ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Mahaifin Jalal ya hada mahaifin Jawwad da manyan mutane akan harkar kasuwancinsa, wanda silar hakan Allah yasawa mahaifin Jawwad nasibi a kasuwancinsa, yasai gida a Sharada NNDC, suka koma, Jalal yasamu daddynsa yace masa dan Allah yanaso yasaimusu gidan dayake makawabtaka danasu Jawwad sukoma, haka kuwa akayi suka tattara suka koma kusada juna, ga gida ga gida.
Har yanzu babu jituwar Arziki tsakanin Jalal da Ilham, ba Ilham bama kawai hatta mamanta Saudat basa shiri saboda hakanan Allah be hada jininsuba, wataran Saudat tazo gidan, tabawa Jalal kyautar turare, da yanuna baze karba ba, Amma Jawwad yasashi ya karba, yace masa ba a haka mutum yamaka kyauta ka gwaleshi, Tunda Saudat uwace a gurinsa, Ranar suna kwance cikin Dare, Jawwad yaji kaman ana jijjiga gadon dasuke kwance dan haka ya tashi da sauri ya kunna fitila, yaga Jikin Jalal yanata Kakkarwa, abun yabashi tsoro sosai, ya tattaba Jalal yace “Dan uwa meyasameka kobaka da lafiya ne” Jalal ya masa shiru, koda Jawwad ya cigaba da magana se Jalal ya bude idonsa seda Jawwad ya firgita wani irin Green yaga kwallarsa tayi, ga jijiyoyin kansa sun tashi sunfito sosai har goshinsa, Jalal ya rike Jawwad yace “Jawwad wani hayaki ya shiga jikina, kamin Addu’a amma karka gayawa kowa, ka dauki turarenda Maman Ilham tabani ka jefar dashi, daga ciki hayakin yake fitowa” Jawwad yadinga karanto masa duk abunda yazo bakinsa a haka har bacci ya dauke Jalal, sannan Jawwad ya dauke turaren ya boyeshi, Jawwad beggayawa kowa ba kaman yadda Jalal ya bukata.
Tundaga nan Jalal yafara zama wani iri, Suna SS2 Jalal yafara haduwa da miyagun abokai, ciki hada wani hatsabibi waishi Jabir Junaid, suna ce masa Jeje, gaban Jalila seda yafadi jin an ambaci Jeje,
“tunda Jeje ya shiga Rayuwar Jalal komai nasa yafara lalacewa, ya koya masa shaye2, Jawwad yai kokarin ya raba Jalal da Jeje amma abu ya gagara, Jawwad be gayawa kowa Jalal yafara shaye2 ba, yayai2 amma Abun na Jalal kullum gaba yakeyi, a haka har mutane suka fara ganewa. Habib yashiga tashin hankali daya fuskanci Jalal yafara shaye2, ya shiga dakin Jalal ya tarar dashi a kwance ga kayan shaye2 Jawwad na gefensa yayi tagumi, hankalin daddy ya tashi, ya tambayi Jawwad me yake faruwa haka, nan Jawwad yaiwa daddy bayanin komai, amma be gayamasa tun asalin meya faruba, ya dai ce masa shima kawai gani yayi Jalal yana shaye2, yayi2 ya dena yaki Habib yashiga tashin hankali jin tilon dansa yafada mummunar Rayuwa, A lokacin khadija kusan watanta guda bata Nigeria, Bayan Jalal yadena maye ya zaunar dashi yaita masa nasiha yana masa fada, amma Jalal fadan nan ko a jikinsa.
Bayan dawowar Mummy Habib ya dinga yi mata fada yana cewa “Khadija a sanadin rashin kulawarki, da sakacinki Rayuwar dana ta tasamma rugujewa, Jalal yakama hanyar lalacewa, wace irin uwace ke”
A fusace tace “Nifa baangane inda maganganunka suka dosa ba, da can bakasan inada sakacin ba se yanzu?”
“ABDUL JALAL yafara shaye2, shaye2 yakeyi” Zare ido tayi “Kamar ya shaye, ni dana baya shaye2, Jalal baze hakaba”
“koki yadda kokarki yadda yarage naki, sekije ki bincika” a gigice ta fita tanufi dakin Jalal, aikuwa tana shiga ta tarar dashi yanata busa hayaki, cikin tashin hankali ta karasa cikin dakin
“Jalal mekakeyi haka? Shaye2 fa kakeyi”
Banza yamata yacigaba da abunda yakeyi, ta karaso ta nufo inda yake amma ya dakamata tsawa “Karki sake kizo inda nake tunda ba kyason bakya kaunata, bakida wata magana dazaki gayamin lokaci yariga ya kure, Mummy da hannunki kika rusa Rayuwata, kin fifita son zuciyarki akan Rayuwar danki, kifita ki barmin dakina, bana kaunar ganinki”
“Amma Jalal……..
Jifa yafarayi da duk abunda yaci karo dashi cikin tsawa yake cewa” Kifita Nace bana son ganinki, kije kudi su baki farincikin da duk kike bukata, kifita kibani guri, Jawwad ne yashigo dakin da Sauri yaga abunda Jalal yake da sauri yaje ya rikeshi, Mummy ta juya cike da damuwa tabar dakin.
Tundaga wannan lokacin Rayuwar Jalal tashiga rudani, yadena jin magana ibada ma baya iyayi, yadena ganin girman kowa, yadena ganin mutuncin kowa, kowa ya janye dansa daga shiga huldar Jalal, Jawwad ne kawai be barshiba, da mahaifiyar Jawwad ta fuskanci Halin da Jalal yafada setayi kokarin ta rabasu, saboda kar itama nata dan ya lalace. Amma abu ya gagara mahaifin Jawwad yace indai tai kokarin raba Jawwad da Jalal batayi adalci ba Addu’a yakamata tayi musu gaba daya, wasa2 abu yafara shafar kwakwalwar Jalal ya manta abubuwa saboda shaye2, a haka suka gama secondary suka shiga jami’a, Jawwad na mechanical engineering, shikuma Jalal yana karanta civil engineering, shima a university din haka yakara lalacewa da shaye2, kullum Jawwad kokari yake yaga Jawwad yadena abunda yakeyi amma abu ya gagara.
Suna level 1 kakar Jalal mahaifiyar khadija ta rasu, Jalal yazama rikakken dan shaye2, yazamana in har Jawwad bega Jalal ba to a Club ze tsintoshi. Dukdahaka lokaci zuwa lokaci Jawwad yana raka Jalal maiduguri su gaida dangin mahaifinsa Khadija tacewa Jalal bata yadda yakuma zuwa maiduguri ba, inyakuma bata yafe ba tunda dangin mahifin sa basa sonta shikuma Jalal yace sedai katta yafe, ita mutum nawane sukace basu yafe mataba, Jawwad yace masa be kamata yadinga zuwaba tunda tace bazata yafeba hakkinta ze iya kamashi, dama dangin Habib tuni suka dena zuwa saboda wulakancin Khadija.
Jalal yana shekararsa ta karshe a Jami’a abun nasa yakara ta’azzara, da yana iya karatu dukda yana shaye2, yana da kwakwalwar sosai dan yana daga cikin wanda ake ji dasu ga barin kudi dayakeyi, amma a final year kwakwalwar Jalal takara birkicewa, yakasa karatun ga mantuwa, makarantarma gaba daya yadena zuwa, se yawon club, abokansa yan iska suka kara like masa saboda yadda yake sakar musu kudi, gaba daya iyaye suka hana yaransu shiga harkarsa, suka shiga tsangwamarsa da an ganshi se a tashi abar guri yazama abun kyama, kowa ya gujeshi se Jawwad, hakan yakara tunzurashi yafara rashin mutunci yadena ganin girman kowa, memakon amasa nasiha ko Addu’a se akaita Allah wadaran da halinsa, hatta dangin Khadija basason yaje inda suke bayan abaya harsosuke yaje saboda sunsan indai yaje seya musu barin kudi, ana cikin wannan halinne Ilham ta nuna tanason Jalal a haka, hakan ya tabattar da akwai abunda Ilham suke shiryawa dan daukar fansa akan Khadija da danta, Amma hankalin khadija be kaiba itama ta goyi bayan hakan tana ganin tahaka ne zata wanke zuciyar Saudat akan abunda taimata, har zuwa wannan lokaci ake wannan turka turkar.

Kakar Jalal mahaifiyar Habib tayi kuka lokacin data samu labarin yanda jikanta yakoma, gashi kiri kiri an hanashi zuwa inda take da wannan bakincikin takoma ga Allah, tanawa jikanta fatan shiriya, amma ranar dasukazo gaisuwa suka juya, Mummy tahana Jalal kwana, wannan abun yakara bakantawa danginmu Rai, muka dauke kafarmu daga gidan Habib tsawon shekaru. Babban abun godiya ga Allah shine Jalal baya neman mata ba ruwansa da mata, ko a makaranta ko a club ba ruwanshi dasu, ze sha giya yayi askin banza, yayi rashin mutunci, baya ganin girman kowa musamman Mummynsa dayake ganin sam batayi masa adalci ba a matsayinsa na danta, tunda ta goyi bayan ya auri Ilham, da nufin ta wanke laifinta na baya yakara jin haushin mahaifiyarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button