ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jalila ta yanke hukuncin yau zata samu Abba ko agaban waye, zata nuna masa illar abunda yake shirin yi
Kai tsaye part din Abba taje, ta shiga da sallama a bakinta, ya amsa sallama sannan yace “dama ina son ganinki, Baby ankaiwa yayanki kudi ze Auri ‘yar uwassa, kune’ yan mata kunfi sanin menene kuke so, kuma kuna tareda ita, maybe a kayan lefe akwai abunda takeso maybe ku tayi hirar daku, ba lallai tagayawa iyayen ta ba, dan haka inda wani abu da take bukata kokune tagayawa kota rubuto, saboda asan me za’a samata a kayan lefe”
“Abba wannan Auren fa bame yuwuwa bane?” mamakine ya kamashi yace “meyasa Jalila?”
“Baya sonta fa”
“Amma na kirashi na tambayeshi yace min ya yadda”
“Haba Abba zuwa yanzu yakamata kagane halin Yaya Jawwad, tunda kake ka taba nuna kana son Abu yace bayaso? Wallahi Abba Auren nan tamkar kasa hannune da kanka ka rusa doguwar tsaftataciyar katangar rayuwar Yaya Jawwad ne, Abba please kayi bincike”
“karya kikeyi bakar munafuka, ba wani bincike daza’ayi, yarinya ‘yar dangice, me tarbiyya da sanin yakamata suna son junansu, Amma dan munafunci shine kike bata mata suna a gurin sirikinta, kedai Azzaluma ce, ni ina kudina ma da Mummy ta bayar akawomin? Ilham tace tabaki amma dan son zuciya baki baniba seda na buga waya aka gayamin ke aka bawa”

Daga Abba har Jalila tsayawa sukayi suna kallon Maama, Jalila takasa gane inda Maama ta dosa
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

             *ABDUL JALAL*

Story and writing
By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girls)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A*✍️


PART 2         
                      _PAGE  3️⃣8️⃣91

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

      _MY FIRST NOVEL _

Abba ransa ya baci dajin kalaman da Maama ke fadi dan haka yace

“zainab meye haka kuma? Kibar ta ta fadi abunda yake bakinta mana, be kamata ki katse mata hanzari kidinga jifanta da wannan muna nan kalaman ba akanme? Na dade ina tunanin Jalila bata jin dadin zaman gidan nan, Allah ka dai yasan mekike mata inba na nan, nayi shiru ne dan bata taba gayamin wani abu akan irin zaman da take ba, kallonki kawai nakeyi zainab “
Se yanzu Maama ta shiga hayyacinta take tuna maganganun data fada idonta ya rufe ta manta shaf agaban Abba tayi su, cikin kokarin kare kai tace
” kayi hakuri Abban Jawwad, raina ne ya baci, iya sanina Naja batada wani aibu amma Jalila se kokarin kushe Auren take, kuma da ina cuzguna mata aida zata gaya maka tunda kasan bakinta baya shiru”

Jalila kallon Maama kawai take, Abba yayi tsaki yace “Inajinki Jalila cigaba da maganar ki”
Jalila tace
“A’a Abba base muncigaba ba, Amma Maama ni Ilham bata bani kudinki ba, tsawon zamana a gidan nan ban taba daukan cokali da sunan ha’inci ba, kina aikena gurare da dama da kudi, har banki kike turani da ATM card dinki ban taba batar miki da ko kwabo ba abaya, wallahi ni Ilham bata bani kudi ba”

Yadda Jalila take maganar kasan zuciyarta a cunkushe take da bacin rai, dan har idonta yatara Hawaye, Maama kuwa fakar idon Abba tayi ta watsawa Jalila wani kafirin Kallo.
Abba yace
“ke Zainab kikoma can kuyi maganar kudinku, ni ‘yata bata sata, bata ha’ inci na yadda da ita, Jalila tashi kije Allah yayi miki Albarka, karki sake ki zubar da hawayenki a banza”
Jalila jinjina masa kai kawai tayi ta mike, tana fitowa taji hawaye nabin fuskarta wani bayan wani, koda Jalila ta koma daki Nana tana bacci dan haka ta samu guri ta takure ta fashe da kuka, hada sheshsheka tana kuka tana surutai
“Ummi kingani ko? Da tun farko kin tafi dani da kome zefaru tare ze samemu amma kinmin Nisa, kin barni inata fama da wahalar Rayuwa, banida matemaki se Allah”
cikin bacci Nana taji kukan Jalila, koda ta bude idonta Jalila ce ke faman sharbar kuka, da sauri ta sakko daga kan gadon tazo gabanta tareda fadin
“Jalila lafiyarki kuwa? Gayamin me yasamiki?”
Shiru Jalila tayi se kuka data cigaba, duk yadda Nana tayi Jalila taki gayamata me yafaru, Nana ta rumgumeta tana fadin
“tunda bazaki gayamin ba bazan takuramiki ba, Amma dan Allah kidena kukan nan, Jalila banajin dadin ganin kina kuka haka dan Allah kidena in bahakaba nima zaki sani kukan”
Jinjina mata kai kawai Jalila tayi, ta zame ta kwanta akan cinyar Nana, ta juyarda kanta hawaye na cigaba da zuba.
Da Naja ta dawo gidan seda Maama tagaya mata abunda ta tarar da Jalila tana gayawa Abba, Naja ta dinga masifa taana zataga bayan Jalila, setasa ta bar gidan da kafarta, tunda ita mayyace, Maama ta gaya mata wai Jalila ta cinye mata kudi dubu tamanin Abba yace karta kuma daga maganar shi yasan Jalila bazatayi haka ba, suka kuma haduwa sukasa Jalila a gaba da gori, Maama ta hade kai da Naja suka cigaba daYiwa Jalila barin miyagun maganganu, Amma sam Nana bata san meyake wakana ba, zuwa makaranta ne kawai kesa Jalila samun raguwar pressure dake kanta, shima yanzu makarantar idan taje kuka takeyi bata jin lectures din. Jalila batayi mamakin abunda Ilham tayi mata ba dukda abun yamata ciwo, Amma a yanzu ita ba wannan ne ya dameta ba, maganar Auren nan ce yake damunta.

Wasa2 Jawwad yayi rama ta ban mamaki, yana cikin tashin hankali an saka biki a kusa watanni shida, ko Abinci baya iya ci, nutsuwarsa daya idan yana waya da Hanan, kokuma Idan Jalila tana masa nasiha da bashi kwarin gwiwa, ko Abinci baya iyaci, duk haskensa seda yayi duhu, Jalila tarasa ta ina zata fara shawo kan matsalolin nan.
Yanzuma gurin Jawwad ta tafi don ba karamin tausayi yake bata ba, taje ta kaimasa Abincin rana, ta tarar ya idar da salla ta jira Jawwad yayi Addu’oin sa ya shafa, sannan tace
“Yaya Jawwad nasan kana cikin damuwa, amma kadinga kokarin kwantar da hankalin ka, ina nan inata kokari sannan ina Addu’a Allah ze kawo mafita”

Murmushin yake yayi wanda yafi kuka ciwo yace “ina Addu’a baby, ina fatan Allah yabani ikon cin Jarrabawa”
“Insha Allah komai ze wuce sannan nace ya batun zuwan ku kaduna kuwa? Bana son plan dina ya tafi a banza”

“Ina sane Jalila, zamuje Insha Allah, kafin lokaci ya kure”
“to shikenan, amma ka dena wannan damuwar kaji Yayana?”
“Na dena babyn Ummi”
Murmushi tayi masa
“yawwa haka nakeson ji, bari in dawo in gyara maka dakin nan, naga yayi kura”
“to shikenan Autar Ummi nagode sosai, Allah ya sanyawa Rayuwar ki Albarka, Yadda kike kokarin faranta min Allah yabaki mijin daze kula dake ya soki ya rikemin ke Amana, a lokuta da dama kina sadaukar da farincikinki dan ganin wasu sun samu nasu farincikin, Allah yabaki wanda ze kulada ke, yabaki mijin marainiya, wanda ze kula dake da maraicinki”
Taji dadin Addu’ar yayan nata, Amma takasa cewa Ameen sema Hawaye daya taho mata.
Tagama abunda take a cikin gida, taje domin gyara bangaren Jawwad, Jalal na kalmashe akan kujera yana game a system, sukaci Abinci shida Jawwad, yacigaba da game dinsa, tunda ta shigo ba wanda ya kula wani tsakanin ta da Jalal, Maama takira Jawwad a waya tace yaje cikin gida tana son ganinsa, jiki ba kwari ya tashi ya tafi, dan yasan be wuce akan maganar Naja ba.
Jalila tasan babu alamun Jalal yayi sallar Azahar, ta duba taga system din a jikin caji take yake amfani da ita, tasa hannu ta kashe main socket na dakin, system ta dauke dama babu caji, kallonta yayi a fusace ze masifa amma yakasa, ganin irin kallom da take masa,
“Kayi sallar Azahar kuwa?”
“ban Sani ba, ko innayi ke zanyiwa?”
“Subhanallah karkayi sabo, ai ba fada bane, Salla fa, haske me girma ga tarin lada ga ma’abota yinta akan lokaci, kaga da kana bata mahimmanci sosai da yanzu Rayuwarka ta canza, da abubuwa dayawa kadaina aikata su, karfe uku ta wuce amma bakayi salla ba, wanda ya mutu baya salla kasan makomarsa wuta ce ta saqara, wadda ake sa wanda basa salla, Ai baka son shiga wuta ko dan gidan daddy? Ta tambayeshi kaman tana magana da yaro karami”
Be Amsa ba se kallon ta dayake, tasa hannu ta janye system din
“Yawwa abokin Yaya, kayi yaki da shedan, ka yaki zuciyarka ka daure, kaga in kayi sallah sekayi Addu’a, Allah na karbar addu’a bayan sallar farilla, kaje kayi salla”
Mikewa yayi ya nufi bedroom din Jawwad ba tareda yace mata kala ba yaje yayo Alwala, yana shiga tayi Ajiyar zuciya mutum kaman wani dan karamin yaro, komai se an lallabashi Allah ya shirye ka, yanzu tagama gane halinsa, ba yasan fada ne sam, indai zaka gaya masa magana da fada, to zakuiyi fada dashi. Jalila tanata goge2 ta kunna TV takai sunna tv ana karatun Al’qur’ani, tana aikinta tanayi, sosai takejin dadin karatun suratul Yusuf, dauke wuta akayi dan haka tv ma ta dauke, ta danyi shiru, kawai taji an dora daga inda ta tsaya, waigawa tayi ta ga Jalal yana karasa mata ayar, ya iya karatun qur’ani, bata manta randa ya kaita makaranta ba ranar data fara jin yana karatu, Murmushi tayi tace
“cigaba mana”
“A’a kedai kicigaba, na manta Aya tagaba, bana tilawa, bana tuna haddata duk na manta, kwakwalwar ta toshe”
“Ahh waika manta, ba wani kamanta”
“Am serious na manta, cigaba maybe inkin cigaba in tuna”
Ba musu kuwa ta dora, tana cikinyi setaji yakama yanayi,
“Amma kace ka manta? Dama ka iya karanta Al’qur’ani haka, inama kana yawanyi da ko a hanya kaga giya zaka dauke kanka ne, waye ya koya maka karatu haka?”
“A islamiyya sannan kuma Ummi, bazan manta ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button