ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Please pray for me zanfara exams, dana kammala zan cigaba da posting insha Allah
Comments nakeso ba sticker ba kokuma just thanks

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680

.????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 16️⃣ 69

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

    _MY FIRST NOVEL _

WANENE ABDUL JALAL???!!!!!

Khadija munir shine cikakken sunan mahaifiyar Jalal, malam munir shine mahaifinta suna zaune a unguwar dorayi dake cikin garin kano, malam munir malamin makarantar secondary ne, sannan yana yan sana’oinsa domin rufawa Iyalansa asiri, yanada mata uku, hauwa itace uwargida, se sadiya itace matarsa ta biyu, da zulaihat itace matarsa ta uku, yanada yara goma sha uku, khadija ‘yace ga sadiya matar malam munir ta biyu, khadija su ukune agurin mahaifiyarsu, itada yayyenta maza biyu, Abubakar da Aliyu, itace yarinya ta tara a gurin mahaifinsu, khadija tana da kyau daidai gwargwado, wanda har wasu suke cewa duk tafi yaran gidan kyau, dukda kasancewar ta ba fara tas ba amma tanada kyau, khadija yarinyace mara kunya, bata dagawa kowa kafa, duk wanda yayi mata duk yarintarsa duk tsufansa zeta cimasa zarafi babu ruwanta, tun yayyenta na kamata su daka intayi rashin kunya harsuka gaji suka kyaleta, saboda rashin mutuncin ta bata bar kowaba ciki harda matan babanta da yayyenta, mahaifiyarta ta sangarta ta kasancewarta ita kadaice yarinyarta mace, duk wanda ya daki khadija ranar se anyi tashin hankali da mahaifiyarta, har kirari takewa khadija cewa “ni ‘yata matar manyace, se wanda yaci yatada kai zan bawa, dan khadija na ba kalar talakawa bace” hakan yasa abun yafara tasiri a zuciyar khadija tun tana yarinya, takejin cewa kota isa aure seta samu me kudi zatayi aure idan kuwa bata samu me kudiba, gara ta tsunduma ita tanemi kudin dan bazata iya auren talaka ba, kuma batason rayuwar wahala.
indai khadija nason abu, kaya kona uban waye koda kudi ko a bashi, mahaifiyar khadija zata siyamata su.
Saudat kanwace ga khadija sakuwarta ce khadija tabata shekara daya da rabi, ita saudat ‘yace ga zulaihat amaryar malam munir, itace ta biyu a dakinsu, wani lokacin suna matukar shiri ita da khadija saboda halinsu yazo daya dukkaninsu tsagerune, Sedai Khadija tadama saudat ta shanye a tsageranci, dukda wannan shiri dasukeyi baya hana in tsiyar khadija ta motsa tayiwa babar saudat rashin mutunci a hadu aita masifa a gidan nan, makaranta da yan unguwa babu wanda besan halinta ba, karamin aikintane ta zagi malami agaban dalibai, in an koreta mamanta seta canza mata makaranta, dama islamiyya tuni ta dena zuwa, a cewarta tunda tasamu na salla shikenan, dan bazata jure wannan masu gemun kaman brush suna dukan kyakyawar fatarta da fatar bunsuru ba, abun dukan doki, malam munir yayi iyayinsa gurin ganin khadija ta nutsu amma abu yaki yuwuwa,
Abinci se wanda taga dama zataci, sutura se wadda takeso zata saka, wani wanki da guga almajiri uwatta take biya yayiwa khadija, haka dai rayuwar khadija ta tashi a mugun sangarce, ga rashin tarbiyya.
Tun tana jss2 tafara samari, inda a nan ne ta hadu da saurayinta Kabir, Kabir yana matukar sonta kaman yayi hauka, Kabir marayane, mahaifinsa ya rasu, dagashi se mamansa da kannensa mata biyu, shikadaine namiji gashi mahaifinsa bebarmusu wani abun kirkiba se gidan dasuke ciki, seyaje yayi aikin wahala yake samo abunda zasuci yake biyan kudin makarantarsu, tunda yafara soyayya da khadija abubuwa suka fara tabarbarewa saboda yawan bani2, yazamana da kyar yake iya morawa mahaifiyarsa da kannensa wani abu sedai yayiwa khadija haka yadinga dawainiya harta shiga sss, nan manyan mutane suka dinga fitowa suna sonta, duk cikin manemanta babu wanda yayi mata saboda ita burinta ta auri, namiji kyakyawan gaske sannan wanda ya tada kai da naira, sannan tanada burin tazaga duniya, tayi ilimi me zurfi a kasashen waje, yadda zata goga kafada da manyan mata a kasar Nigeria dama nahiyar Africa gaba daya, shiyasa duk wanda yazo indai yanada kudi zata wankeshi son ranta sannan ta sallemeshi, dan har yanzu bataga dai dai da itaba, malam munir yayi iya yinsa dayimata nasiha itada yar uwatta saudat amma abu ya gagara, ana cikin wannan haline Allah yayiwa malam munir rasuwa, mutane sunji mutuwarsa saboda mutumin kirki ne kwarai dagaske, bayan an gama makoki khadija tacigaba da tsiyarta daga inda ta tsaya, ganinda Kabir yayi masu kudi na neman aurenta yasa kara zage damtse, dayasamu kudi ko anmusu albashi dayake yasamu aiki a wani kamfani, seyaje ya kashewa khadija su, har rawar jiki yake wasu kudin sushigo yakuma kaimata, alhalin gidansu wataran se a kwana biyu ba a dora tukunya ba, se ayi term biyu ana korar kannensa saboda kudin PTA, amma baze iya basu ba sedai khadija.
Mahifiyar Kabir ta zubda hawaye ba’adadi amma bayadda ta iya da wannan hali na ko inkula da danta Kabir yake musu itada kannensa, sam takasa gane kansa.
In khadija ta dau wanka ta taho seka dauka wata yar hamshakin Attajiri ce, saboda ‘yar kwalisa ce ga karya data dorawa kanta, khadija tayi candy amma taki cigaba da makaranta tace seta auri mekudi zataje abroad tacigaba da karatu, sabida abun kunyane a ce nan gaba intazama wata a Nigeria ace za’ ayi interview da ita tace a Nigeria tayi karatu.
Yauma yammace taci uban ado tana taku kamar tana taka kwai, taji anamata horn da babur amma tayi banza taki matsawa, mutumin yadinga horn amma taki ko daga kai balle tabashi hanya ya wuce, parking yayi ya kalleta yace “baiwar Allah kokurma ce ne? Inata horn kibani hanya zan wuce amma kinyi banza” wani mugun kallo tayi masa, “idanni kurma ce kaikuma mara hankali ba” zaro ido mutumin yayi saboda yasan a haife ya haifi wannaan yarinyar
“nine mara hankalin yarinya?”
“kwarai kaine mara hankali, ya za’ayi ina tafiya zaka isheni da horn da wannan rubabben gwangwanin naka, kana nema ka kashemin dodon kunnena, aida seka tsaya in wuce, kokuma ka canza hanya, tunda bakai ka gina hanyar ba ai”
“Amma kina ganin ya dace ki kirani mara hankali da girmana da komai”
Cikin tsiwa tace “to semenene? Ai abun rashin hankalin kayi”
“shikenan in abunda kikayimin dai2 ne za’ayiwa mahaifinki kiji inda dadi”
“to ya mutu wata uku dasuka wuce, inkuma kabarin za’abishi ayi masa se inji, aikin banza mutane suyita abu kaman wasu yan kwaya”
Cikin rawar murya yace “nine kaman dan kwayan”?
“kaimana da dawani nake, wayasanima ko ita kaje kasha, kake nema kayimin akuya nonsense” tayi gaba abunta, mutumin nan seda ya zubda hawaye, ya kunna babur dinsa yazo daidai saitin khadija ya tsaya ya kalleta yace “Insha Allah sekin haifi dan kwaya, sekuma ya miki abunda kikayimin”
“kai kasani, koma kwayar zan haifa, shirmen banza kawai, adai dinga kula, da irin kwayar daza’asha in bahakaba a kare a gidan mahaukata” bataji mezece ba tayi tafiyarta.
A fusace ta shiga gida tana ta mita, saudat na tsakar gida tana danna waya, ta dago ta kalli khadija tace “Ahh kaga manyan mata a gidan Kabir ya akayine, waya taboki kike mita?”
A wulakance khadija ta kalli saudat, “waye kuma kabir, karki kara hadani da wannam matsiyacin, a tunaninki mace mai daraja kamarni zan iya auren wani Kabir, tausayinsa kawai nakeji wanke dan banza zangama, da zarar nasamu my dream hubby inyi dumping sha3 aside inyi aurena, idan na auri wannan fakirin ta ina burina ze cika” murmushi saudat tayi, “angaisheki matar manya, banga laifinkiba, nima ina bayanki wayakeso talauci ai kudi kawai alaji, amma meya bata miki rai haka?”
Nan khadija ta gayamata abunda yahadata da wannan mutumin, saudat tace “ke manta dashi, kinsan irin wannan mutanen, basa raina abun magana”
“aikuwa yajawa kansa dan sedana masa rashin mutunci naji dadi a raina” sukayi shewa gaba daya, uwar gidan malam munir tana jinsu tace
“khadija baki kyauta ba abunda kikayi”
Khadija ta murguda baki “ai dama banyi dan in kyauta ba, kinganni ba ruwana, da kusanci, ko girman mutum ana mun nake ramawa ehee”
“to Allah ya shirya”
“Ameen ya shirya abunda yafi hakama”.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, khadija tana gwara kan samari, yau ta wanke wannan gobe ta wanke wancan, ba wanda yake da ikon yin Magana, gefe dan wahalarta wato kabeer yanata faman wahalta mata, uwarsa da kannensa kuma ko oho.
Yau ake sa ran za’a kawo kudin auren kanwarsu khadija, wato surayya babbar yayarsu maryam tanatayiwa khadija da saudat fada akan su tsaida miji sudena wannan shiriritar, zumbura baki khadija tayi “waike Anty Maryam akanki muke zaune ne? Duk kinbi kin ishi mutane, itakanta surayya guda nawa take za’ayi mata aure, yarinya da kuruciyarta shekara iyanzu ta haihu, ga mijin shiba kudi ba, gaba wani ilimi me zurfi duk tabi ta tsofe da wuri” bude baki Anty Maryam tayi “lallai sannu khadija, surayya ce tayi yarinta da aure, kuma shi arziki na Allah ne ai, sannan ita ya mace darajarta shine dakin mijinta, ba gararamba a layi tana tara samari ba”
“eh ansan arziki na Allah ne amma ba wanda yakeson talauci ai, tara samari yanzu muka fara semun wankesu munci rabonmu mayi auren”
Saudat ta kwabe baki sannan tace “batta ai ita na fuskanci so take kowama yayi rayuwar wahala kaman yadda tayi, kuma babu wannan zancen”
Anty Maryam dataga abun nasu dagaske suke tace “to Allah ya baku hakuri matan masu kudi”
Khadija tace “Ameen Anty Maryam, Allah yabamu mutemakamuku tunda ku baku da rabo” suka kyalkyale da dariya itada saudat. Ana haka sega surayya ta shigo dakin goye da yarinyar Anty Maryam tace “Anty kinga humaira tayi bacci a bayana gaskiya na iya raino” Anty Maryam tace “Aikuwa dai kin iya raino, badi iyanzu in Allah ya kaimu Insha Allah kinkusa haifar naki” rufe ido surayya tai tace “gaskiya inajin kunyarki Anty maryam amma dai Ameen” dan zaro ido khadija tayi “au kekinayin auren zaki zage kiyita barin yara sekace kazar hausa”
Saudat da sauri tace “ganemin hanya dai”
Surayya tace “to meye a ciki yaya khadija, yara rahama ne bakasan wanda zaka huta dashi ba”
“Ai seki zage kibada himma, ga auren talaka ga haihuwa, nan da nan ki ragwabe akasa banbance tsakaninki da mamanki, kinga bari in tashi in je in abunda yake gabana wannan batamin rai zatayi” khadija ta fice daga dakin, Anty maryam ta girgigiza kai “Surayya kyale wadannan sunyi nisa basajin kira, se fatan Allah ya shirya”. Haka rayuwa tacigaba har akayi bikin surayya, yayinda su saudat duka dorawa ransu dogon buri musamman khadija, bata saurarawa duk wani saurayi da yashigo hannunta, duk tsiyarka duk arzikinka seta wankeka sannan ta sallemaka, amma duk da haka tana tare da Kabir, sha wuyanta kuma yana cigaba dayimata hidima iyakar yinshi, ya wofantar da mahaifiyarsa da kannensa.
Kawayen saudat sun san khadija sosai, duk da kasancewarta me izza da jin kanta, ko kawayen kirki khadija bata da su se yaran manyan masu kudi, yaran masu kudin ma se yarinyar da akasan ubanta wanda ya tara dukiya sannan tayi kawance dake.
Ranar wata laraba suna zaune, saudat tayi bakuwa, kai daganin yarinyar kasan kudi sun zauna, saboda ba tayi kalar wahala ba, motar da aka kawota ma a ciki ba karamar mota bace, kawar saudat din me suna Salma ABDUL JALAL Tajudden, kawar saudat ce sosai tasanta da dadewa dasuka hadu a gurin wani biki, khadija tanajin sunan salma a gurin Saudat, tana bata labarin kudin da familyn su salma ke dashi, bayan Salma sun gaisa da mutan gidan, taciro iv card a Jakarta ta bawa Saudat tace “ga iv din nan, saudat dan Allah kizo gurin bikina saura three weeks” saudat tace “Insha Allah zanzo, ashe abun yazo yama za’ayi kice bazanzo ba bayan nayi duk ankon bikinki”
Salma tayi murmushi tace “Ainasan halinkine saudat, yanzu in bakiga dama ba sekice bazaki ba”
“zanzo Insha Allah”
“kinga bari inyi sauri, akwai guraren danake son zuwa, se anjima” har Salma ta mike zata tafi, khadija tace “Salma ni baza’a gayyaceni ba, anyway ina miki murna Allah yasanya Alkhairi” murmushi salma tayi “ni na isa, kema ga naki, ina gayyatarki yaya khadija” ta mikawa khadija iv, tasa hannu ta karba, bayan fitar Salma suka duba iv din nan, kwana bakwai cif za’ayi ana bikin nan, khadija tace “Saudat wai ita kam wannan wazata aura haka”
“mhmm yaza’ayi insani khadija? Najidai ance dan uwanta ne, boyeshi take kaman ciwo batason aganshi, iya sanina da ita tana son gayen nan kaman ranta, ko sunansa bata fada, kinga jikin iv dinma sunan tane kawai, Allah ya kaimu bikin dai muje muga wazata aura haka”
“Ainima dole inje bikin nan, dan naga alamar irin bikin da nake sone, dan haka dole a kece raini, muyi wanka kaman yaran senetes, inje inyi sababbin kamu” dariya sukayi gaba daya suka tafa. Kafin lokacin bikin Khadija tasa Kabir a gaba, seda yasamomata kudi kusan dubu arba’in ta sai less din dinner, ta dinga bin samarin ta, tana karbar kudi a gurinsu da haka seda ta sai komai sabo, tayi anko kafin lokacin bikin nan
Ranar da’aka fara biki, khadija da saudat sun dau wanka, kaikace sune dangin amaryar, khadija takira wani saurayinta yazo ya daukesu a tsaleleliyar motarsa, ranar kamu da bridal shower, da mother’s evening duk ango bezoba, amma anci an sha, anyi barin kudade, kai dagani kasan wannan family sunci sun tada kai, naira ta koka a wannan bikin, gasu kyawawa kaman su sukayi kansu, daga mazansu har mata, gasu dayawansu ba farare baneba amma sunada matukar kyau, sunada dogayen hanci mazansu da matansu, wanda hakan ze tabattar maka family dayane, saboda suna kama da juna, khadija tayi samari a gurin bikin nan, saboda tayi kwalliya tayi kyau harta gaji, kaman uwa daya uba daya suke da amaryar, bangaren saudat ma hakane tasamu samari a gurin bikin.
Ranar dinner hall ya cika taro yayi taro, manyan mutane maza da mata daga bangarorin Nigeria sun halarci bikin, Mc yabada announcement cewar ango da amarya zasu shigo, nan aka shiga yimusu kirari “Ango Alhaji Habib kamal tajudden, matashin Attajiri me ji da kansa, me gwalagwalai da zinare, Ango kayi dacen amarya hajiya salma ABDUL JALAL Tajudden, me kyautar zinare da dama hagu bata saniba, me ado da sarkar zinare, abu naku maganin a kwabeku” haka aka cigaba da yimusu kirari tareda saka musu kida flower girls ne suka fara shigowa, se wasu kyawawan ‘yan mata sannan ango da amarya a tsakiya.
Amarya da ango sun hadu, sunyi kyau harsun gaji, tunda khadija tayi tozali da angon nan tarasa nutsuwarta, ya hadu karshen haduwa bata taba zaton akwai kyakywa a maza irinsa ba, da farine toda tabbas zaka iya rantsewa kace bayajin hausa, wannan shine irin mijin datake tsarawa zuciyarta tana son aure, wanda bata taba zaton ganinsa a gaske ba, Habib ta maimaita sunansa a hankali kaman yadda taji Mc yafada dazu, gumi taji yana tsatstsafo mata a goshi. Shikam ango se fara’a yakeyi cameras kota ina se hotuna akeyimusu, Saudat ta janyo hanun khadija sukaje suka dinga hotuna da ango da amarya, bayan sun dawo gurin zamansu ne saudat tace “khadija kinga wannaan bawan Allah kaman shi yakera kansa, dan Allah ga kyau, wallahi yafita kyau sosai” da kyar khadija tace
“mhmm aikam dai yana da kyau” duk bata cikin hayyacinta, haka aka gama dinner din nan aka watse, a hanya khadija tacewa saudat “Sauda amma Salma ba hausawa baneba ko?”
“eh to rabinsu hausa rabinsu kanuri, yan borno ne, kasuwanci yakawo wasunsu kano”
“lallai kam, gasu da kyau gasu da kudi” haka suka cigaba da hira har sukaje gida,ranar khadija kwana tayi tana tunanin habib, tareda mafarkinsa.
Suncigaba dazuwa gurin bikin nan har akayi akagama. yayinda kullum khadija insukaje suka dawo, soyyaya da tunanin habib ya cigaba da ninkuwa a zuciyarta.
Ranar daza akai amarya, juyin duniya saudat tayiwa khadija akan suje kai amarya tace bazata ba, tun tana lallabata har itama ta hakura tace tafasa zuwa gurin kai amaryar, taje daga baya, in Salma ta tare. Ranar Khadija ta kwana da matsanancin kishin Salma, kasa bacci tayi daren ranar dan tayi mamaki yadda kaunar habib ta mamaye zuciyarta lokaci daya haka, haka ta kwana sake2 da tunani har gari ya waye. Koda gari ya wayema bata fito tsakar gida ba tana tana kan gado tana juyi Saudat ta shigo dakin tazauna gefen gadon ta kalli khadija tace “yar uwa tashi muyi wata magana kibani shawara dan Allah” khadija ta kalli saudat idonta duk yayi ja alamar rashin bacci, ta mike zaune ta dan yatsina fuska ta kalli saudat “fadi inajinki?” Saudat ta gyra zama tareda kallon khadija sannan tace “Khadija nifa tunda mukaje bikin salma, nayi ido hudu da mijinta naji wallahi inasonshi, shiyasa nazo kibani shawara yazanyi, Dan gaskiya bazan iya hakuri ba, bazan iya auren kowa ba seshi, dan Allah sister bani shawara ta ina yakamata in fara?”
Gaban khadija ne yafadi, zuciyarta ta shiga bugawa da karfi, ga wani gumi dayake tsatstsafo mata a iya goshinta, taiwa Saudat wani irin kallo, sekuma tayi murmushi seda hakoranta suka fito, ta kalli saudat” Kin tabatta kinason Habib? ” da sauri Saudat tace” Wallahi khadija so bana wasa bama, wallahi ina sonshi, aurensa nakesonyi” khadija ta gyada kai takuma yin wani murmushi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button