ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jalila takira Ahmad ya sanar da ita cewar baze shigo yauba, saboda yayi dare a hanya sedai zuwa gobe Insha Allah, seda suka sha soyayya sannan sukayi sallama gefe daya kuma hannunta se ciwo yakeyi, da wanine yai mata abunda Jalal ya mata yau da seya gane bashida wayo, shima ďin dan yanzu bata son yawan fitina da shine saboda gaba ďaya yanzu tausayi yake bata, da dane da seta rama. Amma to meyake damunsa haka? Lokaci ďaya mutum ya rikice kaman wani me tabin hankali, yana zaune lafiyar Allah amma ya birkice lokaci daya wai seyasha giya.

Jawwad kasa boye farincikinsa yayi, seda ya kira Jalal a waya, yana ďagawa Jawwad yace “My man kana inane?”
“Ina gida mana, ina zanje tunda baka nan? Wai yaushe zaku dawo? Tun dazu nake zuba ido amma baku dawo ba”
“Ai mu ba yau zamu dawo ba”
“Se yaushe?”
“Ai bazaka gane ba Jalal bansan yadda zan fasalta maka farincikin danake cikiba”
“Abba yaje nema maka Auren Hanan a Bauchi” Jalal yafada kai tsaye
Da mamaki Jawwad yace “ya akayi kasani?”
“Zuciya tace tagayamin”
“ban yadda ba dama can kasani kai shiru kaki gayamin, amma akwai saura ai”
“to gayamin inaji”
“Abba ya gano danginsu daya daďe yana nema”
Murmushi Jalal yayi yace “Alhamdilillah, na dade ina fatan hakan ya tabatta, kakarsu Abdallah ce Inna Hafsatu da Inna mairo take fada take bamu Labari ko?”
Cikin mamaki Jawwad yace “wai dan Allah ya akayi kasani?”
“Allah ne yasanar dani, dan Allah kadawo da wuri, ni bana jin dadi in baka nan”
“wai kana in dawo da wuri, kamanta in Allah ya kaimu next week zan tafi inda aka turani aiki”?
“kumafa hakane se yanzu nakejin babu daďi, amma Insha Allah hakanne mafi Alkhairi agaremu baki daya”
“Amma ni ina mamaki yadda akayi duk kasan wannan zancen ni ban saniba” dariya Jalal yayi yace
“Ba abun mamaki bane, kai dai seka dawo kawai
Seda suka gama hira da Jalal ya katse wayar, Jawwad yaji kaman ya kira Jalila amma ya fasa, dan yasan idan ya kirata farinciki seyasa yagaya mata abunda ke faruwa kuma Abba ya gargade shi akan kar kowa yasan wannan zancen a yanzu harse sun koma gida.

Maama tarasa ta inada zatayiwa Naja bayanin Abba yana bukatar ta bar masa gida, saboda tana matukar Jin tsoron Masifar Yaya Mairo, tarasa abunda yake mata dadi, yanzuma da Abba yayo waya seda ya jadadda mata baya son ya dawo ya tarar da Naja cikin Iyalinsa, tarasa ta inda zata fara harga Allah bazata iyaba sedai inya dawo shiya koreta da kansa, can wani bangaren na zuciyarta yake cemata banda ma ya raina miki hankali, ita Jalila dake zaune a gidan meyasa bece ta bar gidan ba, shekarar Jalila nawa a gidan, se yanzu zece Naja tabar gida, indai Naja zata bar gidan nan to dole Jalila ma ta kama gabanta, Maama tayi kwafa tace
“Zaka dawo ka sameni, dai2 nake da kai”

Naja se iyayi take tana wasu irin abubuwa na ban haushi wai ita zatayi Aure, A gaban su Nana take waya da kawarta sunata shirye shiryen abunda zasuyi da biki, ba kunya Naja take cewa a mata booking na kayan mata na tashin hankali, masu tsada, se wasu irin lissafi takeyi, kala2 party da zatayi, da irin expensive clothes da zasu saka itada kawayenta.
Tagama wayarta su Jalila suna jinta, tana gamawa Nana ta tinstire da dariya,
cikeda tsarguwa Naja tace “ke Nana meye abun dariya haka?”
“A’a ni ba dake nake ba, mahmud ne yabani dariya a waya”
Itakam Jalila bata samu zarafin dariya ba tana fama da ciwon hannu, ko uffan ba tace ba.
Nana tagayawa Jalila Abba yace bazasu dawo yauba, Akwai abu me mahimmanci daya rikesu, Jalila a ranta taketa addu’ar Allah yasa abunda take tsamanni ne ya tabatta.

Washegari da safe Monday ce Jalila tace bazata makaranta ba, Dan haka Nana ita kadai ta tafi, tai kwanciyar ta tana bacci, Zahra takirata a waya tagaya mata zasuyi test karfe goma shadaya da rabi na safe, Jalila sam bata da niyyar zuwa makaranta haka ta tashi tana tsaki tayi wanka tasaka kaya, doguwar riga pitch da mayafinta se wata ‘yar karamar Jakarta ta dauka, iyakacin Jakar nan ta dauki waya da kudi da ďan abunda baza’ a rasa ba sekace jakar roko,
Jalila Ta fito fuskar nan babu walwala, ta tarar Maama na palour tana karyawa itada Naja, yanzun ma hirar bikin suke, Jalila ta durkusa tace

“Maama zan tafi school, yanzu aka kirani zamuyi test anjima”
Banza Maaman tayi mata taki kulata, dama batayi tsamannin Maama ta amsa ba, tayine dan hakan shime tarbiyar da Ummi ta dorata, ta mike jiki a sanyaye Zata fita Naja tace

“Aikin banza wai za’a school za’a tafi yawon gantali dai irin wanda uwale ta saba yi”
Maama tace “dan Allah kidena shiga harkar yarinyar nan shiyasa take kara rainaki”
ai kafin Maama ta gama magana Jalila ta waigo tace “ta Uwale tayi kyau, kekuma ki saurar kiga naki sakamakon, anzo an bararaje ana cin duniya babu a house, gara ki zage ki ciki kafin ki kara gaba, Akuya kawai”
Ashar Naja ta mulmulo zatayi Maama ta dakatar da ita, Jalila kuwa tayi ficewarta ranta bakikkirin babu dadi.
Maama tace
“kyaleni da ita, ki zuba ido zakiga matakin da zan dauka akanta”

Jalila na fita ta hango Mummyn Jalal tareda Ilham da alamu wani gurin zasuje, da kaman ta basar tayi tafiyarta sekuma taga hakan be dace ba, dan rabonta da taga Mummy harta manta dan ko gidan bazuwa takeba yanzu, dan haka ta nufi inda motarsu take, Mummy tana kokarin shiga, Jalila da fara’arta ta karasa ta durkusa ta gaida Mummy, amma ga mamakin ta taga Mummyn tayi mata wani irin mugun kallo kamar bazata amsa ba sekuma ta amsa da kyar, Jalila taji ba dadin abunda Mummy tayi mata, amma ta dake ta mike tace “Mummy Adawo lafiya sekun dawo”
Mummy ta yamutsa fuska tace “Yawwa dama ina son ganinki kuwa, akwai magana me mahimmanci da nakeson mu tattauna dake, dan bazan saka ido abunda ke faruwa yacigaba ba”
Seda gaban Jalila yai mummunar faduwa, wannaan wane irin abune ita kowa ma laifi take masa, kowa ya tsanenta a fili tace “to Mummy Allah yasa ba laifi nayi miki ba? Zanzo Insha Allah, Adawo lafiya”

“Munafukar banza barauniya, me bin ďan mutane, Akuya kawai”

Taji sautin maganar Ilham ta sauka a kirjinta saitin zuciyarta, dukda yadda maganar tayi tsauri tareda dukan zuciyar Jalila, amma ta danne taki juyowa ta kuma kallon inda suke, ta mike tacigaba da tafiya.
Jefa kafarta take ba tare da tasan ina take saka kafar tata ba, Hawayene yake bin idonta, Allah ya temaketa unguwar tasu se kayi minti goma babu wanda yazo ya wuce, kuma wajen karfe tara ne duk wasu sun riga sun fita, hakan yakara bata damar zirarar da hawayen ta son ranta, tana cikin tafiya ne taji ana mata horn kaman za’a kashe mata kunne, ita dai iya saninta ba a tsakiyar titi take tafiya ba gefen hanya ne, Amma an cika mata kunne da horn, banza tayi tacigaba da tafiyar ta.
motar aka sa aka sha gabanta, sannan yafito daga motar yace
“Bakya jin ina miki horn ne ? Sekace wata kurma, Kuma Se yanzu zaki tafi school karfe tara? Allah ya shirye ki, zo muje in ajeki ta nan zan wuce” ya dinga jero maganar daya bayan daya
Juyowa tayi ta kalleshi, ya saka farin yadine dukda kansa babu hula yayi kyau sosai, dan zata iya kirga sau nawa taga Jalal da dogayen kaya, kallonta yayi sosai yaganta kaman a birkice, hawayene a fuskar ta, idonta har yafara Ja, cikin tsiwa tana hararsa tace
“bazan hauba ai da can ba kai kake kaini ba, salon in hau motar ka, ka karasa karyani bazan hauba”
“hmm bazaki hauba ko? Bazaki hau motar mahaukaci ba, Dama interview din nan zani, Amma tunda bazaki hauba se inkoma kuma bazan kuma zuwa ba”
Cikin sauri tace “A’a yi hakuri zan hau, Amma dan Allah karkayi gudu dani” tafada hawaye na zubowa daga idonta
Gaba daya tausayinta ya kamashi, kome yasata kuka haka a titi, itada take da dakakkiyar zuciya? Abunda ze satana tafiya tana kuka ba karami bane ba
“bazan ba, a hankali zan tafi” ya faďa a takaice
Ta bude motar ta shiga, shima yazaga ya bude ya shiga, ya kunna motar yai mata key, suka fara tafiya, ya kalleta yace “Kukan me kike?”
“bakomai”
“bana son karya fa”
Shiru tayi masa, ta maida kanta titi kyaleta yayi tunda yaga batasan faďa masa, maybe is her personal issue. Suna cikin tafiya Jalal yayi parking ya kalleta yace “Zoki rakani zanci Abinci, banyi breakfast ba”
“Ni bazaniba, kaje ka dawo, nibana son ana ganinmu tare” ta fada tareda dauke kanta daga kallonsa
Ba tareda ya kalleta ba yace
“ohh yeah, be kamata adinga ganinki tareda ďan iska mara tarbiyya ba, kar azata irinmu daya, bari yanzu zan dawo”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button