ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

“Sosai makuwa gurin yayi matukar kyau kuma da kikazo seyakara haskawa kyansa ya kara fitowa”
Murmushi ta kuma yi
“That’s good”
Tafada tana kallonsa
“Akwai gurare masu kyau a garin nan gurare masu saka nishadi, Wanda nasan babu su a garinku”
Tafada tana Dan kashe masa Ido
“Kinsan garin namune kika fadi haka”
“No ba kayi kama da yan garin nan ba shiyasa nasan ba Dan garin nan bane kuma bana tunanin kanajin yarenmu”
Shikam abiola gefe yakoma ya nutsu kaman bashiba
“Hmm to garinmu yafi naku kyau”
“Wane gari kenan?”
Ta tambaya
“Se dai ki canka”
Ta Dan kalleshi
“Kana kama da hausawa”
“Yes ni bahaushene”
Jikinta ne ya danyi sanyi ta dan tafi tunani
“Akwai matsalane?”
Girgiza kai tayi
“A’a babu”
“Bari in tafi kar mamana tai min fada na Dade”
Ta juya tafara tafiya
“To ai baki gayamin sunanki ba”
“Marry”
Tabashi amsa a takaice
“Maryam, a nice name”
“Ki ban lambarki mu dinga gaisawa mana kinga semuje ki nunamin inda yafi garinmu kyau”
Murmushi tayi masa ta bashi lambarta sannan ta tafi
“Abiola naga tunda yarinyar nan tazo kawani kame a gefe ko kasanta ne kokuma akwai matsalane baka gayamin ba?”
MatsalaBabba ma kuwa
Amma a fili se yace
“A’a bawani matsala kawai dai na Baku gurine”
Tun daga nan Aliyu ya jone da marry kullum cikin waya suke in tanaso ta ganshi se tace su hadu a lambu
Yayi² ta nuna masa gidansu amma se tace in mamanta ta ganta da wani zatayi mata fada ne
Sunyi matukar shakuwa soyayya suke sosai mussaman tayi masa girki sufita guraren bude ido
Dukda kasan cewarta kirista bata shigar banza sedai yawo ba dan kwali shima Aliyu ya hanata
In lokacin salla yayi zata jirashi yayi salla koma ta tuna masa, suka shaku matuka amma besan wacece ita ba, tanayin abubuwan dasu kan bashi mamaki, indai zasu hadu ko Suyi waya setayi masa sallama, gashi lokaci zuwa lokaci yakan ji tace masha Allah, subhanallah da maka mantansu
Se yayi zaton kawai saboda yana yawan fada ne itama takeyi
A kwana a tashi gidansu marry aka fuskanci sauyi a tare da ita sakamakon yawan fita datakeyi,
Kuma fitar ma ita kadai dan haka aka tsaurara mata tsaro ta shiga damuwa sosai rashin ganin Aliyu da batayi sedai suyi waya abun ya dameta matuka,
Aliyu yace tabarshi yazo shi Inda take amma tace masa baze yiwu ba,
Wasa² suka shiga matukar damuwa saboda rashin ganin juna
Abiola yake gayawa abinda yake faruwa
Abiola ya tausayawa Aliyu ganin yadda marry ta jashi fage me matukar wahala dakuma hatsari
(Wato soyayya)
Gakuma banbancin addini da kabila ga kuma uwa uba dokar masarautarsu
Aliyu yasaka ranar zuwa kano domin yaga gida don kusan watansa hudu a kogi state haduwarsa da marry ne ya mantar dashi kewar Gida datake damunsa da farko,
Wata rana Suna waya da daddare shida marry yake gayamata yanaso yaje kano domin ganin Gida
Kuka sosai ta kama yi masa ya shiga damuwa
“Haba maryam ya haka zaki tayarmin da hankali kin hanani zuwa inda kike kinki bari mu hadu,
bakisan yadda nakeji ba ne naga kaman baki damu ba ko baki yadda dani bane bansani ba”
“Noo bahaka bane nima ina cikin damuwa an samun tsaro sosai, am sorry Aliyu akwai abunda na boye maka amma inaso mu hadu kafin ka tafi”
“A ina zamu hadu ?”
Yai mata tambayar cike zakuwa
“Inda muka saba haduwa a garden”
“To shikenan kaman karfe Nawa?”
“Da yamma by God will”
“Allah ya kaimu da rai da lafiya”
“I love u Aliyu”
“Love u more my dear”
“Kamin wani Alkawari”
“Wane Alkawari ?”
“Will u marry me?”
“I will me sunan mum insha Allah in dai family dinku zasu yarda dani su bani auren ki, bantaba soyayya ba se akanki, akanki nafara kuma daga kanki nagama insha Allah”
Ajiyar zuciya tayi
“Aliyu ka kwanta karka makara sallar Asuba kaimin addu a lamuran suzo da sauki”
“Kullum inayimana kiyi bacci me dadi zanzo a mafarkinki muje yawo”
Dariya sukayi suka kashe wayar
Kaman yadda tayi masa Alkawari haka tayi kokari seda ta fito daga Gida bawanda yasani
Inda suka saba haduwa yauma anan suka hadu
Se dai sabanin sauran kwanaki dasuka saba haduwa yau fuskarta dauke take damuwa
Kusa dashi ta zauna shiru ya Dan ratsa
Sannan ya kalleta
“Baki da lafiyane?”
Ta girgiza masa kai
“Ya akai kikayi wannan ramar haka meyake damunki, tell me, meyake faruwa”
Idonta taf hawaye ta kalleshi
“In ka tafi yaushe zaka dawo?”
“Bazan Dade ba insha Allah”
“Dagaske kake zaka aureni?”
“Am serious ina sonki son da bantaba zaton zanyiwa wani makamancinsa ba bayan Dan uwana I love u with all my heart”
“Aliyu ina sonka Dan Allah in kagama service ka tafi dani garinku ka aureni musulunta zanyi”
Mamakine yacika Aliyu ba maganar da tayine ya bashi mamaki ba illa magana da tayi da harshen Hausa Wanda be taba zaton ko zo tasani da hausaba
” Noor (sunan da yake kiranta dashi kenan)
Dama kin iya Hausa?”
“Na iya Hausa”
Tabashi amsa
“How comes ban taba ji kinyiba”
Wata nannauyar ajiya zuciya ta sauke
“Mamana kiristace babana kuma musulmi ne kuma ba haushe ne family din babana dukansu musulmai ne kuma musulmi suke aure
Baba nane kadai ya auri kirista wadda ta kasance ya mace tilo a masarautarmu yan uwanta duk mazane dan haka ake matukar sonta a cikin masarautar da ta ISA aure ta dage akan wannan musulmi take so akayi² ta hakura taki Dan haka aka kyaleta ta aureshi
Tunda ta aureshi ya tafi da ita take samun cusgunawa daga dangin mahaifina suka takura mata da kyama da tsangwama a daddafe ta haifeni ta yayeni babanta yece sedai ta dawo Gida a hakura da auren ba za adinga wulakanta masa ya ba a matsayinsa na sarki me fada a aji amma ace ana wulakanta yarsa a gidan aure
Dangin mahaifina suka kwaceni shekarata takwas a hannunsu babana ya rasu a gurin kakata na zauna ita ke koyamin karatun addini shekarata takwas amma na haddace izu ashirin na Qur’ani
Da mamana taji rasuwar mahaifina ta daga hankalinta akan se an batani ,
An kai ruwa rana seda kakana ya hada da karfin mulkinsa sannan aka karbeni daga dangin mahaifina
A gurin kakannina ni musulma ce na iya abubuwa dayawa kuma na tashi da Hausa a bakina dana dawo nan mamana ta maidani addinin ta sannan tayi Alkawari bazata bari inyi gangancin datayi ba, family dinmu ba a auren Wanda ba yarenmu ba ko kuma ba addinin mu ba tun daga kan mamana akasaka wannan dokar”
Tana kaiwa nan ta sauke ajiyar zuciya
“Meyasa tun farko kika boyemin hakan, why”?
Idonta taf da hawaye ta kalleshi
” please Aliyu don’t leave me tun randa kukazo da abiola na ganka naji ina sonka kate makamin Aliyu, in kai haka zaka ceceni daga halaka danakee ciki zan samu damar komawa addnina na musulinci”
“Lallai abiola munafiki ne shine ya kyaleni nake ta fama ko Ashe yasan komai”
“Ni nahana shi yagaya maka Dan Allah Aliyu kar kaarabu dani kayi Alkawari zaka aureni”
Kuka take sosai
“Is OK ai bance miki nafasa ba Dan haka kiyi shiru zansan yadda za ayi zanzo innemi aurenki a gidanku”
Zaro ido tayi tace baze yiwu ba ita dai kawai ya tafi da ita basu saniba
"Idan nayi haka banyiwa iyayenki adalci ba kibari inje kano in dawo zamuyi abinda yakamata"
Haka sukayi sallama kaman bazasu rabu ba
Aliyu ya dawo kano cike da tunanin noor (marry) sunyi farinciki da ganinsa, dayake da weekends ya dawo yaita zuba ido yaga Jawwad amma be Ganshi ba
“Wai INA Dana ne” ya tambayi Usman
“Hmm wallahi wani yaro ya hadu dashi a kusa da makarantarsu, sun likewa juna yaita kuka se an kaishi gurin yaron, shima yaron in aka tashi daga tasu makarantar seyabiyo shi gida direbansa da malaman makarantarsu suyita nemanshi se mun maida shi makarantarsu yayita kuka,
To shine babansa yace Dan Allah da weekends akai Jawwad kokuma shi akawo shi akawo shi nan”