ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP ???? ???? ???? ???? ???? ???? inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku ????????????????

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.

???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
_PAGE 3️⃣0️⃣83

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

      _MY FIRST NOVEL _

Hanan takuma dawowa zata wuce
Abdallah yace “Auta bakiga Jawwad din naki bane” dan kallon Jawwad tayi, tayi murmushi tace “Naganshi mana” Naja kamewa tayi a gurin musamman dataga Jawwad yana kallon Hanan, da alama beji dadin yadda Hanan taki kulashi ba.
Abdallah yace “Wallahi Hanan totally dinta se a hankali, duk ta takuramin wai muyi Sauri muzo taganka amma ta ganka ta wani basar” Jawwad yai murmushi yace “Kyaleta Abdallah zamu shirya ne, maybe gajiyar Hanya ne ya hanata yimin magana”
“Bawani gajiya tsabar wulakanci ne kawai” Hanan ta murgudawa Abdallah baki, suna hada ido da Jawwad ta kashe masa ido daya, gaba daya ya rikice, gani yake kaman kowa yaga Abunda Hanan tayi gaba daya yakasa sukuni,
ita kam Hanan ta wuce Naja takoma inda tabar Jalila a daki, ba kunya Naja takuma biyota dakin, Hanan tana shiga tace “Ohh God, Jalila Haidar yakara kyau yakuma zama babban mutum, wayyo dadi kasheni, naga farincikin zuciya ta” Jalila tace “Waye kuma Haidar?”
“So kike indinga kiransa da sunan da kike kiranshi ne, kowa yace Yaya Jawwad nima ince Yaya Jawwad, Haidar dai kaman in sace shi in gudu haaka nakeji, yawwa Queen ranar muna waya dake naji wata namin kashedi akan abunda yake mallakina, wacece dan Allah?”
“Nice nan, kuma wallahi duk maitarki iyayenmu sun tsaida magana, bashida wata mata in baniba, mayun banza dana wofi marasa zuciya” Naja ce taketa fiffika tana fadan maganganu Hanan taja wani dan tsaki tace
“Jalila aina dauka wadda take cewa zata auri Jawwad din mace ce, ashe mata maza ce mata ta rako duniya, ke cewa akayi ya Aureki, nikuma Jawwad yana sona ne” , dan saurin kallonta Jalila tayi, lokaci da dama Jalila tana daukar abunda Hanan take a matsayin wasa, dukda tana ganin tsagwaron gaskiyar abunda Hanan din ke nufi a idonta Jalila na cikin wannan tunanin Hanan tace “zan tabattar da hakan anan kusa ba a nesa ba, ke Queen ina mutuminne tunda nazo ban ganshi ba”
“Wakenan?”
“kinfini sani, Jalal mana” tsaki Jalila tayi tace “Nifa bana son maganar wannan shirmammen”
“Jalal dinne shirmamme?”
“Eh shidin, ke Akwai Labari amma semun je bauchi Lafiya insha Allah”
“To Allah ya kaimu lafiya”

Abdallah yace “Jawwad nikam ina Jalal ne naganka kai kadai?” Jawwad yace
“Yana part dina baya jin dadi”
“Allah sarki, muje inganshi, muyi salla Azahar sannan mu wuce”
Suka tashi suka tafi part din Jawwad, suka tarar da Jalal zaune akan kujera, yana kallon TV amma sam hankalin sa baya kan Tv, shigowarsu yasa ya daga kai, murmushi yayiwa Abdallah, ya mika masa hannu suka gaisa
“Jalal ashe bakaji dadi ba? Sannu gaskiya ka rame, Allah ya sawwake”
“Abdallah aini na warke tuntuni, Jawwad ne da zuzuta abu”
Jawwad yace “Au ni nake zuzuta abu, dadinta kallo daya za’ayi maka asan baka da lafiya” sukayi Salla, suka zauna sukayi ta hira, Jalal ya sake sosai.
Can aka jima Abdallah ya kira Hanan a waya yace su fito yanzu zezo su tafi, Hanan tace masa to, Jalila ta nunawa Hanan akwatinta tace “Hanan kaimin mota, bari in sa kaya” Nana tace
“bari inje ingayawa Abba zaku tafi” Hanan ta ja trolley Jalila ta kai bakin mota, amma motar a rufe, tasan Abdallah suna part din Jawwad kanta tsaye ta tafi part din, tundaga waje take iya jiyo hayaniyarsu, shiga tayi da sallama duk suka amsa mata, ta fadada murmushin fuskarta ta Kalli Jalal tace “Yaya Jalal kwana dayawa, Yakake ya gida amma naga ka rame sosai” shima murmushi yayi mata yace “lafiya kalau Hanan, amma aini hakanake dama can ban rame ba, yagida ya hanya?”
“Alhamdilillah, ina wannan kanwar taka, yama sunanta?”
Abdallah yace “Kai Aku me magana, daga zuwanki kinfara zuba kaman kanya”
Dan hade rai tayi “kace mufito kuma ka kulle mota, ga kayan queen can na fito dasu, kazo ka bude in samata a mota”
“Sedai kizo ki karba kibude, bari mugama hira”
“Gaskiya Abdallah ka dinga jin tsoron Allah muka katse namu hirar kace mu fito kaikuma ka zauna”
Taki kallon inda Jawwad yake, balle yasaka ran zata kulashi, Jawwad ya karbi key din motar a hannun Abdallah yace
“muje in bude miki motar, Abdallah bashida niyyar tashi yanzu”
Dan murmushi tayi ta juya, Abdallah yace “tasamu abunda takeso, dama ba dan Allah tazo nan dinba, sarkin gulma wani inzo in bude mata mota, kawai kice Jawwad yataso gurinsa kikazo, sewani Iyayi kike”
Hanan taji kaman kasa ta bude ta shige, Abdallah mugun dan rainin hankali ne Jalal yace “Ahha kai Abdallah ina ruwankane? Yada shishshigi haka?”
“Auto nayi shiru, tunda ka goyi bayanta”
Suna fitowa Hanan ta nufi hanyar komawa cikin gida, Jawwad ya kira sunan ta, ta tsaya amma bata juyo ba, ya karasa gabanta yana kallon ta amma ta sunkuyar da kai,
“Hanan, menayi mikine? Tunda kikazo kin kula kowa amma ni kin shareni”
“Bakomai”
“Ban yadda ba komai ba, laifin menayi miki?”
“Haidar dan Allah ka kyaleni, banason matsala, kace baka sona, gaa nazo na tarar da wata tana gayamin ita zaka Aura ya zanyi? Ina kokarin in cireka a raina amma nakasa, ganinka din nan ma yana karamin pressure ne, na damu da kai sosai kaikuma ka nuna baka sona, base in hakura ba, mezesa incigaba da shishshige maka?” Abun mamaki hawaye ke kokarin fita a idon Hanan, hakan na nuna maganganun da take fada har cikin ranta, Jawwad yace
“Zannemi wata alfarma daya a gurinki, zakiyi min? “
“Alfarma kuma? Wace iri”
“Sekinyi min Alkawari zakimin Alfarmar”
“Inkuma bazan iya bafa?”
“Bazan tambayi abunda bazaki iyaba ai, abune me sauki”
“To fadi in zan iya” yai murmushi yace
“Sonake inkuma jin sunan dakika kirani dashi please, yanamin dadi”
Dan zumbura baki tayi ta noke kafada, “Niba wani suna”
“Kince fa zakiyi min Alfarma” cikin shagwaba tace
“ni banyi Alkawari ba ai”
“Please, ko inyi kuka ne sannan ki fada”
“Eh to yi kukan in gani tukuna” sukayi dariya a tare, yanayin irin tsokanar Jalila haka Hanan takeyi, amma Hanan bata iya komai ba akan Jalila, Jawwad yace
“Hanan da bakina ban taba cewa bana sonki ba, ban taba soyayya ba, amma nasan ina son Jalila so ba na wasa ba, kinga akwai alaka me girma tsakanin ki da ita, sannan batun Naja da kikeyi Wallahi Hanan yanzu haka ina dauriya ne kawai, Naja zabin Maama ce, tanason in Aure ta ni inason yiwa Maama biyayya amma bana tunanin zan iya Auren Naja,
Hanan nasan kinshiga damuwa saboda ni but am very sorry, banason kowani rai ya shiga damuwa saboda ni, ta mussaman ke ce a gurina” Hanan tai murmushin da seda hakoranta suka fito, ta jingina da motar tace
“Kasan meyake kara burgeni da kai Haidar?”
“A’a sekin fada”
“A dukkanin maganganun ka kana kokarin fadar gaskiyane, sannan kanada tausayi shiyasa nake kara sonka, Amma bari ingaya maka wani abu, alakar dake tsakanina da Jalila bazan so ta baci ba, saboda ina mata so na gaskiya, bazanyi wani abu in cutar da ita ba, Amma maganar gaskiya kanawa Jalila so ne irin na ‘yan uwantaka ba soyayya ta Aure ba, haka ma zuciyar Jalila tana maka sone na’ yan uwan taka, nasan zakayi mamaki, Jalila bata taba soyayya da wani ba, tanada Samari Amma har yanzu taki yadda zuciyarta akwai wanda takeso saboda taurin kanta, kaima zan baka lokaci zaka gazgata abunda nake nufi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button