kai kawai Jalila tayi ba tareda tace komai ba.

Yau weekends ne, Hanan sun gama cin Abincin Rana da Jawwad, tana ta zuba shagwabarta yana biye mata, dan ba karamin birge shi wannan shagwabar take ba, yace
” Habibty Inaga ranar Saturday fa sister dinki zata tare”

“Wai Jalila?”

Jawwad yace

“eh ita, munyi waya da shi dazu da safe kina bacci, ya gayamin ya sai gida, an gama zuba komai ranar Saturday zata tare, inkuma sunki zeje ya dauketa ne kawai”
Dariya Hanan ta kama yi, Jawwad yace
“ya dai, ya naga kina dariya?”

“Akwai kura ne”

“Kura kuma? Meyasa kikace haka?”

“Hmm bakomai, gaskiya yakamata muje kano, zanso inyi kallon yadda wannan rayuwar masoyan zata kasance”
Jawwad yai murmushi yace “lafiya kalau zasu zauna”

“Hakane wuyatta su zauna guri daya, bari a jima in kirata, naga har yanzu bata da waya, se dai kabani taka in kirata”

Jawwad yace “Shikenan naga be bata wayarba har yanzu”

“nasan ze bata insha Allah”
Hanan ta mike ta tafi bedroom dinta.

Jalila tarasa meya kema ta dadi, wai ita ce zata tare a gidan Jalal, a matsayin matarsa, tanata tunane2, Amal tayi sallama, Jalila ta amsa, Amal tace “Anty Jalila, Mummy tace in kawomiki phone, your sister wants to talk to you”
Jalila a ranta tace ;kai yaran gidan nan sunfiye iyayi, ji yadda take magana kamar me koyon hausa
Jalila tasa hannu ta karbi wayar tareda cewa “Nagode”
Wayar aka sake kira Jalila ta daga wayar tareda fadin
“Salamu Alaikum”

Yanayin muryarta ze gaya maka tana cikin damuwa, Hanan tace

“Amaryar Yaya Jalal, ke ko kirana ba kyayi se idan nina kiraki ko?”
Cikin sanyin jiki Jalila tace

” kinsan bani da waya tun ranar dinner da ya karba be baniba, bana son yawan takura musu da karbar waya”

Hanan tace “hakane ya kike ya shirye2”

“shirye2 me?” Jalila ta tambaya

Hanan tace

“Ahhh Haidar yacemin ranar Saturday In Allah ya kaimu zaki tare”
Dan karamin tsaki Jalila tayi

“shine wani ya shirye2, ba wani shirye2 ni abun duniya ya dameni, ina tunanin irin zaman da zanyi a gidan nan”

“meye wani abun damuwa kuma? Karki dorawa kanki ciwo mana, Allah yabaku zaman lafiya yasa kina zuwa kiyi karo da shi”

Jalila tace “inyi karo dame?”

“ďan baba mana, nan da wata tara muzo suna” hanan ta bata amsa

Wani uban tsaki Jalila tayi “Ke kinfiye shirme wallahi”

“bawani shirme, Addu’a nai miki tagari”

“rike addu’ar ki bana so, ni ba haka naje yi ba”

Dariya Hanan ta dinga yi “Wallahi karya kike, abunda kikaje yi kenan, sekin cika masa gida da ‘ya’ ya duk shekara zaki dinga haihuwa”
Kashe wayar Jalila tayi, tareda yin dogon tsaki, inta biyewa Hanan bata mata rai zata cigaba da yi.

Shirye2 sunyi nisa, Hajiya Salma da Anty sun tsaya an gyara Jalila yadda yakamata, sun hada mata kayan turaruka daban2, Suka shirya mata kayanta a trolley. Ta wani bangaren Jalila tanata murna zata koma garinsu, ta cigaba da zuwa makaranta,

Anty tace “Jalila na cika alkawarin dana taba yi miki, ga turaruka nan, in sun kare ma kiyi magana se in hado miki wasu”
“to Anty na gode”
Abee yayiwa Jalila nasiha sosai, tareda yi mata fatan Alkhairi, yabata kyautuka na litattafan Addini dana zamani, sekuma kyautar system yace taje taita karatu. Jalila tai tayi masa godiya.

Hajiya Salma sunyi waya da Jalal, cewar zasu taho da Jalila gobe zasu tsaya a gidan su Jalila, sannan su kaita gurin Mummy daga nan akaita gidanta.
Jalal yace “gaskiya bana son ku kaita gidan Mummy, dan seta bata muku rai, kawai ku kyale ta”

“A’a Jalal baza’ayi haka ba, Mahaifiyarka ce akwai bukatar a sauke hakkinta na uwa, yakamata ta sawa Aurenka Albarka”

Jalal yace “Shikenan yadda kuka gani, Amma ni a gurina babu bukatar hakan.

Ilham bata taba sanin tana kaunar Jalal ba kamar yanzu, gaba daya kishi ya hanata sukuni ko Abinci bata iya ci, ita a tunanin ta tana so tayi soyayya da Jalal ne dan cika burin mahaifiyarta, Amma yanzu ta gane kaunar Jalal tayi mata illa, bata bacci sam, yadda taga rana haka taga dare, wai Jalal ke gaya mata shidin mallakin Wata mace ne, macen da ta dade tana cusa masa miyagun maganganu da cin mutunci amma saboda bashi da zuciya yake fadin shi mallakin ta ne, hawaye ne ya gangaro daga idon Ilham tace “Wallahi Jalal muddin baka Aureni ba sena fitini rayuwar Auren ka, sena uzzurawa rayuwarku, se Gidan Auren ka yazama kurku ta fishi ‘yanci, idan har kuka ji dadin Aure ba Saudatu ce ta haifeni” ta cigaba da kuka da surutai a daki.

Jalila se murna take zata koma Kano, koba komai zata dinga zuwa makaranta ta rage kadaici, karfe goma sha daya na safe suka shirya, Anty, Hajiya Salma, Husna, da wasu daga danginsu Jalal suka taho yiwa Jalila rakiya Kano,
Se kusan karfe hudu na yamma suka iso, Maama ta san da zuwansu dan haka ta riga ta shirya komai, har ‘yan uwanta da makwabta ta sanar, bayan sallar magariba za’a raka Jalila gidanta.
Jalila tayi murna ganinta a gida, Abba yayi murna yadda yaga Jalila tayi kalau da ita tayi fes kaman wata matar hamshaki. Dakinsu taje komai yana nan yadda ta barshi, kewar Nana ta dinga ji a ranta, tana tuno abubuwa da dama da ya faru a wannan dakin, wasu ma farinciki wasu na bakinciki. Maama tazo ta sameta tace

“Jalila ki debi duka abunda kike so akayanki, wanda zakiyi Amfani da shi nan kusa se a tafi miki dashi”
“to Maama zan diba Insha Allah”
Sukaci Abinci sukayi Sallolin da ake binsu.
Anty tace “Jalila yakamata ki shirya muje a kaiki gurin uwar mijinki, kar dare yayi sosai”
Ras gaban Jalila ya fadi! Jikinta yafara Rawa, ta shiga duniyar tunanin wace irin karba Mummy zatayi mata.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta Amsa, seda takuma wanka ta canza kaya, suka nadeta a cikin lafaya, se kamshi takeyi Maama ta kama hannunta ta kaita gurin Abba, ya dinga mata nasiha da Addu’a, Jalila se kuka take, yadda Abba yaji rabuwa da Jalila beji haka akan Nana da Jawwad ba, yana matukar tausayinta. Bayan ya gama ne Maama tayi mata ‘yan nasihohi da Addu’a, dan sosai take jin kunyar abubuwan da ta aikatawa Jalila.
Wasu daga cikin’ yan rakiyar amarya sunyi gaba dan suje suga ďaki, Yayinda Hajiya Salma da Antyn Jalal suka nufi gidan su Jalal Da Amarya Jalila.

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
……???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣3️⃣ 106

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button