ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Ilham shiryawa tayi takanas ta tafi gidansu, domin taji abunda yakamata suyi, dan ita ta riga ta karaya da lamarin nan bata tunanin akwai nasara dan kullum Jalal kara bauďewa yake, babu alamar ze sakko.
Tayi sa’a ummannata tana gida, suka kule a daki kaman yadda suka saba in Ilham ďin tazo.
“Umma nifa najiki shiru ya’ake cikine? Na ďora mata sata amma Jalal bakiga rashin mutuncin dayayi min ba, wallahi son yarinyar nan yake, kincemin zakije Nijar gurin wani malamin amma shiru kullum abubuwan kara tabarbarewa sukeyi”
Umma tace “ke nayi maganar zuwa nijar, munyi waya da mutumin na masa bayanin komai, amma budar bakinsa wai yayi bincike akan yarinyar indai inason a yimin aiki akanta zan bashi dubu ďari biyar, nikuma ina naganta? Banida ita bani da wata kadara da zan sayar in bashi wannan uban kuďin, dan haka nakoma gurin wanda muke zuwa tun farko, shikuma yacemin baze iya aiki akanta ba sedai a kara watsa rayuwar Jalal”
“to Umma batun Auren namu fa?”
“shima za’ayi ne amma yace muďan kara hakuri”
“umma kenan, mu kara hakuri fa kikace? By mistake idan Asirin ya karye gaba ďaya kuma yaya zamuyi?”
“bazeyiba, malamin yabani wannan tabbacin ki kwantar da hankalinki burinmu seya cika, sena wulakanta shi shida uwarsa hada uban nasa, bana yafiya ga wanda yamin laifi”
“to shikenan Umma, Allah yasa, ni bari in tafi, zan ďan tsaya inyi siyayya”.

Dogon wandone a jikin Jalila da riga, dan haka ta ďakko katon hijjabinta me hannu tasaka ta fito part ďin Jawwad taje tana tsammanin ganin Jalal a can amma baya nan, rabonta da shiga gidansu Jalal kuwa harta manta, direct ta nufi gidansu Jalal, amma tarasa ina zatayi tasan dai be dace ta tafi part dinsa nemansa ba, fasawa tayi ta juyo tanufo gate zata fita itakuma Ilham ta shigo.
Tsayawa sukayi suna kallon kallo itada Ilham, haďe rai sosai Ilham tayi tareda yin tsaki tazo zata gifta gefen Jalila ta wuce, caraf Jalila tasa hannu ta riketa ta janyota gabanta suna fuskantar juna, a fusace Ilham tace “ke dalla malama meye haka? Meyasa bakida tunani ne?”
Jalila taja wasu seconds tana karewa kwayar idon Ilham kallo sannan tace
“banida tunani kam, dole ki fadi haka, kinsan ba’a tabani a zauna lafiya, dan haka sekinyi hakuri da duk abunda zaki gani har se kin biya abunda kikayimin”
Hararta Ilham tayi takuma kokarin rabawa ta wuce ta barta, amma Jalila takuma shan gabanta tace
“Ilham nasani tsawon shekaru ina bata miki rai, kinyi alwashi daban2 akan ganin bayana, baki taba nasara ba se wannan karon da kika ďora min sata, to bari kiji in gayamiki wani abu dabaki saniba, babu abunda zakiyi a rayuwa ki rama abunda nayi miki, na riga nagama dake Ilham, kuma Wallahi Jalal baze taba aurenki ba, nagaya miki dama muddin kudirina yayi karo da naki sena watsa naki, kudirinki akansa yaci karo da nawa na watsa shirinki watsawa ta har gaban abada zanso ingaya miki wani abu daya kamata ki sani amma ban saniba ko kinason ji”
Kallonta kawai Ilham take batareda tayi magana ba, Jalila ta ďora tace
“Ranar da Jalal ya kwanta a Asibiti, kukazo duba shi keda Mahaifiyarki kisani idonsa biyu yaji duk abunda kuke faďa, dan haka ki cirewa ranki cewar burinki ze cika, Na riga naganoki Ilham tuntuni shiyasa nayi miki illa inda ba wanda ze gani, na illata shirinki bakida wata dama data miki saura, damarki ďaya shine ki jajirce kicigaba da jarraba sa’arki kozaku daidaita”
Jalila takarasa maganar tana mata wani mugun kallo sannan ta juya tayi ficewarta, gaban Ilham ne ya shiga dukan hamsin2, kaddai Jalila dagaske take, amma to in hakane da yaji aida yaďauki mataki, “kai karyane bejiba, koma yaji wallahi seya Aureni, se burin mahaifiyata yacika”
Ta shige cikin gida da sauri hada tuntube.

Maama takasa zaune takasa tsaye, Naja batasan budurin da’akeba dan lokacin da Abba yayi wannan maganar bata nan tafita yawonta, harta dawo Maama tarasa ta inda zata fara mata bayani.

Jalila na fitowa taga Jalal ya dawo a mota, yana kokarin shiga gida, ganin da yayi ta tsaya ta ki tafiya ta kura masa ido yasan akwai magana a bakinta, tsayawa yayi agaban ta yayi parking, yana tsayawa ta zagaya inda yake, ďan ďage mata gira yayi alamar meke faruwa?
Ďan kallonsa tayi tace
“daga ina?”
“kin aikenine?” ya tambayeta
“Ohh No Allah yabaka hakuri”
Yace “Ina Jawwad ne? Na duba baya nan ban san inda ya tafiba?” hade rai tayi itama tace
“ka duba shi mana, kokabani ajiyarsa ne?”
Kallonta yayi, wato ta rama kenan
Yace “A’a ban baki ajiyarsa ba”
“dama..” sekuma tayi shiru
“Dama me?”
“inada magana ne”
“fadi ina jinki”
“toka fito daga motar mana”
“In fito kuma? Gaskiya ni yunwa nakeji, zuwa zanyi in kwanta, naje neman Abinci narasa me zanci, dama in kin bawa Jawwad nake ci nima amma yanzu baya nan nasan bazan samuba”
“Hmm to kace Ilham tabaka mana”
Hade rai yayi sosai yana Kallonta, sunkuyar da kai tayi tana dariya kasa2
“Yi hakuri, ai yanzu mundena faďa ka jirani a part din Yaya Jawwad zan kankaro maka kanzo in za kaci” tayi maganar tana dariya, tana matukar kyau idan tayi dariya, gyaďa kai yayi ta juya ta tafi, yabi bayanta da kallo harta shige gida, sannan yaja motar ya shiga da ita gida.
Gida takoma taje ta ďakko masa breakfast ďin Jawwad da yatafi beci ba, dayake da zafinsa a cikin flask, tana zuwa ta tarar dashi a zaune a palourn Jawwad yana jiranta, ta shiga tayi sallama amma be amsaba, seda tazo kansa ta tsaya takuma yimasa sallama ya ďago ya kalleta ya amsa a hankali, ta ajiye tray din tace
“Yana daga hakkin musulmi akan musulmi in yayi sallama ka amsa masa, kadinga amsa sallama please”
Shiru yayi yaki kulata, Jalila tarasa wane irin miskilin mutum ne Jalal, koma tace ďan rainin hankali kana masa magana yana jinka amma yayi maka banza dan tsabar wulakanci,
ta aje masa Abincin ta zauna a kujerar dake kallonsa. Ta danne fushinta
Ya hada Abincinsa yafara ci, can yace “Me ya kai Alqur’ani dana baki hannun Ilham?” yai tambayar kamar bashi yayi ba
“ďauka tayi” tabashi amsa a takaice
“Ya’akayi ta ďauka baki hanata ba?”
“Ina bauchi aka aikota taganshi shine ta ďauka”
Bekuma cewa komai ba yacigaba ds auna loma, can Jalila tace
“Ya akai kasan yana gurin ta?”
Kallonta yayi ya danyi murmushi
“in kinaso in dawo miki dashi, yana gurina, amma bakiga abunda na ajiye a cikiba ko?” ďan yatsina fuska tayi sannan tace
“Nifa tsawon lokacin da yayi a gurina banga komai a ciki ba”
“zan dawo miki dashi kikuma dubawa”
“to naji zan duba”
Ya cigaba da cin Abincin sa, can ta ďan nisa tace
“An baka aiki ance kaje interview kaki why?”
Ďagowa yayi ya kalleta, “dama nayi tunanin kece kikasa aka nemamin wannan aikin, tayaya ina shaye2 zakice asamomin aiki a hukumar dake yaki da shaye2, amfanin me zanyi ko nima so kike a kamani?”
“calm down let me explain, mezesa in so akamaka? da hakane naso akamaka da nasa an ka maka kaida abokinnaka jeje ai”
ďagowa yayi ya haďe rai kaman be taba dariya ba
“Am sorry banyi hakan da wata manufa ba, sedai inkana aikin na farko ze rage maka yawan damuwa, sannan ze sa ka kara kokarin kadena shaye2 kaima, at least in kana da gurin zuwa ze kara dauke hankalin ka daga kan Shaye2”
Zuba mata ido yayi yana tunani daban2 akanta, ta damu dashi dayawa, she’s so simple and calm, matsalarta kawai taurin kai da rashin kunya, Amma tanada zuciya me kyau.
Tsarguwa tafara yi da kallon dayake mata tace
“Ya dai?”
“meyasa kika damu dani haka?”
Shiru tayi dan bata san mezatace masa ba, basarwa tayi tace
“dan Allah kaje interview din nan karka watsamin kasa a ido”
“Senayi shawara” yabata amsa
“shawara kuma, dan Allah mene kuma na wani shawara dan Allah Yaya Jalal kaje please karkasa inji kunya” da shagwaba takarasa maganar
Bude baki yayi tareda yin murmushi kaman karta dena magana
“Nine Yaya kuma yau, yarinyar bakida kunya fa”
“Aida ďinma dan muna fada ne amma yanzu mundena faďa, dan Allah kaje ba dan halina ba, kaji Yayana ďan gidan daddy abokin Yaya Jawwad, badan halina ba” murmushi yayi ya ďan girgiza kai yace
“Aikuwa kinsan indan halinkine bazaniba, innayi tunani zan gaya miki”
“to Allah yasa inji alkhairi”
Be amsaba ya kai hannu ya dauki cup ya kai bakinsa amma jikinsa yafara rawa yakasa kaiwa
“lafiya menene kuma?”
Ajiye cup din yayi, yai shiru yana rintse ido”
Da sauri ta mike ta nufi inda yake tana faďin “Subhanallah meyafaru?”
Dagowa yayi idonsa yayi jawur yace
“Gi.. Giy….. Giya,…. Giya zansha, ita nakeson sha”
“giya kuma? Meyasa zaka sha giya?”
Numfashi yake ja ya mike tsaye ya nufi hanyar fita, idonsa yayi jawur jikinsa se rawa yakeyi da sauri ta sha gabansa
“dan Allah Jalal karka sha giya, meyasa idan kuma kasha ka bugu daga nan ka mutu mezaka cewa Allah? Dan Allah karka sha kayi hakuri zaka ji bakason sha”
Tureta yayi ze fita, takuma tare kofa tana masa magiya, yasa hannu ya hankadata jikin kofa ta bige kafaďa ta faďi a gurin shikuma ya fice kaman wani horrorn dayake bukatar jini.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button