ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jawwad yace

” Ikon Allah, ji yadda ya wani kashe murya yana gayamin yayi missing din matar sa, kaman ba shine me cewa Mata matsalane, soyayya shirme ce, to yanzu kuma mene? “

Jalal yayi murmushi yace
“a bayan ma duk basaja nakeyi in gaya maka, da zaka tona zuciya ta seka tausayamin, nayi zaton cire soyayya abune me sauki daga zuciya, amma duk lokacin da nayi yunkurin cire son ta a raina, se naji kaman ina kara azabtar da zuciya ne, gashi a lokacin bana ganin komai se kiyayya ta a idon Jalila, se kuma daga baya da Hanan ta nunamin son da Jalila takemin ne yasa take fada da kowa akaina, kishina da take yasa take bani Kariya da dukkan mummunan abun da ya tinkaroni, shiyasa na samu karfin gwiwa na cigaba da kaunar ta, ina son Jalila sosai, kai se anjiman ku, zan fita gurin aiki”

Jawwad yace “har ka gaji da zubar? Da labarin soyayyar taka?”

“ina fa? Ai labarine sakanni, awanni, da wuni, sati, watanni ko shekaru bazasu bada damar gama wannan Labari, me dadi da ban tausayi ba se an jimanku”

Murmushi Jawwad yayi
“A da in aka cemin Jalal yana wannan zazzafar soyayyar zan rantse ince karya ne, yau gashi kunne na yaji min”

Hanan tace “Ain dama tuni nasan yana kaunar ta, kuma itama tana sonshi, shiyasa nai tayi musu Addu’a, nikuma na kafa tawa soyayyar”

Jawwad yayi murmushi yace
“gashi nan an kafa min ita inda ba wanda ya isa ya ganta balle ya taba, mata ta abar Alfahari na, Allah ya rabaki da cikin nan lafiya dake da Nana”

“Ameen my lovely Haidar”

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣9️⃣112

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Shiri sukayi sosai don tafiya garinsu Ummi, da farko akace baza’aje da su Nana ba saboda larurar ciki, amma sukace baza’ayi babu su ba suma suna son zuwa garinsu Ummi.
Shiri sukayi sosai, suka dau motoci suka nufi kwara state.

Tunda suka shiga garin Jalila ta kara tabattar da lallai Akwai banbancin Addini da al’ada.

Jalila tayi mamakin irin kyau da tsaruwar masarautar su Ummin ta, lallai Ummi ta cancanci yabo da jinjina, da ta iya tsallake wannan daular ta zabi Addinin musulunci da kuma soyayya.

Su nasu masarautun basa amfani da doki, se manyan motoci, ga barori nan nata kaiwa suna komowa, gasu da matukar biyayya, duk inda suka ratsa zubewa ake ana girmama su, musamman Ummi.

Seda suka shiga cikin gidan ta kara tabattar da lallai Ummi ba karamar ‘yar gata bace ba, Tangamemen hoton Mahaifiyar Ummi ne sakale a wani katon guri kamarta daya sak da Ummi, duk da ta manyan ta seka dauka ya da kanwa ne.

An karbesu cikin girmamawa da mutuntawa, Seda suka huta, Aka dinga gabatar musu da kayan Abinci,
Seda aka jima suka huta sannan Mahaifiyar Ummi ta fito, Mahaifiyar Ummi na ganin Jalila ta rungumeta cikin harshen turanci tace

“ko ba’ a gayamin ba nasan wannan itace jikata”
Ummi tayi murmushi tace “Eh itace”

Mahaifiyar Ummi ta kalli su Hanan ta kalli Jalila tace

“wannan ‘yan uwanta ne?”

Jawwad yace “Eh duk’ yan uwanta ne”

“to wace matar Jalal kenan?”
Nana tace “Jalila ce matarsa”

Mahifiyar Ummi ta jinjina kai tace

“Sunan ta da mijin ta suna kama, mijinki yana da kirki sosai lokacin da mamanki ta dawo gida yana zuwa nan”

Maman Ummi tana da kirki sosai, nan aka dinga gabatar da su gurin mutanen gidan, ‘yan gidan sunyi murnar ganin yarinyar’ yar uwasu, bayan tsawon shekaru ‘yar uwatasu bata tareda su.

Sarkin da yake mulki a wannan lokacin wanda yakasance Yaya ga Ummi shima ya nuna farincikin sa da jin dadi, na ganin su Jalila.

Daddare suna hira, mahaifiyar Ummi take cewa su Jalila,

“nayi dana sanin hana marry ta auri wanda take so a wancan lokacin, dukda ba laifina bane, laifin kakanta ne, yana ganin na auri bahaushe musulmi zaman beyi dadi ba, nayi kewar ta sosai tsawon wannan lokaci, bana iya bacci, sannan mahaifina yace be yadda in tura kasar hausawa a nemo ta ba, duk abunda yafaru da ita babu ruwan wani. Ban taba zaton marry zata iya jure zama tsawon wannan lokacin ba ba tare da mu ba, bayan rasuwar mahaifina shekaru biyar baya, Yayanta ya karbi mulki, shi da kansa yasa a bincika koza’a gano ta amma abun be yuwu ba, na koma Addinin musulinci, Yayana yaba wa kowa damar yayi Addinin da yake so, abun mamaki akan marry na yadda musulmi kuma hausawa mutanen kirki ne, lokacin da ta dawo gidan nan nayi mamaki, labarin da ta bani akan yadda rayuwar hausawa musulmi yake, da kuma karamcin da suka nuna mata, musamman wannan dan kyakywan yaron me dogon hanci, yana burgeni matuka yana girmama ta kaman ta haifeshi, kuma da ta gayamin alakar dake tsakaninsu naga babu wani babbar alaka da suka hada amma yake ta dawainiya da ita shida iyalansa”

Jalila ta kunshe kai tana dariya taji ance Dan kyakywan yaro me dogon hanci

Hanan tace “Dallacan se wani murmushi take dan ance mijinta kyakywa, nima mijina kyakywa ne, dan mijina farine tas”

Nana tai caraf tace “nima mijina yana da kyan ai, tunda kanin mijin Jalila ne”

Sukaita hira suna dariya, mahaifiyar Ummi tana da kirki da sanyin hali kamar Ummi gata da faran faran babu ruwanta.

Amma duk abun nan Jalila hankalin ta yana kan Jalal, ta damu sosai rashin ganin sa, ba karamin missing dinsa take ba.

Kwanan su hudu a garin, sun sha yawo, garin yana da kyau, sun sha hotuna, gasu da yalwar dazuka, Akwai fulani a garin, da babur amma yawancin su yarabawa ne, suma mutane masu kirki da kyakywar mu’amala.

A kwana na biyar suka fara shiri domin tafiya su bar garin.

Mahaifiyar Ummi taji babu dadi, seda tayi mita

“marry meyasa bazaki barmin yaran nan ba su dan kara kwanaki, wallahi sun shiga raina sosai naji dadin zama da su”

Ummi tace

“kiyi hakuri zasu dinga kawomiki ziyara, matan aure ne yaran nan, yakamata su koma gidajen Auren su, sannan Zamuje maiduguri gidan Su Danki Jalal, Abban Jawwad zasu jira mu a can”

“Shikenan amma ba haka naso ba, naso kara zama damu, yanzu na kara tabattar da abunda ake fada akan hausawa musulmai ba haka bane, kuna da kyakywar mu’amala da kuma girmama mutane, Jawwad amma kaima zaka dan dinga zuwa ko?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button