ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

..
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 1️⃣4️⃣66

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

    _MY FIRST NOVEL _

Koda Saleema ta dago tai ido hudu da mahaifinta a gigice ta mike daga cinyar wanda take zaune, tana zazzare ido, gaba daya sukayi cirko2 suna kallonsa, koda ya duba yaga waye Saleema take kan cinyarsa ba kowabane illa Jeje, a gigice Alhaji Kabir yace “Saleema abunda kike aikatawa kenan, kin cuceni kin cuci kanki Allah ya isa tsakanina da ke” ya maida idonsa kan Jeje “nizaka ciwa amana, karasa da wadda zakayi lalata se yar cikina, duk halaccin danayi maka a rayuwa wallahi seka ga karshenka sekaga abunda zanyi maka, sena dau mummunan mataki akanka” Jeje rasa mezece yayi gaba daya ya rude, daga gefe wani tsageran matashi yace “wai dan Allah meyakawo ka nan gurin, kake wannan maganganun ne, nina dauka harka kazo, kaima fa ana kaimaka matan nan guest house dinka to meye dan anyiwa yarka, abunda kakewa yayan wasu nefa” seda Alhaji Kabiru ya duba sosai sannan ya gane matashin, tabass suna kaimasa karuwai yana biyansu kudi. A fusace Alhaji Kabiru ya dau wata kwalba ya nufi inda matashin yake, Saleema se kuka takeyi, jin ance itama ga abunda mahaifinta yakeyi, yana zuwa ya bugawa matashin a ka, sauran matasan sukayo kansa, duk wanda yazo seya kaimasa suka da fashashiyar kwalba.
Itako Jalila koda taga Alhaji Kabiru ya shiga cikin gidan nan ta kuma kiran yan jarida, tana gama wayar sega motar “yan hisba, tareda yan sanda, sukayiwa gidan dirar mikiya, suka kewaye shi, sannan wasu suka shiga cikin gidan, babban abun kunya da asara shine kama uba da ‘ya a gidan karuwai, nan aka tarkata kansu tsaf, Alhaji Kabiru se rantse2 yake, ga wadanda yajiwa ciwo da kwalba, Saleema banda aikin kuka ba abunda takeyi, kan Jeje se zubarda jini yakeyi,’yan sanda suka caje gidan inda akasamu miyagun kwayoyi, da kayan shaye2 kala2, kafin a tafi dasu yan jarida suma suka karaso, suka rufawa motar yansanda baya dan zuwa daukar rahoto, ba karamin farinciki Jalila tayiba, rasa inda zatasa kanta tayi dan murna, batasan lokacin dataji hawaye farinciki nabin fuskarta ba “Allah kai kabani wannan dama, Allah kaikabani nasara ba dabarata da wayona ba, Allah nagode maka, nagode da ni’imarka da kariyarka, Allah kasa sanadiyar shiryuwar bawanka ce tazo” hanyar titi ta nufo tana sauri, yamma tayi sosai, ta tafi gida gida cike da murna da farinciki.
Takoma gida tanata murna, tana zuwa ta tarar da sa’ada tazo itada Naja wai a gidan zasu kwana biyu, Jalila ko takansu bata biba, murnarta kawai takeyi,
Nana tace “Baby meye sirrin wannan fara’ar da murmushinne haka?”
“Nana nima ban saniba ina murna ne kawai” “Hmm kyama fadi gaskiya” “gaskiyar kenan Nana” sukayi dariya gaba daya. Kan kace me Labari yafara yada duniya cewar an kai sumame gidan karuwai, inda aka kamo hada wani uba da ‘yarsa tareda yaronsa a gidan” nan da nan zance yafara zaga social media, da sauran kafafan watsa labarai, inda ake ta tir da Allah wadaran akan Alhaji Kabiru.
Nana takira Jalila a waya “Jalila Allah yasaki a Aljannah, kinceci rayuwata da sauran rayukan dasu Saleema sukaso lalatawa, Allah yabiyaki da mafificin Alkhairi, Allah yabaki miji nagari me kaunarki” “ba komai Zahra, Nagode sosai nima Allah ya amsa mana bukatunmu”

Alhaji Kabiru yashiga cikin matsanancin bakin ciki, yarasa msyake masa dadi, wai yarsa yakama da wanda ya amincewa wato jeje, abun bakincikin ankamoshi da yarsa a gidan karuwai, gashi ba’asan ainihin me yafaru ba amma zance yanata yada duniya, nan yashiga tunanin waima wacece wadda takirashi tace yaje gidanta ne, in akajima ya tuna yadda yaga yarsa da jeje, se ransa yakara baci, ya kalli Jeje yace “Jabir (shine ainihin sunan jeje) Allah ya isa tsakanina da kai, duk halaccin danayi maka a rayuwa amma ka lalata min yarinya” “dama can lalatacciyace, kuma halaccin dakayimin aiba kyauta kaimin ba aiki nake maka, shekaru nawa nayi inamaka bauta” “Au hakama zakace ko, zamu fita ai zakaga abunda zanyi maka, kasanni kasan halina” Jeje ya kalleshi “kabari kaga munfita lafiya tukuna, aisena bari munfita lafiya zaka samu damar yimin wani abu, dan haka sena fadi komai” zazzaro ido Alhaji Kabiru yayi, “me kake nufine wai?” inbaka ganeba seka bari sena aiwatar zaka gane”.
Duk yadda su Sa’ada sukaso bakantawa Jalila rai bata kulasu ba dan karma su bata mata farincikinta, tabar musu dakin takoma na halima ta kwana a can, tun sassafe tai salla, sukayi aikace2 dazasuyi itada halima a cikin gidan, sannan ta tafi gidansu Jalal itada Halima, tunda Ilham tai arba da Jalila takejin kaman ta dau wuka ta kasheta, suka gaisa da Mummy ta nuna mata kitchen Jalila suka shiga suka fara abunda yakamata, aka jima Nana itama tabaro wasu sa’ada gidan ta tabiyosu Jalila a ranar suka hada snacks din dayakamata, sukabar aikin dabasu gama ba zuwa gobe, kafin bakin suzo sesu karasa, Nana da halima suka koma gida, Jalila ta tsaya tana jarasa gyara kitchen din, Jalal ya shigo da katon kwando cike da fruit ya ajiye yai waje abunsa, ta zauna ta shiryasu a fridge sannan ta tafi. Wahsegari da safe Jalila ta dawo, bata tashi halima ba daga bacci saboda taga alamar tagaji sosai jiya, ta dama kunun gyada, ta dibi nata a dan karamin flask ta tafi dashi.
Jalila tayi busy sosai a kitchen, dan bata samu ko karyawa tayi ba, dogon wandone a jikinta da rigarta har gwiwa me dogon hannu, ta daure kanta da dankwali, amma karshen gashin ta yafito, taji alamun ana kallonta, bata waigaba ta basar tacigaba da abunda take, cikin kitchen din ya karaso ba sallama ba komai yakama dube2, bata kulashiba tacigaba da aikinta ya jijjiga tea flask bakomai a ciki, tsaki yayi ya bude fridge yana kallon arrangement din datayiwa fruits din, still ya rufe fridge din, Jalila ta fuskanci yunwa yakeji, ta kalleshi “wai meyene?” “bansaniba”
“karka sani din” yaje ya duba kettle yaga akwai ruwan zafi a ciki, ya dakko ya zuba bako lipton, ya dakko madara da sugar yana kokarin antayawa, ita Jalila ma dariya yabata, ta dakko flask ta zuba masa kunun gyada a cup, ta zubamasa samosa, ta mika masa, bako kunya ya karbe, yanemi guri kan kujera a kitchen din yai zamansa yafara ci, itakuma tacigaba da aikinta, wayarta tafara ringing, sunan sweet hanny shine akan screen din wayar, tadaga wayar tasa a kunnenta “Hello sisyna ya kike” hanan tace “Hmm ba fada meyakawo gaba Baby, kin yadani, kin manta dani ko?” “A’a hanan ban manta dake ba, ko zan manta komai bazan manta da yar uwata ba”
“Anya kuwa Jalila? Kina guduna saboda inason Jawwad ko? Karki damu hakan baze shafi zumuncinmu ba, amma yakamata kikawomin ziyara, in duni6da gaskiya bekamata ace tunda kikabar kaduna baki kuma zuwa ba”
Kwalla ce ta taru a idon Jalila, cikin muryar kuka Jalila tace “Hanan bazan iya zuwa kaduna, bazan iya zuwa anguwarmu ba, Hanan hakan ze tayarmin da hankali, inzo unguwarmu ummi bata nan, bansan inda take ba, kiyi hakuri Hanan, amma kina raina daks da sauran mutane masu mahimmanci danake dasu a garin” takarasa maganar hawaye nabin idonta, “Jalila na fuskanci abunda yake damunki, inajin damuwarki a zuciyata, kiyi hakuri mucigaba da addu’a kinji, kidena kuka” gyada kai Jalila tayi kaman tana gaban Hanan, sannan tace “Nagode Hanan, kigaida kowa da kowa mussaman babana” “zasuji Insha Allah yar baba” ta kashe wayar, duk kokarin da Jalila tayi ta cigaba da aikinta amma takasa, tanata kokarin daurewa ta hadiye kukanta amma takasa hawaye ketabin idanunta, sosai Jalal yaji tausayinta ya kamashi, yaji inama ace shima zeji wannan kaunar da shaukin da y’aya sukeji game da iyayensu mata, har fuskar Jalila tayi ja. Tasowa yayi yazo bayanta ya tsaya yana kallon ta, dagowa tayi ta kalleshi suka hada ido, “Meyasa bazaki karbi kaddara a duk yadda tazo miki ba, memakon kiyi addu’a amma kike kuka, hakan bekamata ba, kizama jaruma mana” dauke kai tayi takuma fashewa da kuka wannaan karon hada sheshsheka, sunkuyowa yayi daf da ita a hankali yace, “Ummi tana raye, kuma zaki ganta very soon, jikina yana bani” da sauri ta kalleshi ya jinjina mata kai, yai mata alama tasa hannu ta goge hawayenta, “da mutum yana da ikon sauya kaddararsa, kokuma kuka yana canza wani abu, da mutane dayawa sun fita daga matsalolin dasuke ciki, wani lokacin mukanyi kuka ne don samun sassauci a cikin damuwar da take damunmu, amma ta wata fuskar kukan yana karamana matsala ne da damuwa, ummi tayi rayuwa me tsayi ba tareda yan uwanta ba, kuma hakan besa wani abu yafaru da itaba, dan haka kema addu’a zakiyi kicigaba da hakuri ” yana gama fadin hakan ya mike ya kai hannu ya juye sauran kunun gyadan nan ya juya ya fice, Jalila tabi bayansa da kallo, tai ajiyar zuciya tacigaba da aikinta jikinta a sanyaye.
Wajen karfe shadaya na rana mummy ta shigo tanayiwa Jalila sannu da aiki, Jalila tace yawwa” Mummy barka da safiya”
“Yawwa barka ya aikin?” “lafiya kalau Mummy nakusa kammalawa ma” “to masha Allah” Bayan Mummy tafita ba dadewa Jalila taje gida ta dakko wasu spices ta dawo, ta windowa kitchen dake harabar gidan taga Ilham tana zukar wani abu a kwalba da syringe tana tsirawa ruwan a jikin wani jan Apple, Jalila ta tsaya tana kallonta, tana gamawa ta maida shi cikin fridge ta rufe ta fita ba tareda ta lura Jalila ta ganta ba. Se wajen karfen daya Jalila ta karasa girkin Abincin tareda taimakon Nana data biyota daga baya. Sun kammala komai sun gyara kitchen din kaman ba’ayi amfani dashi ba, suka fito itada Nana, daddy yana palour “Sannu da aiki yaran kirki, nasaku wahala ko?” Jalila tai murmushi “ba wani wahala daddy mun kammala komai ma” “Masha Allah, Allah yayi Albarka” Nana tace “Ameen daddy, amma ni gaskiya nagaji” “Aidama ke lazy ce Nana” sukayi dariya, daddy yace “Jalila amma in sunzo aizakizo kiga yan uwan yayanki ko?” murmushi tayi ta jinjina kai, daga nan suka fita suka tafi gida. Jalila ta gaji dan haka wanka tayi, Naja tana kan gadon ta baje, Jalila ta haye gadon ta kwanta itama, Naja ta kalli Jalila “malama meye haka? Bakiga nice a kwance agurin ba” “Eh banganiba, babu a house ko?”
A fusace Naja tace “amma kinsan karyane kicemin babau a house ko” “in akwai a house ai dabakiyi wannan shirmen ba, kodayake aiba mamaki a sha rashin hankalin nono” “kut me kike nufi?”
“inkika bari, nakuma bude baki da nufin mayar miki da martani sekinyi kuka, dan haka kiyi abunda ya dameki bacci zanyi” Jalila ta kwanta abunta, tabar Naja tana kallonta, can cikin bacci Jalila taji Nana tana cewa “Ke Jalila ki tashi, bakinku sunzo fa?” A hankali Jalila ta bude ido “wane bakin kuma?”
“Bakinsu Jalal mana, ki tashi yau zakiga yan uwansu, masu irin hancinsa”
Jalila takuma juyawa akan gadon tace “ni dan Allah ki kyaleni mana” “Ke Jalila kinada matsala wallahi, dan Allah ki tashi muje, akwai wanda nakeson gani a cikinsu, inajin kunya inje ni kadai” Jalila ta bude ido ta kalli Nana, “ikon Allah, Nana kinda damuwa, wallahi nikam ki kyaleni”
Nana tace “kar Allah yasa kije” “eh bazaniba” har Jalila tafara bacci, ta tuno Apple din nan, kartaje Ilham takuma zuba wani abu, zumbur ta mike, ta bude drower tasaka kayanta, tafito da sauri ta tafi gidansu Jalal, harabar gidan duk motoci, tundaga varrender take jiyo hayaniyar mutane, ta bude kofar palour a hankali, dayawansu kamansu daya da Daddy Jalal, duk haka suke da dogon hanci sosai aranta tace “tab wannan ko bata sukayi da wannan hancin nasu za’a ganesu” se yare sukeyi, ga Jawwad ma a cikinsu, shima se yaren ake dashi, tanaji daya yana tsokanar Nana, da wata irin hausarsa yace “gaskiya Nana kin girma kin ganki kuwa, waike yan mata tunoki nake lokacin kina dan karamarki” Nana ta dan zumbura baki “kajika Kaima ai da bahaka kake ba, ji yadda ka wani tara gemu, waikai dole ka girma” dariya sukayi gaba daya, daddy yai murmushi yace “Nana yaushe zaki dena surutu ne, bakinki baya mutuwa” kallo daya zakayiwa Jalal kasan yana cikin farinciki, fara’a yake sosai, ‘yan uwansa duk nutsatstsu, amma shi yafita daban a cikinsu dan gashin kansa ba kyan gani, ga kallo daya zakayi masa kasan lips dinsa yana shaye2, setaji hakan ba dadi, a hankali ta sulale ta shiga kitchen ba wanda ya ganta, Tana tsaye a kitchen din Ilham ta shigo taci kwalliya sosai, gashi tasa wani turare me karfi, wanda sam bashida dadi, wani banzan kallo taiwa Jalila sama da kasa a wulakance, “Aikin banza jaraba da maita, tunda kingama abunda akasaki aisekikoma inda kika fito ko, ko yanzunma wani munafuncin zakiyi, shine kika dawo”
“Aini bana munafunci kaina tsaye nake abunda nakeso, Aikinne ban gama ba, nazo nakarasa wanda aikin da nakarasa yafi kowanne mahimmanci, na bata aikin wasu dan gyara nawa, kamar yadda nasha fada muddin aikin wani yashigo nawa, sena bata shi” kallon Jalila tayi cike da mamaki wannan karon kuma me take nufine, kwafa Ilham tayi tawuce ta fara daukar kayan Abinci tana fita dasu, alhalin lokacin da Jalila take aikinta ko dauraye spoon Ilham bata tayata ba, Jalila ta tsaya tana kallonta tagama fita da kayam Abincin, ta dawo ta bude fridge tafara jera fruit a tray, tana kallon Ilham ta dakko Apple din nan tai masa guri na musamman akan tray din, tayi waje, Jalila tabiyo bayanta ta tsaya a window tana kallonsu, Ilham sewani iyayi take tana kwarkwasa, Jalila tayi mamaki da bataga Mummy ta fito ba, bakin su biyar ne maza hudu se mata uku, duk daka gansu kasan yan uwan daddy ne,
Ilham cikin iyayi tace
“bari kufara da fruits kafin kuci Abincin ko” cikin bakin daya shima me matukar kama da Jalal yace “Eh hakane gaskiyanki Ilham” tafara binsu daya bayan daya tana basu Apple, Jalila tana kallonta ta dauki Apple din nan ta mikawa Jalal, ya mika hannu ya karba shima kamar kowa dayake Apple yana daga cikin favorite fruit din Jalal. Jalila tana ganin irin kallon da Ilham kewa Jalal, Ilham na ganin Jalal yaci Apple din nan tafara murmushi. dawowa Ilham tayi da tray din ta ajiye a kitchen, har zata fita Jalila tace “bar murna karenki yakama zaki kinyi mantuwa” waigowa Ilham tayi tana kallonta, kawai taga Jalila tana jefa Apple sama tana cafewa
“Ilham kinsaba lamba, saboda na canza Apple din” a razane ta kalli Jalila, Jalila ta karaso gaban Ilham, ta kamo hannunta ta doramata Apple din, duba da kyau wannan shine Apple din dakika zubawa magani ba wanda yaci ba, ko baki gayamin ba nasan abunda kika zubawa Apple din nan na asiri ne akan Jalal, Ilham shi so ba’asiyan sa kuma sihiri be isa yabaki soyayya ba koya soki na lokaci kadanne, in abun ya barshi shikenan, yanzu meye ribarki a cikin cutar da dan uwanki? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button