ABDUL JALAL PART 2

Suka amsa da Ameen
Suka bi doctor Salis office ɗinsa ya tambayi Jalila me yake damun ta tace “ni lafiya ta ƙalau, wannaan gobar da nake ci ce baya so”
Jalal yaiwa doctor Salis bayanin abunda take yi ya rubuta musu tests, yace suje lab ayi, da safe suzo su kawo masa result ɗin.
A daren aka fito da Mummy, likita yai musu bayanin cewar hawan jini ke damun ta kuma ya fara taɓa mata zuciya dan haka tana buƙatar kulawa, ba ƙaramin damuwa Jalila ta shiga daa jin hakan ba, a daren Jalal ya maida Jalila gida yace bazata kwana a Asibiti ba bata da cikakkiyar lafiya.
Da safe Jalila tayi girki ta taho Asibiti bata jira Jalal yazo ɗaukar ta ba, da ta je ɗakin Mummy ba kowa a ɗakin, Mummy na kashingiɗe tana tunani, Jalila ta shigo da sallama tana gaida Mummy Amma Mummy tayi mata banza, Jalila ta zuba mata Abinci ta zauna a kusa da ita tace
“Mummy ki daure kici Abinci seki sha magani”
make plate ɗin Mummy tayi tace “ke wace irin mayya ce bazan ci ba, kina so ki ƙarasa ni kiji daɗin mallake min ɗa ko? To baki isa ba ki tashi ki bani guri”
Jalila ta girgiza kai tace “Mummy wallahi ni bawani abu da nakeyi dan in mallaki Jalal, ina ƙoƙarine kawai inga ya gyara rayuwarsa, Amma wallahi ni ba wani abu da nake yi in mallake miki ɗa” Jalila na cikin maganar ne Jalal ya shigo ɗakin yana murna gaba ɗaya ya manta da Mummy a gurin yace
“sweet heart yanzu naje gida ba kya nan, congratulations you are soon to be a mother”
Kallon shi tayi da mamaki “mother kuma”
“yes matar so you are 3 months pregnant”
Mummy ji tayi kaman ta mari Jalal taji tamkar ya soka mata mashi a ƙirjin ta.
Asalam Alaikum warahmatullah ‘yan uwa da masoya masu nunamin ƙauna ina godiya, masu bina private in tura musu daga farko ina sakawa a watpad masu neman part2 kumin afuwa ku dinga tambaya a group abubuwa sunmin yawa nagode sosai da kawar ku Allah ya bar zumunci
Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????
ABDUL JALAL
Story, writing and edited
By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)
PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????
(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
PART 2
_PAGE 6️⃣2️⃣116
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724
_MY FIRST NOVEL _
Jalila ji tayi kaman tayi tsuntsuwa ta gudu dan kunya, sam Jalal ko a jikinsa ya ci gaba da magana
“Jalila na rasa me zanyi dan farinciki, ɗazu na karɓo result ɗin na kaiwa doctor Salis yace muje office ɗinsa nida ke”
Jalila zata yi magana ya janyo hannun ta sukayi waje.
Mummy ji tayi tamkar zuciyar ta tsage, a gaban ta ɗan ta yake rawar ƙafa akan wata mace alhalin ita baya wannan rawar ƙafar akan ta.
Office ɗin doctor Salis sukaje, yana ganin su ya faɗaɗa murmushin sa, suka samu guri suka zauna, doctor Salis ta dube su yace
“Congratulations once again Mr and Mrs Jalal, you are expecting your baby in the next six months Insha Allah, a scanning ɗinki cikin ki ya shiga wata na huɗu, ya akayi ke ba kiyi noticing kina ɗauke da juna biyu ba?”
Ɗaga kai tayi ta kalli Jalal ta sunkuyar da kai. Jalal yai murmushi yace
“ya zaki kalleni? Ki bada amsa mana”
Shiru tayi ba tace komai ba, nan doctor Salis yaita counseling ɗinsu, tare da basu shawarwari kuma ya jadaddawa Jalal cewar se yayi haƙuri da wasu halaye da ze ga tanayi wanda ba tayi masa a baya, yanayin ciki ne zesata yin hakan.
Sun kai kusan minti talatin a gurin doctor Salis, sannan ya rubuta mata magungunan da zatayi amfani dasu kafin ta fara zuwa awo.
Suka baro office ɗin doctor Salis sam bakin Jalal ya kasa rufuwa saboda farinciki, ɗakin da Mummy take kwance suka koma.
Jalila tace “ko zaka bawa Mummy Abinci da kanka na bata Abincin ta ƙi ci”
Jalal yace “kinga ki ƙyale ta nima idan na bata baci zata yi ba haushi na take ji, tun ɗazu nake fama taƙi ci munyi waya da Daddy jiya anyi sa’a yana Maiduguri yace yau zezo”
Jalila tace “A’a yakamata ka gwada mata ko yaya ta samu taci”
“Ke wai ina ruwan ki dani ne? Dole ne bazanci Abincin ba cikin ki ko nawa? Kinibabbiya kawai”
Tsawar Da Mummy tayi seda Jalila ta ɗan tsorata, Jalal yace “Wannan yana daga cikin abunda yasa bana zuwa gurin ki, yanzu me tayi miki dan kawai tace kici Abinci? Haba Mummy zuwa yanzu yakamata ace kindena irin wannan abubuwan da kike yi”
“ka rufamin baki tun banci mutuncin ka ba, naji duk abunda ka aikata, uwar matarka ta fini tunda har ka iya ɗaukar ta aka fita da ita tai jinyar shekara biyar, ka sa uban ka ya maida tsohuwar matarsa saboda tana ƙaunar matar ka, yanzu ba ko kunya kazo gaba na kake faɗar matar ka tana da ciki, ka je kayi duk abunda kaga dama Jalal, indai kaine na sallamawa mace kai, kaje ta maida kai cikin ta tsabar ƙauna”
Murmushi Jalal yayi yace “Mummy Allah yana son bayinsa masu godiya, idan yayi maka ni’ima ka gode masa seya ƙara maka, karki manta a baya ko kwatankwacin haka baki samu ba daga gare ni, kowa harkokin sa yake yi ba ruwa na dake, na rasa dalilin da yasa har yanzu baki ɗau darasin rayuwa ba, yanzu kome zan miki baki da taka maimai dalilin da yasa kike ƙina da Jalila, matar da kika so in Aura a baya Ilham kin gani da idonki abunda suka yi min, so sukayi su kassara rayuwa ta saboda ke, kin taɓa tunanin meyasa nake gudun ki nake kyautatawa wasu? Idan duniya da gaskiya ya kamata ki tuna Ummi ta riƙeni ta maida ni ɗa lokacin da kika ajiyeni kika tafi neman duniya, ko kin manta waye Jalal ɗin naki,? kin Manta halina ne a baya? Ba wanda zeso ya raɓeni saboda mugun halin Shaye2 da rashin girmama ɗan adam, Rayuwa ta fa ta rushene saboda ke Mummy, Abaya bama shiri da Jalila amma kin taɓa tunanin wani dalili ne yasa na ɗaukaki soyayyar mata ta da mahimmanci? Me yasa baki tsani Jawwad haka ba se Mata ta?”
Jalila tace
“ka tausasa harshe Zaujee Mummy ce”
Ɗagawa Jalila hannu yayi alamar tayi masa shiru ya ci gaba da magana
“A baya in ba mutum ya sanni ba ko yaji sunana ba se a ɗauka Arne ni saboda yanayin saka suturata ma sam beyi kama da na musulmi ba, Yanzu kalleni Mummy Allah ya shiryeni, da kinsan gudunmuwar da Jalila ta bawa rayuwa ta da koda wasa bazaki mummunar magana akan ta ba, a gabanki akace sanadin ta Asirin jikina ya karye, Mummy ko a lokacin da aka ɗaura mana Aure da Jalila ina shaye2 ban fasa ba, Amma ba wanda ta kaiwa ƙara ta, tayi aiki ba dare ba rana dan ganin na shiryu, ni wani irin butulu ne da ba zan nunawa duniya ina sonta ba, Mummy haifa ta fa kawai ki kayi, Tarbiyya ta da sauran Al’amurana mahaifina da duniya ce sukayimin, wallahi Mummy idan baki dena butulci ba abunda ya faru da Umman Ilham kema ze faru dake”