ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jalila tuni fuskarata ta jike da hawaye tace

“kidena wannan maganar Yaya mairo, sannan kai kuma officer, this is confidential you don’t need to expose her like this baka kyauta ba”

Jalal ba kunya ya rungumo matarsa a gaban mutane yana goge mata hawaye yace

“Haba Jalila kidena kuka mana, Allah ne ya saka miki, ke da’akewa gori Ana cewa tubabbiya ce mahaifiyarki ke gashi Allah yayi ki shiryayiya, SU da suke ikrarin an haifesu a musulinci, kalli yadda suka kare, musulincin nasu a bakine, mu tafi gida kidena kuka “

Jalal yace” Yallabai zan dawo Insha Allah “

Sa’adah ta sunkuyar da kanta tana zubda hawaye, aka tasa keyarsu aka mayar dasu ceil

Sukayi sallama yasa Jalila a mota se gida.

Da sukaje gidan ma taki walwalwala, duk abun duniya ya dameta, wayarta ta dauka ta hau online aikuwa tai sa’a Nana ma tana online suka dinga chatting Jalila ta Gaya mata abunda ya faru
Nana tace “Alhamdilillah ai dama sharri dan aikene, tayi ya kuma koma kanta”

Jalila tace

“A’a Nana, a duk lokacin da musiba ta fada kan wani be kamata muyi murna ba musamman mata, duk abunda yasamu mace raguwar muce”

Nana tace

“rayuwar su dai dan bandani, Allah ne yakamasu wallahi naji dadi kuma, dan sun dade suna zige Maama, yanzu naga ta bakin zagin ‘ya’ yan wasu”

Jalal na zuwa ya karbe wayarta yaga da Nana take chatting voice message ya turawa Nana yace

“Nana ki kyaleta ta zauna ta damu kanta akan wannan mutanen, ki mata fada kema, ki gaida su Mahmud da Anty Salma”
Ita dai Jalila kallonsa kawai takeyi

Ya ajiye wayar ya zauna kusa da ita ya bude system dinshi, ya shiga wata folder ya mika mata system din, dan zare ido tayi, dan kuwa hotunan tane kawai a folder sun kusa dubu kaman yadda ya fada tun daga na jariran taka har iyanzu, mamakine ya kamata, dan wasu hotunan nata bata taba tunanin sunfita daga wayarta ba tace

“Jalal ya’akayi ka tara wannan hotunan nawa haka?”

Dan hade rai yayi yace “Jalal ko?”

“ohh sorry Zaujeee” ta fada tana murmushi

Ya dan gyara zama yace

“wasu hotunan naki tun kina gurin Ummi, wanda na nunamiki ne a gadon kaya, wasu hotunan kuma Hanan ce take turomin, Hanan ta dade tana supporting dina akanki, wasu a wayar Jawwad nake turawa be sani ba, ta saki ta turamata hotuna nikuma tana turomin”

Bude baki Jalila tayi tace

“Amma gaskiya Hanan bata da kunya, ashe an dade ana yaudara ta, inta antaya mata hotuna na tana tura maka, wayace ka kalleni ba mayafi a lokacin?”
Tai maganar tana yamutse masa fuska kaman yarinya karama.

Jalal yace

“Abunda yasa nake kallonki yanzu ba mayafi shine yasani ake turomin hotunanki ba mayafi nake kalla”

“mekenan?” ta tambayeshi

“So mana” ya bata amsa, ya dora da cewa

“Jalila kaman kina tantama akan son da nake mikine, tun a wancan lokacin da nayi kokarin in cire sonki daga raina ganin hankalinki yana kan Jawwad, Amma duk sanda nayi yunkurin yin hakan se inji ina kara azabtar da zuciya tane, Jalila so mugun ciwone, haduwar da mukayi sanda kikazo kano, nasaka miki wasika a cikin cover Al’qur”ani, amma bana tunanin kin gani, Jalila lokacin dana ganki da Ahmad seda naji kaman in kashe kaina saboda kishi, ko yan kwanaki nayi ban ganki ba sena shiga damuwa, dukda in muka hadu bawani abun arziki da ke hadamu”

Ya kalleta ya dan murmusa yace

“kinsan wataran Jawwad ya sha kamani ina kallon hotunan ki? Na maze na hade rai sedai ya kalleni ya kyaleni kawai, kwana biyu na hanashi taba wayata, abunda banayi a baya, ya dau wayar yaga na saka password yana saka sunaki ta bude, wallpaper na hotonki ne da mukayi a gurin birthday dina, aikuwa ya ritsani da tambayoyi, seda na tabattar masa dani har yanzu wannan soyayya da nake miki a baya tana nan, Amma kar ya gayawa kowa, shine yace ze shigemin gaba Indai Aurenki ze sani farinciki, Jalila na dade ina azabtuwa da soyayyarki “

Ya kwanta a jikinta yace

” please Jalila karki rabu dani, ko da ba kyasona ki cigaba da jin tausayi na dan Allah, ko iya tausayinne, nasan watakila watarn tausayin yakoma soyayya, nikam Soyayyar da Umminki tayimin da sadaukarwa da kikayimin, bazata taba bari in cutar dake ba Jalila, Ina sonki my wife ko baki soni ba dan Allah kiyi hakuri zama dani, kinfi kowa sanin halina da fuskantar abunda nake so ciki harda mahaifiyata, ina sonki”

Hannu tasa tana shafa gashin kansa, tausayinsa duk ya mamaye jinkinta, ta kasa magana, shi kuma yayi lamo a jikinta kaman maraya

Jalal Yace

“Gobe in Allah ya kaimu zaki tafi da kayanki, Munyi magana da Abba yace zakuje bauchi da Maama tunda kunyi hutun makaranta, nima zan koma lagos zan cigaba da aikina Insha Allah, amma sati biyu zanyi kawai in dawo, sannan in kun tafi bauchi karki kirani a waya, sedai in nina kiraki”

“But why?”

“haka nan kawai, zakiji dalilin hakan amma, zanyi missing dinki sosai Baby gaskiya transfer zan nema, in ba hakaba damuwa zata min yawa”

Jalila tace

“kanemi zabin Allah kafin ka nemi transfer din nan Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi”

“zamana a kusa dake shine mafi Alkhairin ai”

Tacigaba da shafa kansa a hankali tana tunani daban daban a ranta.

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣7️⃣110

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Washegari tun safe Jalila take shiri tana murnar zata je gida, gefe guda tana tunanin in taje dole ne taje ta gaida iyayen Jalal, ko wane tarba Mummy zatayi mata oho? Ga abunda ya faru da su Sa’adah har yanzu abun yana damun ta sosai, karfe goma na safe ta kammala shiryawa tsaf, ta hada kayanta, tun dare ta hadawa Jalal nasa kayan shima wanda zeyi tafiya dasu Lagos.

Jalal ma ya fito tsaf da shi, Jalila ta kulle ko ina, Jalal kuma yafita da akwatunan su, a mota taje ta tarar da shi ita kawai yake jira, ta bude ta shiga ta zauna, ya kalleta yace

“Baby ya dai naga duk jikinki a sanyaye?”

“bakomai fa” ta bashi amsa

“shikenan tunda bazaki gayamin ba”

Ya kunna motar suka tafi, koda yaje unguwar su yayi parking kin fitowa tayi daga motar, ya kalleta yace

“Fito mana, ni nakasa gane meyake damunki ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button