ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Daren ranar Ilham ko na minti daya bata rintsa ba ta dau wayarta ta kira malaminta
“hello malam ina cikin damuwa fa, yarinyar nan da alamun soyayya suke da Jalal, tashin hankali na ma kar inje Aikin da akayi masa ya karye” “Aikin da akayi masa har yanzu yana jikinsa, amma kibari zuwa gobe kizo” “to shikenan nagode zanzo goben” sukayi sallama, saboda tunani da bacin rai, tarasa meyake mata dadi, sabida abunda idanunta suka gane mata yau amma gaskiya Jalila tacika yar rainin hankali taita nuna ita batason Jalal dan munafunci ashe soyayya da suke harta kai ta rungumeshi, taita nuna ita ta Allah ce amma abun bahaka yake ba, Allah2 kawai take gari yawaye ta tafi gurin malamin nan ayi duk me yuwuwa ayita ta kare!.

Jawwad har ya shirya ze kwanta, Hanan ta kirashi, kamar ya share ta sekuma ya dauka
“barka da dare abun kaunata fatan kana lafiya” “lafiya kalau hanan yaya mutanen gidan?” “duk suna lafiya kalau Alhamdilillah, kwana biyu ko nemana bakayi meyasa” “bakomai Hanan abubuwa ne sunmin yawa kawai, gashi muna daf dagama school” “Allah sarki nayi murna sannan inamaka fatan Alkhairi, Allah ya sanya Albarka a ilimin ka yasa al’umma su amfana”
“Ameen Hanan naji dadin Addu’arki nagode sosai” “No bekamata kayimin godiya ba, tunda ina sonka zanso duk wata karuwarka Jawwad, amma na lura kaman ina takuramaka ni kadai nakesonka nasan kana guduna saboda Jalila, amma nima yakamata ka tausayamin Jawwad, Abunda kakeji game da Jalila shinakeji game da kai, bazanso incigaba da takurawa rayuwarka ba, bazan so saka ka a cikin damuwa ba, zanso ka kasance a cikin farinciki koda zezama ni narasa nawa”
“Hanan yakamata ki……” “A’a Jawwad base ka gayamin komai ba, karka damu, amma kasani bazan dena sonka ba har karshen rayuwata, inasonka Jawwad, amma Insha Allah wannan shine kira na karshe da zanyu maka, bana son rusa maka farinciki, tunda na fuskanci ina takuramaka, ka gaishemin da masoyita kuma yar uwata” kafin yayi magana ta kashe wayarta, jiyayi daga karshe kaman kuka take, seyaji sam beji dadin hakan ba, dan haka yai kokarin bin layinta amma a kashe haka yaita trying har ya hakura.

Da wuri Jalila ta shirya dan tafiya makaranta, sam bata jin dadin jikinta, ta kwana da ciwon kai wadda tasan damuwa ce datayi mata yawa, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa dan duk ta rame, tana fitowa ta tarar manu yana goge mota, suka gaisa ta shige gaban mota ta kifa kanta, tana jiran manu yazo su tafi, har ya shigo ya kunna motar bata dago kanta ba, seda taji gudun yayi yawa ba tareda ta dagoba tace “Manu mutafi a hankali mana, kaina ciwo yake sosai, wannan gudun kaman zamu bar gari” shiru be amsaba kuma be dena gudun ba, dagowa tayi kawai taga Jalal ke tuka motar ba manu ba
“kaiii meye haka kuma? Ina manun?” shiru yayi yacigaba da tuki “magana fa nake maka, yauma ka dakkonine don kamin wulakanci, inkuma makara wallahi baka isaba ka ajiyeni kawai in sauka” still bekuma cewa komai ba
“wai baka jinane? Nika ajiyeni, bana son adinga gani tareda kai kar wannan shashan yan matan naka su dinga min hauka, gashi har wani yafara titsiyeni sena gaya masa alakar dake tsakanina da kai ni ka ajiyeni” “Ke!!!” seda ta tsorata, saboda yanayin da yayi maganar “idan na ajiyeki duk abunda yasameki kika sani, ba cewa kikayi kanki yana ciwo ba, amma se surutu kikeyi, wallahi kika kuma magana sena baki mamaki, in an ganmu tare duk wanda ya tambayeki kigayamasa abunda kika gadama” ba shiri taja bakinta tayi tsit, ko minti biyar beyi, da wannan maganar da Jalal yayi ba, wata mota tasha gaban tasu motar a guje, wanda ya tilastawa Jalal yin parking.

I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680

Daga Alkalamin
Aysha cool
????️????️????️????️????️????️????️????️

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 1️⃣3️⃣ 66

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

    _MY FIRST NOVEL _

Jalal bai fita daga motar ba, dayake motar tint glass ne, da mamakin Jalila motar data sha gaban tasu, Jeje ne a ciki da wasu manyan karti suka fito, suka tinkaro inda tasu motar take, knocking sukayi a side din direba, a hankali Jalal ya sauke glass sukayi ido hudu da Jeje, rikicewa Jeje yayi, cikin inda inda da mamaki yace
“J man kaine da kanka, huh ya gida amm…
“shut up please” Jalal ya katseshi, “nasan za’ayi haka ai, shiyasa na shirya hakan, Jeje baka da amana, baka da mutunci, kobataci darajar kowaba taci darajar yayanta amininane, amma saboda baka da mutunci shine ka shirya cutar da ita, kuma duk abubuwan data fada akanka karyane? Ba karya bane ba, Jeje inaso in maka kashedi, koda makamancin wasa ba kai babu ita, idan nakuma fuskantar ka shirya wani abu akanta na cutarwa, you know what am capable of doing, ka kiyaye “
” haba Jalal kai ka dauki abun a haka amma ni banyi niyyar yimata wani abuba… “Enough malam, kayimin blocking way, ku janye motarku zan wuce” cike da bakinciki Jeje yasa aka janye motar, ya shirya ya dauke Jalila yaketa mata haddi, saboda abunda tayi masa, ya dauki fansa akan abubuwan datayi masa, ya akayi Jalal ya gane shirina haka, dukan motarsa yayi da karfi, yayiwa kartin umarnin su shiga mota.
“kinga Abunda shishshiginki ya nemi ya janyomiki ko? Da kin bari kin taho ke kadai da wani zancen ake ba wannan ba” ya karasa maganar cikin fada, kallon Jalal tayi, ta dauke kanta
“waman yatawwakallu alallahi fahuwa hasbuh, dan haka be isa yayi min wani abu ba, kuma kaima baka isa ka kareni daga komai ba, ba gudu ba ja da baya wallahi koze kasheni seyayi nadamar niyyar dayayi akaina, kar ya fasa, zan nuna masa wacece ni duk Abunda nasa gaba Allah yana bani sa’a kansa, bana alwashi in kasa cikawa, duk wanda ya takaleni da sharri senaga bayansa, kodame yake takama, dan haka ba kaika kareni ba Allah ne, kuma ka gaya masa zamu gauraya dashi dan haka kadenamin tsawa”
Jalal yakara jinjinawa Jalila akan taurin kai, betaba ganin mace me taurin kai kamanta ba, bata da tsoro bata son raini, kuma abun mamakin she has a luck, kota gangamo rigima se Allah ya kwaceta. Kallonta kawai yayi yai shiru bekuma cewa komai ba yacigaba da tukinsa, suna zuwa kofar gate yayi parking, “Fita” “aiko bakace in fitaba zan fita, komeye nayimin gadara aiba motarka bace, kuma bani nace ka kawoni ba dan haka karka kara yimin tsawa” harzata bude motar, setaga wannan lecturer da Sir Hafiz ya kaita gurinsa wato Sir sagir yazo wucewa, da sauri ta kalli Jalal
“Yawwa kasan wancan mutumin?”
Kallo daya yayiwa sagir yagane shi, cousin din baban Ilham ne, shikuma meye hadinsa da ita oho, amma yace “ban saniba kifita nace” “to kayiwa kanka dama sako yabani in baka, tunda kace haka shikenan” ta fice abunta Jalal ya girgiza kai yatafi.
Karfe tara na safe Ilham tana kofar gidansu Yaseera ta kirata awaya ta fito suka tafi gidan malamin nan. Suna zaune agabansa kaman masu neman gafara, ya kalli Ilham yace “kunyi sake gaskiya, saboda aikin baya tasiri akansa yanzu sosai kaman a baya, amma yanzu mekikeso ayi” Ilham kaman ta fashe da kuka tace “Malam har za’ayi maganar aure bawan Allah nan yaki yaita min wulakanci, amma katsam naganshi da wannan yarinyar da nake gayamaka rungume a kirjinsa, hankalina ya tashi matuka” “to aina gayamiki Asiri baze tasiri a jikinta ba, yarinyar bahaka take zaune ba tayiwa Al’qur’ani kyakyawan riko, tanada ibada danhaka sedai ayi Amfani da kissa, da dabarunku na mata akanta badai sihiri ba” ya dakko wata kwalba da ruwa a ciki ya mikawa Ilham, yace “gashi nan ki tabbatar kinzuba mai wannan ruwan a Abinci ko Abun sha kin bashi da hannunki yaci, daga nan kome za’ayi baze kuma yinkurin hana Aurenku ba”
Yakuma dakko wani turare, ya mika mata tasa hannu ta karba sannan yace “shikuma wannan ki tabbatar kinyi amfani da wannan turaren, kinshafa kafin kibashi Abinda kika zuba wannan maganin” Ilham ta gyda kai, yaseera tace “to amma malam kana ganin auren nasu ze yuwu kuwa?” “in har tayi yadda nace, komai zewuce ze aureta, kiyi a hankali, kikula da kyau muddin aka samu kuskure to komai ze iya lalacewa, danba karamin hadi nayi ba, karki bari wannan damar ta wuce” sukayi godiya Ilham ta bude jaka ta debo kudi fal ta bashi, sannan suka fito suka tafi,
“Yaseera wallahi bansan ya zanyi inbashi Abu yaciba, haushina yakeji sosai, ko kallona bayayi balle yaci abun hannuna” “aikuwa haka zaki dage ki kokarta har bukatarmu ta biya, kiyi iya kokarinki kiga kin aiwatar, sannan yazakiyi da wannan yarinyar” “banni da shedaniya aini harnaga abunda zan mata kyaleta kawai” akazo inda yaseera zata sauka sukayi salkama. Ilham tana karasawa gida taga mota a bakin layinsu, rabawa tayi da niyyar ta wuce aka kuma biyota da motar, ta ja ta tsaya, Hannah ce tafito daga cikin motar, tasha gaban Ilham, kallo daya Ilham tayi mata ta ganeta, Ilham ta hade rai sosai, Hannah tacire glass din fuskarta tace “nasan kin ganeni, babu bukatar inmiki bayanin waceceni, kashedi ne nazo miki dashi, wanda sabawa kashedina daidai yake da rusa duk wani farincikin ki” “inajinki fadi abunda kikeso”
“Naji labarin za’ayi miki baiko da Jalal, dan haka nazo miki da kashedin kiyi gaggawar janye batun ayimuku baiko, inbahakaba banki in salwantar da rai ba, dan haka kishiga hankalinki, kiyi tunani” mamakine yakama Ilham, wannan maganar kuma daga ina amma ta dake tace
“Kinyi kadan wallahi, sedai muyi asarar rayuwarmu gaba daya amma kome zakiyi, wallahi indai ina numfashi baki isaba, aurena da Jalal se anyi shi” “haka kikace ko?” “bakida kunne ne, dalla matsa ni kibani guri in wuce” Ilham ta bangaje Hanna ta wuce, Hanna tace “zaki gani kuwa”
Ilham tai tafiyarta gida, Hannah ta shige motarta, itama ta bar gurin.
Yausu Jalila suka kamalla first semester exams dinsu, su sameera se kuma bibiyan zahra suke akan su tabattar data amince da bukatansu, yayinda gefe daya suke tayiwa Jalila barazana kala kala. Da Jalila takoma gida ma sabgoginta ta shiga yi, Suleman ne yakirata, ita mutumin nan yafara isarta, ta daga wayar suka gaisa, yaita mata magiya tabarshi yazo gidansu,
“dan Allah kayi hakuri babana ya bawa wani, inkazo gidanmu zega kaman ina kokarin bijirewa umarninsa ne”
“subhanallah kiyi hakuri, baki gayamin da wuri ba, bazanso kisamu sabani da mahifinki ba, amma naso ace na sameki a matsayin matar aure ina sonki sosai, a tarayyata dake ya nunamin kinada nutsuwa da ilimi, dan haka ina son mudinga gaisawa kafin kiyi aure” murmushi Jalila tayi aranta tace “gaskiya mutumin nan akwai saukin kai” a fili tace “karka damu insha Allah zamu dinga gaisawa” sukayi hirarsu sannan sukayi sallama. Yana kashe wayar taga tests din Alhaji Kabiru akan wai tana wulakantashi tsawon lokaci yanzuma ya kirata wayarta busy tama waya da wani, in bazata yadda dashiba ze hakura” murmushi tayi sannan tace
“hmm kiris ya rage zaka gane baka da wayo” ta kirashi a waya ta dinga lallabashi tana bashi hakuri tayi masa alkawarin zasu hadu ranar juma’a, haka ya yadda yaita murna. Takira Zahrah a waya tace mata tacewa su sameera zatazo gurinsu ranar juma’a, zahra ta yadda. Jalila tace “Allah yasa abunda na shirya yatafi dai2”.
A yammacin ranar ta shirya tasa nikabinta ta tafi hisba, taje takai report akan wannan gida da su sameera suke sheke ayarsu a ciki, sukayi mata alkawarin insha Allah zasu kaiwa gurin sumame, Jalila tace tanason ganin mataimakin commnder personally, yace bakomai sukaje wani office din Jalila tace “ranka ya dade gurin nan sonake kuje ranar juma’a misalin karfe hudu na yamma”
“Amma meyasa?” “saboda a lokacinne manyan lalatattun suke zuwa, abun haushin hada manyan mutane” “karki damu Insha Allah zamuje” “to shikenan nagode sosai ranka ya dade” Jalila ta taho gida cike da farinciki tareda fatan Allah yasa su afka tarkonta, sesun kunyata tun a duniya, daga nan ta taho gida, tana zuwa gida Jalila tasamu Nana tace “Nana kece me sauraran radio, dan Allah inaso kibani lambar wani gidan radio inkina da ita wanda kikasan in Labari yajemusu se duniya taji”
Nana tace “ikon Allah yaukuma me za’ayi da lambar radio, Allah yasa dai ba wata rigimar kika kwaso mana ba” “ke haba dai, nima sonake indinga jin radio yadda nima zan dinga kira inji muryata a radio” Nana tai murmushi “to shikenan na dauka wata rigimar za’a kwaso mana ne” Jalila Allah 2 take asabar tazo taga yazata kaya. Ta kaiwa daddy Jalal list din abunda take bukata na girkim da zatayiwa bakinsu.
Jalila tagayawa zahra cewar tacewa su Sameera karfe hudu na yamma zatazo gidansu.
Ilham duk wata hanya data san zatabi domin janyo hankalin Jalal hartasamu damar bashi wannan maganin amma yaki, dan wani mugun kwarjini ya kema ta gashi ko san ganinta bayayi, gefe guda tsanar Jalila na karuwa a zuciyarta, kiris take jira tasamu damar dazata yiwa Jalila abunda se kowa ya tsaneta.
Haka nan Jawwad yakejin tausayin hanan a ransa, yana ganin kaman be kyauta ba, amma duk yadda za’ayi shi Jalila yakeso, kuma yana fatan ze aureta. Yayinda bangare Jalila tana kokarin yin baya2 da Jawwad musamman idan Maama tana nan, sabida batason tashin hankali sam, dan zuciyarta na rayamata yiwa Maama rashin mutunci wataran, shiyasa ko Abinci ta dena kai masa sedai halima ta kaimusu, iyakacinta da shi ta waya, sekuma in anyi sa’a ya shigo cikin gida kokuma sun hadu a harabar gidan.
Ranar Alhamis Jalila taje gidansu zahra, Zahra tayi murna sosai da ganin Jalila, tayi wa ummanta introducing din Jalila suka gaisa daga nan suka wuce daki, Jalila tace “ke ba zama nazo yiba, ya ake ciki kingaya musu gobe in Allah ya kaimu zakije?”
“Eh nagaya musu, zanzo karfe hudu”
“yawwa zahra to yanzuma wani abu nakeso kiyimin” “me kenan?” Jalila ta dakko wayarta tasaka wani sim din a ciki, sannan ta kalli zahra, lamba zankira yanzu, inason kicewa mutumin nan kinaso ku hadu a wannan gidan ranar juma’a, kinuna masa kaman kinsanshi a baya amma bazaki gaya masa wacece ba” Jalila taima zahra bayanin abunda takeso tayi, zahra tace “Amma Jalila…” kinga babu batun amma kawai kiyi hakan” “to shikenan” Jalila tai hiding lamba takira Alhaji kabiru tabawa Zahra, bugu biyu ya dauka sannaan yace
“Hello wake magana” zahra tace wata baiwar Allah ce, kadai kacemin baka dau murya ba”
“gaskiya bangane ba, wacece dan Allah?” “nikuma kaga naganeka ba amma in duniya da gaskiya be kamata ka kasa gane wace ba, a cikin yan matanka ne” “to aikinsan abunne dayawa” “hakane kam, amma in ka ganni zakaji kunya akan cewar baka ganeniba” “ko? To nidai ki gayamin” “bazan gayamaka ba sedai in munhadu a gidana zaka gane” washe baki yayi, “gidanki wanne kenan” ta kwatanta masa gidan dasu Sameera suke zuwa, “kazo ranar juma’a karfe hudu, semu hadu ko?” “aikuwa zaki ganni dan zanso sanin wacece?” zahra tai murmushi “to shikenan nagode se anjima” zahra ta kashe wayar, ta kalli Jalila, Jalila ta jinjina mata “weldone dear kinyi yadda nakeso, zan barmiki sim din nan a gurinki, kucigaba da waya har Allah ya kaimu gobe juma’a, komai yazo karshe”
“Amma Jalila shi waye wannan?” “ba ruwanki kedai kawai kiyi abunda nace inkuma akasamu kuskure kece a ruwa baniba” Jalila taimata sallama tai tafiyarta.
Yau juma’a shine ranar da Jalila take sa ran su Sameera su fada trap dinta, kuma gobe ranar asabar bakinsu Jalal zasuzo dan haka ta rarraba hankalin ta kashi2, tun sassafe take up and down, taje kasuwa tayo siyayyar abubuwan dazata bukata na aikace2 da zatayi, karfe uku da rabi ta shirya tasa hijjabinta da nikab ta dau jakarta, Nana ta kalleta “Jalila ina zaki hakane kiketa sauri?”
“banisa zanyiba yanzu zan dawo” amsar da Jalila tabata kenan tafito, tanata sauri a harabar gidan taci karo da Jawwad, “Baby ina zuwa haka da ranar nan? ” “Yaya zan dan fitane gidansu wata kawata”
“in hanya ne muje se in kaiki” “Aa kayi tafiyarka kawai, yanzu znadawo bazan bata ba kaji sweetheart” ta kashe masa ido tai waje murmushi yayi ya girgiza kai,
Jalila ta tafi layin gidan, can karshe tasamu guri ta zauna, tana nan zaune motarsu Sameera tazo suka shiga itada Saleema, sunyi wata irin shiga ta fitsara abun babu kyan gani, ga wasu manyan karti maza suna shiga suna fita daka gansu kaga manyan yan duniya, dan basu da maraba da yan daba. Jalila takira zahra a waya “ke ya akeciki kunyi waya yatahone?” “Eh ya taho, yacemin yana hanya, yanzu su Saleema suka kirani, wai ina inane, nace musu nakusa zuwa” Jalila tace “good kice masa ya hanzarta inbahakaba zaki fita” “to shikenan”
Ba’ayi minti goma ba da waya dasukayi da Zahra sega Motar Alhaji kabiru a layin gidan yayi parking dai2 kofar gidan da su Saleema suke ciki, yana zaune a cikin mota be fitoba, zahra takira Jalila, “Jalila yacemin waigashi a kofar gidan” “kice masa yashiga kansa tsaye” Jalila ta katse wayar tanata addu’a Allah yakawo yan hisaban nan da gaggawa, tana kallo Alhaji Kabiru yafito daga mota ya doshi gidan nan, Jalila tana ganin ya shiga gidan, takira gidan radio ta sanardasu cewar hisaba sunzo kame a unguwar dan bare kuma akwai wani gagarumin abun kunya dake shirin faruwa,
“Innalillahi wa inna ilaihi raji un” shine abunda Alhaji ya dinga maimaitawa ganin yarsa ta cikinsa Saleema da shiga rabin tsirara akan cinyar wani kato, suna shan shisha, gefe ga wasu sunata aikata badala ciki hada Sameera, a takaice dai gidane na manyan karuwai da yandaudu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button