ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Da sauri ta ɗago tana kallon Jalal, Amma ba tayi magana ba.
Ta wani fannin Jalal gaskiya yake faɗa, Mummy wata irin mace ce ma kafiya da taurin kai, gata da riƙo wata irin zuciya ce da ita yanzu take ganin lallai Daddy yayi haƙuri a zaman sa da Mummy.

Daddy ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo da sallama.
Amsa masa sukayi tareda gaishe shi, yayin da Mummy ta juya baya ta rufe idon ta, gefen gadon daddy yaje ya zauna ya kai hannun goshin Mummy yace
“Sannu deejah me yake damunki haka?”
Shiru tai ko motsawa ba tayi ba balle tai masa magana.
Ƙara matsawa Daddy yayi ya riƙo hannayen ta yace “deejah fushi kike dani haka? Me yake damunki haka,? kin rame sosai”

Jalal yace “hawan jini ne yake damun ta ya hau over, ko Abinci taƙi ci, mu zamuje gida mu ɗan huta”

Daddy yace “shikenan ku gaida gida, Jalila zanzo a kwance jaka dani ba abani tsaraba ta ba”

Murmushi Jalila tayi tace “shikenan Daddy insha Allah da kaina zan kawo maka har gida”

“to shikenan Allah ya huta gajiya”

Su Jalila suka tafi gida, Daddy kuma ya zauna zaman rarrashi Amma kamar yana tunzura Mummy taƙi saurarsa, likita ya sallame ta tareda bata magunguna Daddy ya ɗauke ta suka koma gida.

Ilham fa Abubuwan babu sauƙi, ta rasa inda zata saka ranta, basu da komai komai ya ƙare musu, gashi ita kanta Ilham ɗin cikin dare tsorata ta akeyi, taita gane2 da jin sautuka marasa daɗi, ta fara gajiya da jinyar mahaifiyar ta, babu wani ci gaba kullum jiya i yau ga babu wani me kawo musu tallafi koda na hatsi ne Ilham kuma tasan bata isa ta tunkari gidan Mummy ba.

Kwanan Daddy biyu a kano amma Mummy bata saurarsa, gashi komai a hankali take yi, saboda idan ta fiye aiki se taji kaman numfashin ta ze ɗauke.

Yanzuma Daddy yana ta lallaɓata taci Abinci Su Jalila suka zo dubiya, Amma ba Jalila ba hatta inda Jalal yake bata kalla ba, Jalila tazo da manyan kwalayen turare ta bawa Daddy sannan ta bawa Mummy tace “tsarabar su ce”

Jifa Mummy tayi da jakar kayan tace
“ke nifa bana son jaraba, na meye dole sekin min shishigi? Shegiyar yarinya makira sekace mayya, a baya ma dana yadda dake ban ɗauka haka kike ba, jarababbiya in dai Jalal ne gashi nan kije ki cinye shi, daga yau in zezo inda nake karki ƙara biyo shi, shi na haifa bake ba bana son salon munafunci bazan taɓa ƙaunrki ba, bazaki taɓa wani abu ki burgeni ba, yadda Asirin da’aka yi masa ya karye haka wanda kika yi masa ze karye, in ba aikin Asiri ba ya za’ayi namiji kamar Jalal ya dinga rawar ƙafa akan yarinyar da ta dinga ci masa mutunci a gaban uwar sa, ba miyagun kalaman da bata yi amfania dasu gurin muzanta Jalal ba, Amma mara zuciya ya liƙe mata se kace ita kaɗaice mace, ni ban yadda son da Jalal yake mata na tsakani da Allah bane, tunda uwatta beyerabiya ce ta shiga ta fita an………
“Enough Mummy” Jalal ya katse mahaifiyarsa daga maganar da take son ƙarasawa, ita kuwa Jalila ta shi tayi ta bar falon tana kuka, dan taji zafin maganganun Mummy ba kaɗan ba kai tsaye ta fice ta tafi gidan su.

Daddy ma ya fusata da abunda Mummy tayi dan haka yace “Khadija ke kam bansan me zaki gani a rayuwa da zesa ki dawo hayyacin ki ba, ina ni mijinki ne nima fa wata ce ta haife ni kika aura, kika rabani da ‘yan uwana da kowa nawa, kin auri ɗan wata kin mulkeshi dan me ke baza’ a auri naki a mulka ba,? ki gode Allah ke ta hanyar data dace a ke juya naki ɗan ya kike gani in da za’a miki abunda ke kikayi? Kina dama da kanki amma kina kishi da matar ɗanki wannan wane irin abun kunya ne? Hakan baze ja miki komai ba se zubewar mutunci “

Jalal yace
“tunda ba kya ƙaunar ganin Jalila nima ba kya ƙaunar ganina, sannan dan ta muzanta ni a gabanki a bayan idonki dubun ta sun muzanta ni, dukda kina mahaifiya ta idan na biye miki na cutar da Jalila se Allah ya saka mata, kin san baƙar wahalar da ta sha akaina kuwa? Dukda tana muzanta ni, Amma a bayan idonki baki san gwagwarmayar da tayi akaina ba, duk wanda yake ƙin Jalila ni yake ƙi, sannan tun bani da hankali mahaifiyarta tayi ɗawainiya dani ta kula dani, duk abunda ya faru a baya da Jalila tayi min ƙuruciya ce kuma ya wuce, Sannan ɗaya daga cikin manyan maƙiya ne da yayi kwangilar ɓata min rayuwa da shi da uban gidansa Oga KB Jalila ce tai sanadiyar zuwan su prison don ta nesanta su dani in dena shaye2, kullum muka haɗu ƙoƙarin ta da nasihar ta be wuce in dena wulaƙanta iyaye na ba musamman ke, kuma kinsani duk lokacin da ta gayan muguwar magana to tabbas ta kamani ina aikata abunda be dace bane, ni wani irin baƙin butulu ne da zan tozarta ta? So kike nima inyi dana sani inzo ina cizon yatsa kaman yadda kika yi, duk me son ya so Mata ta da dangin ta, sunmin abunda dangin uwa ta ba su yi min ba”
Jalal ya ƙarasa maganar kaman yayi kuka, ya nufi hanyar fita ya tsaya ya juyo yace
“Insha Allah Jalila bazata ƙara zuwar miki gida ba balle ki ɓata mata rai, har ga Allah a yanzu ma banji daɗin abunda kikayi mata ba” ya juya ya fice zuciyar sa a cunkushe

Jalila kam tana fita ta shige gidan su, Maama tana parlour tana shan tea Jalila ta shigo tana kuka, seda gaban Maama ya faɗi tace
“Jalila lafiya meyafaru haka kike kuka?”
Seda Jalila tayi kuka me isar ta sannan tace “Maama wai dan Allah da ba a yafiya a duniyar nan da zamu cigaba? Da Allah baya yafe laifukan mu da zamu kawo iyanzu muna morar ni’imomin sa?”
Maama ta girgiza kai tace “A’a Jalila, Kullum cikin laifi muke Allah yana yafe mana, ba dan yana yafe mana ba da tuni ya kawar damu ya halicci wanda zasu bauta masa ba tare da sun saɓa masa ba”

Jalila ta goge hawayen ta tace “Maama meyasa Mummy bazata yafe laifukana na baya a idon ta ba, ta tsaneni bata ƙaunata, kullum se tayi mitar a baya na muzanta ɗan ta a gaban ta, Maama Jalal da bakin sa ya yafe min abunda nayi masa, Amma kullum se Mummy taci mutunci na”

Maama tace “Jalila shiyasa a rayuwa dan mutum yana aikata kuskure be kamata ka dinga yi masa gatsali kana cin mutuncinsa ba, kin gama yi masa rashin ta ido ƙarshe ya zama mijinki wanda yake matuƙar ji dake, Amma mahaifiyarsa bata ƙaunarki, duk abunda kikayi wa ɗan ta na kirki ko akasin haka uwa bata mantawa, Nima ƙaunarki ga ‘ya’ yana ce tasa na dawo hankalina na gane kuskure na, dan haka ko nan gaba ki kiyaye muzanta ɗan mutum a gaban iyayen sa, sannan be kamata ta cigaba da ƙinki ba dan ƙoƙarin da kikayi akan rayuwarsa yafi laifukanki, ya kuma ci ace ta yafe miki”

Cikin kuka Jalila tace “bana tunanin zata yafe min ta tsaneni yadda ba kya zato na rasa ina zan saka rayuwa ta, kuma tun a wancan lokacin da ta tsawatar min ta nuna min bata son abunda nake wa Jalal da bazan kuma ba”

Maama tace “Hakane Amma kiyi haƙuri, ba’a taɓa kyale ɗan adam ba’a jarrabashi ba”

Yarone yayi sallama Maama ta amsa, yaron yace “wai Jalila ta fito su tafi gida inji mijin ta”

Maama tace “to kace tana zuwa”

Jalila na miƙewa ta zura da gudu ɗakin su.
Maama tabi bayan ta tana faɗin “wannan wane irin sakarci ne kuma? Ki taso kije ku tafi”

Cikin kuka Jalila tace “ni ba inda zani bazan bi shi ba, Mummy ta zaɓa masa matar da take so ya zauna da ita”

Maama tayi tayi amma Jalila ta ƙeƙashe tace “ba inda zata”

Jalal ya gaji da jira dan haka yazo yana ƙwanƙwasa ƙofar parlourn Maama tazo ta buɗe, Jalal ya durƙusa ya gaishe ta, wanda da se su kusa karo a hanya baze kula ta ba alhalin a gidan ta yake wuni tareda ɗan ta, tabbas idan Mummy ta dage gun raba Auren su Jalal zata tafka kuskure mafi muni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button