ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jiki ba kwari ta fito daga motar, Jalal yace

“muje in gaida su Abba, daga baya sekije ki gaida Daddy”

jinjina masa kai kawai tayi tabi shi, suna shiga cikin gidan kofar parloun a rufe take, Jalila ta dakko wayarta ta kira Maama, bugu daya Maama ta dauka Jalila tace

“Maama ina kika tafine, ina gida amma kofan parlor a rufe”

Maama tace

“ya salam, ai ban dauka da wuri zakuzo ba, kinga mun dan fita da Abba ne, yanzun nan zamu dawo insha Allah”

“shikenan se kun dawo” ta kashe wayar ta kalli Jalal tace

“basa nan wai yanzu zasu dawo”

Jalal yace “shikenan zomuje gida seki jira su”

Dan shiru Jalila tayi tana kallon Jalal.

“kina tsoron Mummy ne? Karki damu ba abunda ze faru muna tare, muje”

Jiki a sanyaye tabi bayansa danji take kaman tace bazata ba, tasan bazeji dadi ba idan tayi hakan, gabanta nata faduwa tana karanta addu’oi daban2, tun daga harabar gidan har cikin parlor ba kowa part din daddy ya nufa tana biye da shi, suna shiga suka tarar da Daddy na zaune na kallon labarai su Jalal sukayi sallama, ya amsa tare da waigowa, yana ganin su ya fadada murmushinsa tare da dan bude baki, ganin Yadda Jalal yazama wani babban mutum.

Jalal yana zuwa ya zauna kusa da Daddy, yayin da Jalila ta zube a gurin tana gaida Daddy, Daddy yace

“Haba Jalila zauna mana semu gaisa, yazaki zauna a kasa”

Cike da kunya da girmamawa Jalila ta dan zauna tana kuma gaida Daddy, ya amsa mata yana tambayarta ya gida. bayan sun gama gaisawa da Daddy ne Jalal ya dan risina yace

“barka da warhaka father, ya hanya?”

Daddy yace “lafiya kalau, ya gidan naka kuma? Ya ‘yartawa take? “

“lafiya kalau, ba gata nan kana gani tana lafiya ba”
Daddy yai murmushi dan tabbas inka kallesu zaka gane suna cikin farinciki

Suka zauna sukayi ta hira da Daddy, Jalila se kunya takeji tana sunkuyar da kai, yayinda Jalal kam se zuba yake yana hira, daddy yaji dadin ganin Jalal, yadda yake magana yanzu ya sha banban da yadda yake yi da babu respect a maganganunsa a baya cikin gadara yake yinsu, amma yanzu gashi yasaki jiki yana hira babu hade rai da masifa.

Daddy yace

“gaskiya Son naji dadin ganinka, kaga yadda kayi kiba kuwa, ka wani zama babban mutum”

Jalal ya kalli kansa yace

“Allah Daddy thank God, and thank my wife efforts, she’s behind the changes you saw on me, behind any successful man their must be a woman, da baku aura min ita ba ban san ya zanyi ba”

Jalila ji tayi kaman kasa ta tsage ta shige dan kunya, daddy yace

“tabbas Jalal matarka ta cancanci yabo da godiya, ubangiji Allah ya kara hada kanku, ya wanzar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakaninku, Allah yasaka miki da alkhairi Jalila”

Jalila ba tace komai ba, Jalal yace “Ameen ya Allah Daddy”

Jalila tace “Daddy ina Mummy ne?”

“bata jin dadi ne, ta sha magani ta kwanta bacci”

Jalila tace “Daddy meyasa meta?”

“kawai dai jikin nata ne bata jin dadi, gashi bata son zuwa Asibiti, likita yazo ya duba ta yabata magani”

“Allah ya bata lafiya”

Daddy yace “Ameen” yayin da Jalal ya basar kaman besan zancen da suke ba.

Daddy yace

“to nima zan dan fita ne, inada meeting dazan shiga karfe daya”

Jalal yace “shikenan Daddy seka dawo, nima daga nan karfe hudu Insha Allah zanbi jirgi zan koma Lagos”

Daddy yace “to Allah ya kaika lafiya, kafin in koma zan biyo ta Lagos din in ganka”

Sukayi Sallama da Daddy ya shirya ya fita.

Babban parlor suka dawo suka zauna suka cigaba da hirarsu kaman a gidansu dayake babu kowa a parlor.

Jalal ya kalli Jalila yace

“nifa yunwa nakeji”
Dan zare ido tayi tana kallonsa

“yunwa kuma? A yanzun”?

“Eh ni yunwa nakeji”

Jalila tace

“to yanzu meye abunyi ga mutan gidan basa nan? Gashi ban fito da komai naci ba tunda ka zama jariri”

Murmushi yayi yace

“tashi muje kitchen mu duba seki dafa mana wani abun”

Jalila tace

“kana ganin babu matsala idan mukayi hakan?”

Jalal yace “matsala kuma? Tashi muje ba wata matsala”

Ta mike suka tafi kitchen.

Ilham juyi take kawai akan gado, tarasa me zatayi taji dadi a ranta, tunda Jalal yayu aure ko bisa kuskure basu hadu da Jalal ba, gashi kaman masifa haka wutar son Jalal ke ruruwa a zuciyar ta ba dare ba rana, gaba daya ta rame tayi baki, idan ta tuna artabun da suka dingayi da Jalila a baya akan Jalal ta tuna yanzu ita ya aura, kuma har yake gaya mata wai yana son matarsa, setaji duniyar ta kara mata zafi taji kaman ta samu wuka taje gidan ta kashe Jalila, gashi yanzu fafutukar Ummanta akan ta dauki fansa ne kawai, gashi ta gaji da zigar da takeyiwa Mummy, ga ciwon so na neman halaka ta, ko Abincin kirki bata iya ci, bata taba zaton radadin ciwon so ya kai haka ba, ko da wasa batayi tunanin son Jalal ze juye ya koma mata gaske ba, ta yanke shawarar zuwa gidansu yaseera taji wace shawara zata bata, yunwa ta isheta dan haka ta sakko daga kan gadon dan neman abunda zata zubawa cikin ta.

Kunun gyada Jalal yasa ta dama masa, ta soya masa irish potatoes, ta zuba sugar da madara ta na juya masa, yasa hannu ya karba, Jalila tace

“kai zaujee se’a zata bana baka Abinci ai kabari ya huce in ka sha zaka kona baki ne”

A dan shagwabe Jalal yace

“ai ba kya bani in koshi duk na rame”

“A hakan ne ka rame, kalli ka fara tumbi fa kalli kumatunka ma”

Dariya yayi ya shafa cikinsa yace

“bafa wata yunwa nake ji ba, kawai zanyi missing delicious food dinki, shiyasa nake so inci kafin in tafi”

Murmushi tayi ta juya tana gyara gurin da ta bata tana tattarw kwanukan.

Ilham da kusan mintunan ta biyar a tsaye a kofar kitchen din ba tareda sun san tana gurin ba, taka sa daga Koda karamin yatsanta, sedai ji da tayi kaman an kunna gobara a kirjinta. Abun mamaki Jalal se dariya yake shida matarsa, cike da kulawa, yasha kayansa na mutunci sabanin a baya,wanda ganin dariyar Jalal seka shafe wata baka ga yayi dariya ko sau daya ba.

Jalal ya dau cup din kunun ya kai bakinsa, aiko yana sha ya kona harshe saboda akwai zafi sosai, aje kofin yayi yana rintse ido, tareda zukar iska cikin bakinsa. da sauri Jalila ta juyo

Tace

“subhanallah sannu wai sha kayi?, dama na Gaya maka da zafi fa amma ka sha a haka”

Janyota yayi da sauri ya hade bakinsu ya fara kissing dinta, Jalila ta tsorata sosai gaba daya jikinta yake rawa, sunyi kusan three minutes a haka sannan ya cikata ta ja da baya tana zare ido kaman mara gaskiya, ya dan kashe mata ido ya juya ya nufi fridge ze bude ya hangi Ilham ta gefen idonsa, a kofar kitchen tana hawaye basarwa yayi ya dau ruwa a fridge ya sha, ya janyo kujera dake dining din kitchen din ya zauna.

Kallon Jalila yayi ya ga yadda take rarraba ido kaman wadda aka kama tana aikata wani zunibi, ya dan kashe mata ido yace

“inkin gama zare idon kizo ki bani Abinci, lokaci yana kurewa, zanje inyi salla inyi haramar tafiya”

Kan table din dake gabansa ta aje Abincin, tana debo kuna tana hurawa tana bashi a baki.

Ilham da tayi kaman ta juya ta fasa shiga kitchen din, amma ta dake ta shiga, ko kallon inda suke batayi ba, suma basu kulata ba, Jalila ce tace

“Ilham ya kike ya gida, ranar me gadi yace kinje bama nan”

Wata uwar harara Ilham ta jefawa Jalila tare da jan uban tsaki, ita kuma Jalila tayi kaman bata gani ba, ta cigaba da bawa Jalal Abinci.

Jalal yace

“Baby badan nayi sauri nai kissing dinki ba, da tuni harshena ya kone gaba daya”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button