ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jalila ta koma gida cike da farinciki jin kamshin Nasara tana saka ran tunda aka kama Jeje to ko Jalal be dena shaye2 ba ze rage sosai, tunowa tayi a halin da yabar Asibitin
“ko yana ina yanzu?, Allah yasa yazo gida lafiya” ta shige cikin gida abunta, tana shiga Nana tace “Jalila ina kika tafine?”
“Hmm kedai bari kawai, gidansu Zahra naje, amma ai gani na dawo”
“Kinci sa’a Abba baya nan, shiyasa kika samu sake” Murmushi Jalila tayi tace “Aiko yana nan ma baze ce komai ba”
“kyaji dashi dai, anjima ze dawo yayo waya ya tambayeni kina ina? Nace masa kindan fita”
“Dagaske anjima ze dawo? Bari inzo inshiga kitchen dole in kintsa cikin Abbana, wannan karon ya dade a lagos” Nana tai murmushi “‘Yar gidan Abba, dama yafi sonki akanmu” Jalila dariya tayi ta wuce cikin daki, ta shiga da Sallama amma Naja bata amsaba sema wani dogon tsaki data ja, Jalila ko a jikinta bata damu ba, dan ita nasarar data samu ta fiye mata duk wani neman magana da Naja takeyi, Jalila tanemi guri ta ajiye jakarta da hijjabinta, Wayar Jalila ce tafara ringing ta duba taga Hanan ce, Murmushi Jalila tayi ta daga wayar, tace “Hanan wai yaushe zaku zone?”
“ke ba gaisuwa ba tambayar ya nake se yaushe zamuzo, idan munzo mezaki bani?”
“Ba’abunda bazan baki ba, yau ina cikin farinciki, nasamu Nasarar daban taba zaton samunta ba”
“Wannan wace irin Nasarace kekuwa kike ta murna haka?”
“Bazaki gane ba, bakina akwai magana sosai, kedai kawai sekunzo”
“Gaskiya kifara gayamin yanzu dan zaki barni da tunani”
“Gaskiya bazan gayamiki yanzu ba, innafara bazan iya gamamiki ba, kuma zakiso kiji komai, kawai se kinzo dai”
“Amma naso kifara gayamin yau, daddy ya kira Abba, amma yace yana Lagos kifara hada kayanki zebamu ke, tare zamu tafi Bauchi”
“Eh dama yau ze dawo Abban, Wayaga Jalila a Bauchi, zanga gari inci waina inture”
“Ji kwadayayyiya, ke burinki kici waina, to bazakici wainar ba” sukayi dariya gaba daya, Hanan tace “Baby, ina Abun kaunata” dan jimm Jalila tayi sannan tace “kinada lambarsa ai, meya hana ki kirashi”
“Ban niyya ba, ke nakeso ki amsamin”
“Yana lafiya” Jalila tafada a takaice
“Kimikamin sakon soyayya, kigaya masa kullum yana kawwame a cikin wani bigire me girma a zuciyata, I Love Him, Kaunar Jawwad a jinina take, kigaya masa ina nan zuwa sati me zuwa, in ganshi”
“Kan bala’i wane Jawwad din, ke banason karamin karauwanci, kobaki San anmasa mata bane?” NaJa ce take masifa daga gefe jin an ambaci Jawwad, dayake duk wayar da suke tana ji, Hanan tace “Jalila se anjima ki isarmin da sakona gurin abun kaunata, ba ruwana da kowace mace ko mata hudu aka masa Wallahi seya saki daya ya Aureni, sannan kigayawa me maganar nan Hanan tafi karfin tayi karamin Karuwanci se babban Karuwanci me lasisi, sati me zuwa Insha Allah zan shigo kano, zan gwada mata nawa salon karauwancin, ki gaida mutan gidan” Hanan ta kashe wayarta. Naja ta hau bala’i ta inda ta shiga bata nan take fita ba, yayinda Jalila ta samu guri ta zauna ta dinga kyalkyala dariya, tace “Allah ya kaimu my Hanan tazo, za’a sha drama, zanga yadda zata kaya, agama mu fece Bauchi in garin dadi in zamana se ankuma ganina” Hakan yakara bakantawa Naja rai, ta tashi fuuuu tabar dakin, Seda Jalila tagama dariyarta sannan ta mike lokaci2 Jalal yana fado mata a rai. Kitchen ta tashi ta tafi, ta tarar an Aiki Nana, ta shiga tafara Kokarin dora sanwa musamman dataji batun Abba ze dawo, tana tsaka da Aiki Jawwad ya shigo ya sameta
“Sannu kukunmu, kullum cikin adanamana cikinmu kike, weldone baby” ta juyo ta kalleshi tana murmushi
“Allah yatemaki babban Yaya, da girman kujerarka, Nace Yaushe za’a dakkomin Abban, na dade ban ganshi ba fa” takarasa cikin shagwaba, karasowa yayi gabanta yace “Autar Abba saekin rikici anjima kadan zanje dakko shi ai”
“Yawwa naji dadi sosai, Ina dan uwanka ne?”
“daga gurinsa nake, bayajin dadi ya kwanta bacci”
“Meyasameshi haka?”
“Jalal ba a rabashi da damuwa, be gayamin ba, yace yana bukatar hutu ne kawai” dan jinjina kai, har cikin ranta takejin tausayin Jalal, hawayen dataga yanayi dazu a Asibiti ya tsaye mata a rai, basarwa tayi tace “Yaya Su Hanan zasuzo a cikin next week Insha Allah, zamuje Bauchi in Abba ya yadda”
“Bauchi kuma? Zasu daukemin ke?”
“Ai bazan dade ba ai, nima zanga gari sosai”
“Bawani nan nidai bansoba gaskiya, banason kiyi nisa dani” tai murmushi tace “Hanan tace inmiko mata gaisuwa, tace in gaisheka”
“nifa nayiwa Hanan laifi Jalila, da tana kirana mu gaisa amma yanzu ta dena”
“Karka damu Yaya Jawwad, nasan halin kayaya don’t mind her”
“Kinsan banason in batawa kowa rai ni”
“Ni zanbada wannan shedar akanka, kai abun sone ga kowa Yaya Jawwad, Irinka basu dayawa ko a cikin mutane shiyasa……..
” To maye bita zaizai” gaba daya suka juyo, Maama ce itada Naja a kofar kitchen din, suka karasa shigowa
“Jawwad ban isa in gayamaka magana kaji ba saboda wannan shegiyar yarinyar ko? Sam kaki saurarar Naja kaki kulata, ka tare a gindin wannan ‘yar macen, to wallahi baka isaba Jawwad, Akan yarinyar nan idan na juya maka Baya sedai kanemi wata uwar baniba” da Sauri Jalila ta kalli Maama, Naja se kara zigata takeyi, Maama tace
“Eh kalleni da kyau, munafuka Mayya za’ a mallakemin da kaman yadda uwarki ta mallake ubanki aka dinga wulakanta ni a lokacin, wallahi baki isaba kinyi kadan, kuma dan uwarka dan ubanka Naja zaka Aura, kekuma kije kinemi mara mutunci mara Asali irinki, ba dana ba dan dangi gaba da baya”
Jawwad yace “Maama dan Allah kiyi hakuri, kidenai gaya mata haka”
“Wato bakason bacin Ranta, gara batamin Rai akanta ko? Nikae gayawa abunda zanyi, ka kiyayi bakina Jawwad” A hankali Jalila ta tako ta rabe gefen Maama zata wuce, Naja ta kamayi mata Gwalo, bata kulata ba ta wuce daki.
Tana zuwa daki tasamu gado ta Haye, ta sunkuyar da kanta se Hawaye wani nabin wani, Jalila ba karamin dagawa Maama kafa take ba amma sam ita bata gani, amma lokaci yana zuwa da zata gane kuskuren abunda take mata, amma tayiwa kanta Alkawarin seta koyawa Naja hankali. Koda Nama ta dawo tayi mamakin ganin Ran Jalila a bace, tabarta da fara’arta amma ta dawo ta tarar da ita rantaa a bace, Nana tace “Jalila nasan wasu lokutan zaman gidan nan baya miki dsdi, mussaman da Naja ta dawo gidan nan, amma kiyi hakuri komai me wuce ne, dukkan tsanani yana tareda sauki”
Murmushi Jalila tayi tace “Ni nace miki ammin wani abunne? Bana jin dadine kawai”
“Amma ai idonki ya nuna kuka kikayi”
“Baki yadda dame ma fada ba kenan”
Nana tace “shikenan Tashi muje, tunda kin kafe, amma idonki ya nuna akwai damuwa, muje mukarasa girkin” Jalila tai kokarin ta danne damuwarta sucigaba da aiki amma abun yaki yuwuwa, ko yaya Nana ta kauce se Jalila zubda Hawaye, ita kanta tasan tana Hakuri da kauda kai akan wasu abubuwan.
Da la’asar sun kammala komai Jalila tayi wanka ta canza kaya, amma duk ranta ba dadi, tasan Jawwad ma yana nan ransa babu dadi, da sunci karoda Naja seta dinga yar mata da miyagun maganganu, ga Maama agurin babu damar ta rama,
“Ai wallahi Maama mungode Allah, danginmu a tsarkake muke, ai karshen masifa a hada maka zuri’a da Arna” Maama tace
“Godewa Allah kam yarinya, dukkanmu musulmi ne, babu shegu babu Arna” Naja tace
“Maama ‘ya’ yan halak dinma im aka bincika wasunsu shegune, dan Arna da Auren suma bin maza suke”
A fusace Nana tace “Naja waike dabbar dajin inace? Wani irin hauka… Maama ta katseta ta hanyar cewa
“Rufemin baki ko make miki baki, aiba karya tayi ba kudinma babu tabbas kun hada jini da ita”
ficewa Jalila tayi gaba daya daga cikin gidan tafito harabar gidan. Nanna ta yunkura zata bi bayan Jalila Maama tace “wallahi kika bita sena baki mamaki, wuce ki zauna daga nan inta tafi karta dawo, haka Nana ta koma ta zauna”
Koda Jalila tafito harabar gidan, taga Manu driver da abokansa, a harabar gidan suna gyran flowers, ta duba taga bataga motar Jawwad ba, dan haka ta wuce part din Jawwad, ko ganin gabanta batayi, ta samu gefen kujera ta zauna ta toshe bakinta tafara kuka, bata son kowa yaganta balle a rarrasheta ta zauna tana kukanta, tanajin yadda ranta yake mata zafi. Tana tunanin meyakamata tayi ta huce yadda Maama ke wulakanta ta, bata son gayawa Abba halin da’ake ciki, tasan hakan ba karamin matsala ze jawowa Maaman ba, tana bukatar wanda zata gayawa damuwarta koba komai ta rage damuwa, tasan Hanan zigata zatayi tayi rashin mutunci, gashi ita bada kowa ta yadda ba, balle tagayawa wani abunda ke damunta,, tana cikin tunani tareda kuka taji magana
“Meyasaki kuka haka?” bata san da mutum a dakin ba, dan haka ta juya da sauri da doguwar sumarsa ta ganeshi, sam bataga kowa a dakin ba, shiru tayi tacigaba da kukanta, karasowa yayi gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ji tayi duk ya takurata a hankali yace
“Meyasaki kuka haka?”
“dan Allah nika kyaleni, ina ruwanka da kuka na”
“Inada ruwa da kukanki, kamar yadda kike da ruwa da Rayuwata, now talle me what happens?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button