ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Nana duk gidan yamata ba dadi, se yanzu takejin akwai shakuwa sosai tsakanin ta da Jalila, Naja kam haushin kowa takeji musamman Nana, Nana tarasa mema zatayi taji dadi, ta dakko waya ta kira Jalila suka sha hira, bayan sungama waya da Jalila, wajen karfe shadaya Nana ta fara kwalemar dakinsu kaman yadda Jalila takanyi wani lokacin, ta hargitsa komai tana gyarawa, Ilham ce ta shigo dakin babu ko sallama Nana ta daga kai ta kalli Ilham tace “Ilham anya ba batan hanya kikayi ba yaukece a gidanmu haka, yaushe rabonki da gidan nan”
Ilham ta tabe baki tace “ba dole indena zuwa gidan nan ba na fuskaci anamin zagon kasa, dama mummy ce ta aikoni, tace ace tanason ganin Jawwad, naga bayanan, kuma bakowa a palour, kuma naji ance wannan yarinyar bata nan shiyasa nazo nan dakin, badan hakaba bazan shigoba”
Nana tace “nifa bangane mekike nufiba Ilham, wani irin zagon kasa akemiki hakane a gidan nan”?
“Haba Nana karki rainamin hankali mana, kema haushinki nakeji kun hada kai za’akwacemin Jalal”
“wai dawa kike ne haka kimin bayani dalla2, dawana hada kai za’a kwace miki Jalal din?”
“wannan tsinanniyar ‘yar uwar taki mana, Kun hade kai zata kwace min miji”
“Wai kina nufin Jalila ce takeson Jalal kokuma yaya”
A fusace Ilham tace
“Nana nifa wannan maganganun nan naki batamin rai suke karayi, ta yaya zakidinga rainamin hankali ne Nana, kina nufin bakisan kulla2 datakeyi na kokarin rabani da Jalal ba, son Jalal takeyi kuma nida ita tace seta rabamu akanme zan kaunaceta”
Naja ce ta shigo dakin ta kalli Ilham tace “to yanzu tsakanin nidake watake rainawa hankali, waini narasa wannan shedaniyar yarinya ya take? Ba’agane gabanta ba’a gane bayanta, kekince tanason yayanki, ni daza’ayiwa baiko da Jawwad yace ita yakeso, katsam sega wata jarabbabbiyar tazo wai itama shi take so, nibana gane kan wannan yarinyar sekace dan wake Allah kadai yasan gabanta”
Nana tace “Allah me iko, Allah gatan bawa, kowa ya kwaso tarkacen tsiyarsa seta jibge akan marainiyar Allah, yanzu ke Ilham keda Jalila tace miki tanason JALAL iya sanina ko shiri basayi dashi, tayay zakizo da wannan maganar kuma yanzu?”
“Nana ke kanki yanzu haushin ki nakje kina rainamin hankali, ninaga abunda baki ganiba, sonshi takeyi kuma wallahi bata isaba”
Naja tace “Ai daga ita har Nanan bakinsu daya, kedai kiyi iyayinki ki kwaci Saurayinki dan wallahi bata isa ta auri Jawwad ba daga ita har wannan kodaddiyar yarinyar, banda zalama ki hada maza kice kina so duk jarabarta ai daya zata Aura”
Ilham tace “Aikuwa ba dai Jalal ba sedai ta Auri Jawwad dan bata isaba”
Nana zuba musu ido tayi, dan tarasa mema zatayi kotace
Naja tace “Ayi mu gani ai tafi dacewa da wanann dan shaye2, ba Jawwad ba kema banda jaraba mezakiyi da mashayi, ki kyalesu taje ta aureshi suta haukan tare”
“ke gyara kalamanki ni dan shaye2 nakeso, kika fadi bakar magana akan Jalal zanmiki ba dadi wallahi”
Abu yanemi yakoma fada tsakanin Naja da Ilham, Har Ilham ta juya zata fita, ta dawo ta nufi gaban drower da Nana ta fito da komai amma banda wani Dan karamin redbox, gaban drower taje tasa hannu ta dakko Al’quranin ta kalli Nana tace “Nana ya akayi wannan Al’quranin yazo gidan nan?”
Nana tace “Na Jalila ne lafiya?”
“Wallahi Nana ke makaryaciya ce, to wannan Al’quranin Jalal ne, kakrsa ce ta fanso masa a saudiyya, yanzu gashi a gurin ta, nace miki suna soyayya amma kin karyatani”
Nana tace “kinga Ilham wannan Al’quranin fa tun wani zuwa datayi akabata shi daga gidanku, kekika kawo kayan amma kina wani zance daban”
Ilham tace “to tunda kince nina kawoshi, to yanzu zan dauka, bekamata Abunda yake na Jalal yaje hannunta ba, kinsan son dayakewa Al’quranin nan kuwa?”
“Ilham karmu yi haka dake, ki bani inta dawo sekuyi da ita”
“Inta dawo kice meshi tazo ta dauka, inta matsu ta biyoni ta karba”

Bayan Jalila tagama waya da Nana, sunyi waya da Jawwad yagaya mata yakira Abdallah yace masa sun sauka lafiya sukayi waya, ta kira Abba ma ta gasheshi, Hanan taja Jalila suka koma gurin Inna,
Suna zuwa takuma rungume Jalila ta shiga yimata hira da labarai irin nasu na tsofaffi, Inna tanada abun dariya sun dade auna hira, zuwa jimawa ‘yan mata da samarin gidan suka ding shigowa duk wanda yaga Jalila seyayi mamakin kamaninsu da Hanan kaman yan biyu, Hanan ta dinga zagawa da Jalila cikin estate din nan, suna da karamci kaman dama can sunsan Jalila tasamu kyakyawar karba, kwanan Jalila uku a garin daddyn su Hanan ya iso shida Mummynta, yaji dadin ganin irin karbar da’akayi wa Jalila, wannan karon sam Mummy bata nunawa Jalila tsana ba sema mamakin girman da Jalila tayi take.
Inna tacewa daddy “dan Allah dan nan kacewa baban yarinyar nan yabarmin ita, wallahi kamar mairona haka take, musamman intana dariya ko tafiya”
Daddy yace “haba inna, yazasu barmiki diyarsu, yanzunma sunyi kokari dasuka bari tazo nan” haka yaita lallaba Inna ta hakura.
Dukda kulawar dasuke bawa Jalila hankalin ta yana kan Jalal tanason sanin hali dayake ciki, amma bata san wazata tambaya ba.
Yau daddare Har sunyi shirin kwanciya Hanan tace “Jalila kina fama da damuwa a ranki, kuma nasan akan Jalal ne meyasa kika damu dashi haka, in ance kina sonsa kice karyane?”
“niba damu dashi ba, ni bantaba jin son Jalal a raina ba, ina tausayinsane kawai”
“karya kikeyi Jalila, kina son Jalal”
“Hanan keba wadda zan boyewa wani abubace ba, bantaba jin son Jalal ba”
“Naji bakyason Jalal, amma mekikeji akansa?”
“Ina tausayinsa ne kawai, dakuma kasancewarsa da Abu mafi soyiwa a gurina wato Jawwad, ina tausayinsa ne da son ganin yazama mutumin kirki saboda Jawwad Hanan koke kikaji labarin rayuwar Jalal zaki tausaya masa”
Nana Jalila tagayawa Hanan komai na labarin Jalal, har kokarin da tayi na ganin an kama oga KB da Jeje, dakuma abunda Jalal yagaya mata lokacin dazata taho
Hanan jikinta yayi sanyi matuka sannan takara jinjinawa Jalila da wannan namijin kokari datayi da sa kanta a hatsari a boye ba tareda kowa yasani ba
Hanan tace “gaskiya Jalal ya cancanci a tausaya masa, Amma kina ganin kowane ze iyayiwa Jalal abunda kikayi masa, Amma tsaya kinason sanin me Jalal ya ajiye miki a Alqur’ani”
“tunda muka taho nakeson Sani”
“yakamata musani, kira Nana a waya kiji in Alqur’anin yana nan ta duba mana”
“Ai in banda ke seshi Jalal ba wanda yasan me nayi”
“eh ai bazata gane ba”
Jalila ta amince ta kira Nana, seda suka gama hira da Nana, kafin Jalila ta tambaya Nana tace “Baby Ilham fa taga Alqur’anin ki wannan Jan, yau inayimana gyaran daki tazo, tace wai na Jalal ne, kakarsa ce tabashi ya akayi yazo gurinki tace inkin dawo kisameta ki karba”
A fusace Jalila tace “What!!!?

???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
_PAGE 3️⃣2️⃣85

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button