ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jawwad yai murmushi yace “karki damu, dukkan mu ma zamu dinga kawo miki ziyara, amma kema muna fatan zakizo mana”

“zanzo mana, tunda ina daku, Insha Allah nima zanzo muku”

A kwana na biyar suka karasa shiri zasu tafi, An musu alkhairi me tarin yawa. Suka yi harama Jawwad ya dauke su suka baro garin suka nufi borno state.

A motar ma se hira suke, suna kara yaba kirkin mahaifiyar Ummi da kuma barkwancin ta.

Suka karasa maiduguri a gajiye, bayan la’asar sosai suka karasa, Antyn Jalal tayi murnar ganin su kwarai, musamman da ta gansu tareda Ummi cikin fara’a tace

“kai masha Allah, bakin ba zata, Ummi Kice keda iyalan naki gaba daya kike tafe”

Ummi tace “Aikam dai gasu nan”

“sannunku da zuwa Jawwad, dazu Jalal ya bar garin nan, nasan be san zaku zo ba”

Jalila a ranta taji dama tun dazun sukazo,

“meyasa Jalal yakemin hakane? Duk na damu yaki bari mu hadu sam, why?”

Anty tace

“Jalilan Ummi, gaki ga Ummi, dazu Jalal yabar garin nan, albarkacin ki yasa ya kan leko mu ya kawo mana ziyara, bashi da aiki se yabon matarsa ko kunya ta bayaji” dan murmushi Jalila tayi ta sunkuyar da kai.
Jawwad yayi alwala ya tafi masallaci,

Suma sallolin su suka gabatar, Anty se lallaba su Hanan take saboda ciki da suke dauke da shi.

Jalila tace “Anty ina Husnah ne da Amal?”

“Husnah ta koma gidan ta, Amal kuma tana gidan kanin Babanta”

Daddare mijin Anty ya dawo, yanayin yadda suka gaisa da Ummi ze tabattar maka da sun san juna, nan Ummi take gaya masa daga kwara State suke, ya nuna farincikin sa da jin dadin sa akan hakan, gefe guda kuma ya dinga tsokanar Jalila

“matar so inji mijin ta, ya akayi kukayi sabani da mijin naki ne? Shi ya tafi dazu kekuma kinzo yanzu, ya akayi hakan ta kasance? Gayamin sirrin mana daughter, banda zancenki ba abunda Jalal yake in ya zauna”

Jalila dai kasa magana tayi, kowa tsokanar ta yake saboda Jalal.

Itakam Hanan ana wannan hirar ta silale ta tafi masaukin Jawwad daga ta kai masa Abinci bata dawo ba se bayan karfe daya, Jalila ta dinga ce mata mara kunya.

Washegari wajen Azahar Abban Jawwad da Daddyn Hanan, se Maama da Mummy Hanan suka iso, gida ya dau harami ya cika da baki.

Suna zuwa da suka huta ba tare da bata lokaci ba Daddy ya gabatar da abunda ya kawo su na zuwa su jadadda godoyar su akan karamci da dawainiyar da sukayiwa Ummi.

Abee yace

“babu bukatar ku cigaba dayi mana godiya, duk abunda Jalal yayi wa Wannan baiwar Allah be fadi ba, musamman shima dawainiyar da soyayyar data nuna masa a lokacin da shi da mara uwa kusan daya, mun riga mun zama daya da mu da ku, dan Allah batun godiyar nan a barshi, Allah yakara hada kanmu ya kara mana kaunar juna, Allah ya Albarkaci rayuwar yaran mu, Amma babu godiya a tsakaninmu”

Suka Amsa da Ameen gaba daya.

Kwana daya su Abba sukayi, suka kama hanya zuwa bauchi, kafafuwan Hanan duk sun dan kumbura saboda zaman mota, hakan yasa Jawwad ya damu yace a bauchi ze barta ta huta, in yaso ya biya kudin jirgi su koma Abuja. Tun suna hanya Mahmoud ya kira Nana a waya yace mata yana bauchi, Nana se murna take yi, yau zata ga mijin ta, Jalila ta danyi shiru tana tunanin nata mijin.

A gajiye suka koma garin bauchi, a yan kwanakin nan sun sha yawo, da suka isa bauchi Jalila wanka tayi ta nemi guri ta kwanta tana baccin gajiya.

Jalila bata tashi ba seda Ummi tazo ta tasheta
“ki tashi haka kiyi salla kici Abinci mana, baccin ya isa haka uwar bacci ashe har yanzu baki dena wannan baccin ba”

A shagwabe tace
“Ummi wallahi a gajiye nake shiyasa”
“ki tashi haka dai baccin ya isa”

Jalila ta tashi tai salla ta zubo Abinci ta zauna kenan ta fara ci Nana ta shigo, ta kalli Jalila tace

“se yanzu kika tashi kenan? In kin gama akwai surprise”

“Suprise kuma? Suprise din me?”

“sekin gama tukuna”

Jalila tace “shikenan”

Jalila ta cinye Abincin ta, tanemi guri ta kashingida tana danna waya.

Nana ta dawo dakin ta tarar Jalila tana danna waya, ta dan hade rai tace

“wato baki damu da Suprise din ba ko?”

Jalila tace

“ai naga baki da niyyar gayamin ne”

Nana ta dakko powder da janbaki tazo gaban Jalila ta zauna.

Jalila ta kalleta

“wannan na menene kuma?”

“fita zamuyi, yaya Jawwad yace mu shirya”

Jalila ta dan bata fuska tace

“haba dai muje ina? Banda wannan gajiyar”

“ni dai ba ruwa na, shi yace mu shirya zamu dan fita”

ta shashsha fawa Jalila powder da jan baki sunayi suna fada Jalila tana mitar ita gaskiya bata son kuma fita a gajiye take

Hanan ta shigo tace

“Jalila har yanzu baki je ba?”

Cikin rashin fahimta Jalila tace
“nifa ban gane muku ba, inje ina kuma?”

Nana tace “kije BQ ki duba Suprise din yana can”

“nifa Nana nakasa gane miki, kince Yaya Jawwad yace zamu fita kuma kince zakiyi surprising dina”

Hanan tace

“dan Allah kije ki gani mana, ke ba kyacin ribar abu, ga mitar tsiya”

Jalila tace “saura inje inga shirme, sena muku rashin mutunci”

Hanan tace “in kuma akasin shirmen kika gani fa?”

Jalila tace “Bari dai inje in gani tukuna” ta dauki gyale ta yafa akan riga da skirt din jikinta ta fita

Da taje inda Nana tace taje bata ga kowa ba se Yaya Jawwad a parlor

Jawwad ya kalle ta yace

“Baby ya akayi ne?” ba tace masa komai ba se dai dan shiru da tayi tana nazarin dakin, tana kokarin gano wani abu, kaman kamshin turaren Jalal take ji, Jawwad yayi murmushi yace

“duba wancan bedroom din yana ciki, nasan shi kika biyo”

Ba tareda tace komai ba ta nufi dakin da Jawwad ya nuna mata da sauri, ga mamaki kuwa tana zuwa tatarar Jalal yabawa kofa baya, sanye da dogon wandon jeans da vest a jikin sa yana waya, da gudu ta tafi ta rungume shi ta baya, dan murmushi yayi yai sallama da wanda yake wayar da shi, ya aje wayar ya juyo da ita suna fuskantar juna, har hawaye ya wanke fuskarta.

“Ohhh am sorry dear, waye ya gayamiki ina nan ma tukuna?”

Shigewa jikinsa ta kumayi ta kankameshi kamar wani ze kwace mata shi ta sake fashewa da kuka.

Jalal yace “Subhanallah Kin san bana son kukanki, gayamin me yasa min ke kuka?”

A hankali ta fara magana cikin kuka “Am sorry Jalal, Am sorry”

“Aini bakimin komai ba, kidena kukan nan please”

Kasa denawa tayi, Hawaye ne wani na bin wani keta zuba daga idon ta.

Jalal yace

“Am sorry My love, ni nayi miki laifi, tsawon wannan lokaci dana boye miki nasan inda Ummi take, am very sorry ba laifina bane”
Tasa hannu ta toshe masa baki tareda girgiza masa kai.

“Nina yi maka laifi zaujee”
A hankali ta durkusa akan gwiwowin ta, ta rike kafafuwan sa tareda fadin

“Jalal nagode, bani da kalaman dan zasu nuna maka godiya ta, Allah ya biyaka da gidan Aljanna, sannan Kayi hakuri Jalal abunda na dinga yi maka a baya please forgive me”

Ba karamin mamaki abunda Jalila tayi ya bashi ba, da hanzari ya dagota ya zauna ya rungumeta a jikinsa, cikin sigar rarrashi ya fara magana

“Jalila laifin me kikayi min dana cancanci haka? Nima Ummi uwata ce”

Cikin tsokana yace “yarinya seda Ummi ta sameni sannan ta haifeki fa, kidena min wata godiya abunda nayi kaina nayiwa, sannan ni ba abunda kika yimin dana cancanci ki durkusa kina bani hakuri haka, ni yakamata in durkusa in miki godiya, Bayan Jawwad ban taba tunanin akwai wanda ze damu da al’amurana kamar ke ba, kalli rayuwar da nayi a baya, kalli wadda nake a yanzu, kinsaka rayuwar ki a cikin hatsari saboda ni, wani nasani wani ban saniba, abubuwam da kikayi min a baya kuruciya ce, kuma kinyi ne saboda kina kyamar mummunar Rayuwar da nakeyi, Thank you very much for all what you did for me, kin kawo canji mafi girma a rayuwar ABDUL JALAL, I love you so much my wife “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button