ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

..
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680

..????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 1️⃣5️⃣ 68

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

    _MY FIRST NOVEL _

A razane Ilham ta cewa Jalila
” Ubanwa ya gayamiki wani abu na zuba a ciki, ke bayan munafunci hada sharri a lamarin naki, ai na dade da gano sonshi kikeyi, kalleki a haka kaman ta Allah amma tsabar rashin tsoron Allah da idona na ganki kina rungume Jalal, se anyi magana kice aike basanshi kike ba, in ba sonshi kike ba uban me ya kaiki jikinsa, meye naki nasamun ido iyee, munafuka kawai” Jalila tai murmushi tace “inkika daga murya kanki zaki tonawa Asiri baniba, danni ba ruwana, sannan dan na rungume Jalal, damace nasamu kema kije ya rungumeki mana inkincika mace” Jalila takarasa maganar tana dariya, tacigaba da cewa
“Ilham tsabar mugun abunkine yasa kullum idonki yake ganemiki abunda ze hanaki sukuni tsakanina da dan uwanki, amma ko makamancin so na wancan abun babu araina fatan kin gane, for now Jalal beci wannan tsafin ba sekije kiyi wani shirin kuma” tana gama fadin haka bata jira me Ilham zatace ba ta juya zata fita, Ilham tasa hannu ta janyota, ta waigo sukayi ido hudu, Ilham kaman ta fashe da kuka tace “wannan karon kinyi Nasara, amma ki saurari abunda ze biyo baya nan gaba”
“Idan har Allah shine abun dogaron mutum to a koda yaushe nasara tasace, dan haka inaji ranki, sannan kisani bani kadai yakamata kigabaya ba, Hanna ma tana nan tana target akanki, sekin kara tunani kin rarraba hankalinki, dan hanna bazata barki ba,” Jalila ta fizge hannunta tai gaba abunta. Ilham taji wasu hawaye na bacin rai suna bin idonta Allah yahadata da Jaraba, mezatayiwa Jalila ta huce ne? Gani take da za’abata wuka seta kasheta, ita hannah ba barazanace a gurinta ba Jalila tafi tsayamata a rai, da Jalal yaci abun nan da yanzu anmawo karshen komai, amma Jalila ta wargaza komai, ajiyar zuciya Ilham tayi “dole in sanar da umma abunda ke faruwa, na dauka zan iya shawo kan lamarin nan amma abun yafi karfina”
Jalila kam takuma silalewa ta fice ba tareda kowa ya ganta ba ta tafi gida. Koda Jalila takoma gida, sabgoginta ta shigayi, amma takan tuna nasihar da Jalal yaimata dazu, babban abunda yabata mamaki yace jikinsa yana bashi ummi tana raye fatanta Allah yasa hakane ummi tana raye, har akayi sallar isha’i sannan Nana ta dawo gida, da fara’arta ta tafi gurin Jalila ta zauna, Jalila ta kalleta “se yanzu kika dawoko? Dan kinga Abba bayanan” “Aiko yana nan baze hananiba, Allah sarki Yaya Jalal se murna yake yaga yan uwansa”
“Hmm Nana ai dan uwa dadi ne dashi, sedai abun tausayin naga yan uwannasa duk nutsatsu amma banda shi”
“ya akayi kika gansu bayan kina gida?” “naje naga palourn a cike bazan iya wucewa ba dan haka na dawo” Nana ta dan girgigiza kai “bari kawai Jalila, Jalal abun tausayi ne, Allah ya kyauta kawai” daga nan Nana bata kuma cewa komai ba ta tashi, ta bar dakin
Jalila ta dauki wayarta ta hau internet, batun abunda yafaru da Alhaji Kabiru ya zaga duniya, hada masu kara abunda ba’ayiba, yan makarantarsu Jalila kuwa se murna suke da kama su Sameera da akayi suke, dama dayawa suna jin haushin su Saleema, sabida yadda suka gallabi makarantar, ga bata yaran mutane dasuke, se zancen ake tareda Allah wadaran da suu saleema ace ankamaka kaida mahifinka a gidan karuwai,
Jalila tace dole taje station din da aka kai su Alhaji Kabiru, kuma yanzu amfanin Yallabai Sulaiman yazo. Don kuwa setayi me yuwuwa ta tabattar da ta kawo karshen Jeje da Alhaji Kabiru, taji dadi da Allah yasa aka kama da jeje a wannan kamen, Dagashi har Alhaji Kabiru sesunyi danasanin shiga gonarta, Tagama abunda takeyi tana shirin kwanciya, sa’ada tace “ya haja? Ba dakin halima zakije ki kwana ba ai dakin zaki barmana malama, mu a ina zamu kwanta” shiru Jalila taimata tana kokarin jan bargo, Naja tasa hannu ta rike bargon “malama maganafa ake miki, ki tashi ki bamu guri kitafi dakin yan aiki ku kwana a can dan bazamu kwana dake a daki daya ba” mikewa Jalila tayi a zaune, ta kalli su Naja “da Abba yake gina gidan nan gudunmuwar nawa ubanku ya bayar” bude baki sa’ada tayi “ke karki sake ki zagarmana uba wallahi, dan kika zagi ubanmu semunyi kasa2 dake”
“inna zage shi mekuka isa kuyi, aiba karya nayiba, in ya kawo gudunmuwa lokacin da ake gina gidan nan ku fadi nawane a biyaku, kudena min gori, inkuma bebada ko sisi ba, kar shashar data kara cewa inje in kwana a dakin me aiki, tunda ba da gudunmuwar tsoho a gina gidan alfarma akemuku, koni nawa iyayen ba mutane bane da kuke zaginsu ? Inkun ji haushi a daren nan kukoma gidan naku iyayen, kuma wallahi duk wadda takuma yimin maganar banza sena gayamata maganar dabazata iya bacci ba” ta juya ta kwanta akan pillow tana murmushi. Haka suka hakura suka tafi dakin Maama suka kwana a can, dan Jalila ba karamin taurin kai gareta ba.
Hannah duk ta rame sabida dorawa kanta masifar son Jalal dakuma kishinsa, tayiwa kanta alkawarin muddin bata aureshiba sedai ayi biyu babu, dan in har tana raye bazata bari ya auri wata mace ya zauna da ita ba, kodai ya aureta cikin dadin rai, kokuma ya aureta kota tsiya, yanzu yazma dole ta hada kai da jeje, ta yaudareshi su hada kai taga bayan Ilham, Ita Jalila nata me saukine, Ilham ce tafi tsayamata a rai, ta dakko wayarta taita kiran lambar Jeje, amma taki shiga, tayi2 harta gaji ta hakura, da niyyar gobe taje ta sameshi, (bata san ankama shi ba)
Da sassafe wayar Jalila tafara ringing, cikin magagin bacci ta kai hannu ta daga wayar, muryar Jawwad taji “Am sorry baby na tasheki ko?” ya fada a hankali
“bakomai Yayana, fatan ka tashi lafiya”
“Lafiya kalau, hope kinyi bacci me dadi?”
“Alhamdilillah yayana” “yawwa baby wata alfarma nake nema a gurinki”
“fadi kanka tsaye komenene indai zan iya dole ayi shi”
“Yawwa baby, kinga a gidansu Jalal na kwana muna tareda su mahmud, gari ya waye babu alamar Mummy zata basu breakfast, na shiga cikin gidan yanzun naga ta kulle kitchen dinta, daddy kuma ya fita kiran gaggawa da akayi masa da asuba ya tafi Abuja, to banason Jalal yasani, dan Allah ki dafa abunda yasamu abawa bakin nan” mamakine ya cika Jalila to meyasa Mummy zatayi haka, meye ma’anar hakan datayi, ajiyar zuciya Jalila tayi
“bakomai karka damu, zan hada abunda ya sawwaka inkawo”
“Yawwa Baby, Allah yayi miki Albarka”
“Ameen bloody” gajiyar jiya bata saki Jalila ba. ta tashi ta tafi kitchen ta dora girki, ba a dade ba Nana ta fito taji karar kwanuka a kitchen ta leka setaga Jalila nata fama a kitchen “Jalila kekam meyasa ba kyason hutawa rankine, da sassafen nan kowa na bacci kekina kokawa da kwanuka, gashi gajiyar jiyama bata sakeki ba”
Jalila ta gayamata duk abunda yafaru, Jinjina kai Nana tayi tace “Tabdijan itakam har yanzu Mummy abu baya wucewa a gurinta, to Allah ya kyauta”
Da mamaki Jalila tace “meye baya wucewa a gurinta? ” Nana tace
“manta kawai, bari inzo in tayaki, bekamata kiyi aikin keka dai ba” Nana ta tayata suka karasa aikin, duk yadda Jalila taso Nana tagayamata wani abu, amma Nana taki ta basar da zancen. Maama tafito kitchen zata dauki plate, Jalila tace “Maama ina kwana” “lafiya” shine amsar data bawa Jalila, ta kallesu “wai wane irin girkine da har yanzu ba’a gama breakfast ba”
Nana tace “Yaya Jawwad ne yasamu aiki, mummy tahana bakinsu Abincin safe” dan zare ido Maama tayi
“Are you serious, ita har yanzu bata dena wannan abunba? Itama dai Mummy by now yakamata ace komai ya wuce, kodan danta, amma Ai shikenan”
Se Karfe tara na safe Suka gama aikin Abincin, suka dauka suka kai gidansu Jalal, a palour suka tarar da wata mata me fara’a, tana kama da daddyn Jalal sosai, zatayi shekara talatin da biyu, Jalila bata santa ba amma dagani tasan yar uwar daddy ce, Nana ta santa, suka gaisheta, ta amsa musu cikin fara’a, suka tsaya suna hira da Nana, Jalila bata da saurin sabo, gashi bakomai take ganewa a hausar matar ba, dan haka Jalila ta mike takoma gida ta dakko sauran kayan, tana dawowa tundaga harabar gidan tafara jiyo hargowar Jalal kaman a filin yaki, a ranta tace “jarababbe Allah yayi dare gari ya waye a gaban mutanen ma baze dena wannan jarabar ba” tana shiga palourn ta ganshi a tsaye a gaban Mummy idonsa jawur yana surfa masifa, wata mekama da wadda suka tarar a palour dazu tana rikeshi tana masa magana da yarensu, cikin fushi yake kallon Mummya yana cewa
“Wace irin macece ke mara Adalci, ai Abincin banakibane ba dazaki hana ‘yan uwan babana ci, kodaga gidanku aka kawoshi, amma kinsan ki diba har kibawa wanda basu kamata ba, akanme dan uwansu ne yake nema yakawo zaki hanasu Abinci, ke wace irin mara adalcicene meyasa kika fiye sonkanki, su basuyi fushi dakeba seke zakiyi dasu, why? Mummy why? Wace irin zuciya ce dake haka”
Mummy tace “Jalal nikake ciwa mutunci agaban mutane, kake zagina a gaban mutanen daba kaunata suke ba, nikake gayawa wannan miyagun maganganun, uwarkace nifa nikake ciwa mutunci haka” takarasa maganar tana hawaye, jiyo hargowane yasa Ilham ta fito da sauri daga dakinta, don ganin meyake faruwa, ta tarar Jalal yanata baka’i
“Eh nayi din, dan sunfiye minke a matsayin uwata, haifata kawai kikayi amma sam bakisauke hakkinki na uwaba meyasa kikazamo uwa a gareni, a rayuwata sam banyi dacen uwaba, kowani da yana farinciki yana murna in aka ambaci uwassa amma bandani Jalal, baruwanki da ya rayuwata zata kkasance se cikar miyagun burikanki sukikasa a gaba, har yau kinkasa yin nadama akan rayuwar da nakeyi saboda rashin kulawa irin taki, dakuma laifukan dakika aikata a rayuwarki, wallahi mahaifina da danginsa sun fiyemin ke wallahi” cike da masifa da bacin rai Jalila tafara magana
“ABDUL JALAL Kaji kunya wallahi, agaban mutane kake gayawa mamanka wannan maganar, ba ladabi babu da’a ba komai, kome tayi maka tunda tariga takawoka duniya tagama yimaka komai, kalli ‘yan uwanka dasukazo kowa a nutse tunda ga fuskarsu shigarsu da kamalarsu amma banda kai, ta yaya kake tunanin zaka cigaba a rayuwa da wannan wulakancin da kakewa mahaifiyarka,kana tozartata kana nunawa duniya kai baka da tarbiyya, tirr da hali irin naka Jalal, Allah ya shiryeka inme shiryuwa ne, ba yadda za’ayi kaga haske ko cigaba a rayuwarka alhalin kana tozarta mahifiyarka, tir da halinka wallahi”
A mugun fusace ya juyo, ya kalleta ido cikin ido, kan Jalila yayo gadan2, itakuma taki motsawa balle ta gudu, kafin ya karaso gurinta, matar dazu dasuka tarar a palour tashiga tsakaninsa da Jalila, tana girgizamasa kai “Allah ya huci zuciyarka, kayi hakuri, ka kyaleta”
Yare ya canza yana magana,ya cigaba da tunkaro su idonsa jawur cike da masifa, tareda kwalla, ya nuna Jalila yanawa matar magana da yarensu, a cikin maganar da Jalal yake taji ya ambaci sunanta, JALILA!!!
Abunda tunda take bata tabajiba, sedai yace mata ke, koyace wannan yarinyar kokuma yacewa Jawwad kanwarka,
Matar tacigaba da bashi hakuri da yarensu, ta kalli dayan tace “mahmud jashi kufita, kabashi hakuri” Mummy tuni tabar palourn yayinda Ilham agabanta akayi komai, Nana ma rasa bakin magana tayi,
Matar nan taja hannun Jalila suka fita daga palourn, bayan gidan taja Jalila ta zaunar da ita akan wasu fararen kujeru, sannan itama ta zauna ta kalli Jalila tace
“Dama kece Jalila?” Cike da mamaki Jalila ta kalleta “Eh nice, ya akayi kika sanni?” Ajiyar zuciya matar tayi tareda murmushi, “kece baki sammu ba, amma mu duk munsanki ai”
“Amma naga bamu taba haduwa ba, ya akayi kuka sanni”
“ba abun mamaki baneba Takwararmu, duk family dinmu munsanki, amma meyasa kikewa Jalal hakane?” da mamaki Jalila ta kalleta
“me nayi masa kuma?”
“duk lokacin dakika bata masa rai seya gayamun, kina yawan sakashi fushi meyasa?” dan dauke kanta Jalila tayi tace
“Anty Jalal baya kyautawa abunda yakeyi, kullum yana jefa rayuwarsa a cikin hatsari, ace mutum yakai munzali kaman Jalal amma ace kullum cikin sa’insa yake da mahifiyarsa bekamata ace yana daga mata murya haka ba? Banda sauran abubuwa dayake dabasu dace ba, kema kinsani, amma meyasa bakwa zuwa inda yake maybe dakuna zuwa da ganinku zesa yarage wasu abubuwan da yakeyi, rayuwarsa ta gurbace dayawa, baya ganin girman kowa, shaye2 shine babban abokin rayuwar Jalal, be damu da ibada ba sam, ko abokan kirki bashida su sena banza, yayi shaye2 a club yayi a gida, kuma ko a gaban waye, baya ubangiji, da sauran abubuwa marasa dadi dayake aikatawa”
Ajiyar zuciya matar tayi
“Jalila tabbas maganarki gaskiyane, Jalal baya kyautawa duk rayuwarsa ta gurbace, amma meyasa kika damu akansa haka?” Jalila tace
“nima bansaniba, kawai dai soyayyar da Jawwad yakemasa ne, dakuma kokarin dayake dan ganin Jalal ya shiryu yasa banajin dadin abunda Jakal yakeyi”?
“kin taba tunanin meyasa babu soyayya da tausayi na da da uwa a tsakanin Jalal da mahifiyarsa?”
“eh nayi wannan tunanin, amma nakasa samun amsa, nayi2 Jawwad yagaymin amma yaki”
“meyasa baki tambayi Jalal dinba?” zare ido Jalila tayi “taya zan tambayeshi nida muke fada, ya shakeni a banza” murmushi tayi “baze shakeki ba Jalila” Jalila ta kalleta
“tab lallai wallahi ze iya shakeni, har dukana yakeyi” matar tayi murmushi “Jawwad yacika dan uwa nagari, daya boye sirrin Jalal, dukda a yau zamu bar kano, zamu koma garinmu, tunda matar gidan bata son zuwanmu, amma yanzu a takaice zan baki labarin waye Jalal, sannan ya ingaya miki ya akayi muka sanki, idan nabaki labarin sekiyi masa alkalanci”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button