Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
What’s https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin???????????? da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks????????????????
Your comments give me courage

Takabbalallahu minna wa minkum eid el Mubarak alaina wa alaikum 

Allah ya karbi ibadunmu yasamu a Wanda yYafewa a wannan kwanaki goma na dhul hajj

     -my first Novel-

Numfasawa yayi ganin yadda yaran gaba daya suke durkushe a gabansa ga maryam da take ta kuka

Ko ba komai Aliyu yaron kirki ne tun tasowarsa ba taba dakko masa magana ba dukda fadansa da shige shigensa baya dakko magana
Kuma ya duba misalin da inna mairo tai masa Suma yadda sukazo basu San kowa ba malam shehu ya daukesu kaman yayansa Dan haka ya numfasa

“To shikenan na amince Allah ya tabbatar mana da Alkhairi yayi muku albarka gaba daya”
Marry ta dago da sauri

“Baba dagaske ka yadda in auri Aliyu”

Ya gyada mata kai
Da gudu marry ta tafi gurin Inna mairo ta rungume ta

“Mama bani da bakin godiya mama kiyimin godiaya gurin baba, kun gama min komai a rayuwa da kuka karbeni nagode sosai.

” ba komai maryam nima nayi diya dama bani da ya mace”
Inna mairo tayi maganar tana sharewa marry hawaye

Aliyu da Dan uwansa haka suka dinga yiwa mahaifinsu godiya tare da adduo’i
Usman yaji dadin yadda baba ya amince ko ba komai shima Dan uwansa ya samu farin ciki

Bayan malam imam ya koma daki ya kira Aliyu yayi masa nasiha ya ja kunnensa game da rike amana da yi masa gargadin zama jakada nagari na addinin musulinci da kuma kabilar hausawa
Haka marry ta karbi musulinci ta koma maryam Amma aliyu yake kiranta da noorat saboda sunan mahaifiyarsa ne
Abubuwa sunzo mata da sauki saboda tasan addinnin musulinci se Dan abinda ba a rasa ba.
Itakuwa Maman Jawwad tunda taga abunda yafaru gashi kuma mutanen gidan sun karbi maryam.ta fara jin haushi, yadda inna mairo take kula da maryam kamar yarta amma ita dasukayi kusan shekara shida da ita bata wani shiga sabgarta,
Dan haka ta shiga yayatawa a anguwa kanin mijinta Aliyu ze auri kirista dukda tasan ta musulinta, hakanan se yan unguwa su shigo dan aga matar da Aliyu ze aura.

Duk surutun da ake a gari Aliyu da yan gidansu suka toshe kunnensu, dama ba a tunkarar Aliyu da maganar Dan ansan masifaffe ne
Sedai ayiwa Usman ko magulmata in sun shigo suyiwa inna mairo
Aka ware musu bangarensu a cikin gidan, dukda kasancewar maryam kabila kuma wadda tayi girma a gidan sarauta amma tana da matukar biyayya da girmama manya ba ruwanta da hayaniya, mamansu Aliyu ana kiranta inna mairo amma ita se dai tace mata mama

Malam ya tsaida ranar daurin auren maryam da Aliyu sati biyu
Usman shi ya hadawa Aliyu lefen da aka bawa maryam itakuma tace ai tana da kayan sawa
Inna mairo tace mata wannan itace Al’adarmu ana hadawa mace kayan lafe abata

A lokaci kankani mutan gidan nan suka saki jiki da maryam ta shiga ransu saboda tsabar nutsuwa da biyayya gashi kullum tana tare da Jawwad yaron yana sonta wataran hada JALAL in an kawo shi,
amma banda Zainab wadda ba ruwanta da ita
yan gidansu Zainab musamman sukazo don ganin maryam suka dinga Yar mata da bakaken magana yayarta wadda suke cewa Yaya mairo ta dinga ziga Zainab,
“Ba ruwanki da ita kuma karki kara yadda danki yaje inda take don arna mugayen kazamai ne gasu da asiri na bala’i dan haka ki rike kanki karki bari a mayar miki d’a da irinta dan wannan tuban nata be kai zuci ba mumafuka CE yaudararku kawai takeyi”
Haka sukayi ta zigata sannan da yamma suka fito zasu tafi suka tarar maryam tana wanke² a tsakar Gida

Se Yaya mairo ta waigo ta kalli Zainab
“wai ya sunan ta ne”
Ta tabe baki
“Wai maryam” Zainab ta fada a wilakance

“Kutt dan wulakanci sunana aka samata”
Itakam maryam tana ganinsu ta fara murmushi
“Sister zaki tafi ki gaida gida Allah ya kiyaye hanya mungode”
Tai maganar tana dan durkusawa
“Au dama ta iya hausa, tab wai Allah ya kiyaye Ashe tasan Allah”
Yaya mairo tafada tana wani kebe baki
Da maryam ta fuskanci wulakanci zasuyi mata seta cigaba da aikinta
“Tab an baro iyaye an fake da za a musulinta an ta ho bariki,
Allah dai ya kiyayemun kanwata”
Ido taf hawaye maryam ta dago tana kallonsu
“Meye kuma na kura mana ido to indai kurwarmu ce kwalelenki dangin maita, banda jaraba wannan kanin mijin naki yarasa wadda ze aura se tubabbiya tir”
“Nawa ubanki yabani gudunmuwar auren da zanyi?”
Sukaji yo muryar Aliyu dama shi ba sabgar matar wansa yake shiga ba saboda ya fuskanci bata da mutunci ita da yan gidansu
“Zainab bari in gaya miki wani abu guda daya tunda iyayena suka karbi maryam banga matar da ta isa tazo tana zaganmin mata ba muddin kika kuma kuskuren zaginta zan baki mamaki munafukan banza kawai marasa tarbiyya”
“Noorat aje wanke² kikoma daki rabu da su jahilai kawai”

Lokaci² maryam kanyi kuka inta tuna da iyayenta tana kewarsu

Yayinda ya kasance bangaren iyayen maryam ma haka mamanta kullum setayi kukan bakin cikin rabuwa da yarta kullum cikin tunanin Allah yasa kar yarta ta fuskanci kalubalen da ta fuskanta a gurin al ummar hausawa ubangiji yasa tana hannu nagari.

Ranar wata juma’a bayan sallar juma’a aka daura auren Aliyu da kuma maryam
Malam imam shi yayiwa maryam kayan daki yayinda Usman shi yabiya kudin sadakin maryam
Suma aka basu guri a cikin gidan ranar maryam bakinta kasa rufuwa yayi ji take kaman mafarki waita mallaki Aliyunta
Haka rayuwa tacigaba da gudana yayinda maryam ke fuskantar wulakanci daban² daga bangaren Zainab, danginta, kawayenta da kuma sauran yan unguwa
Ko ruwa maryam ta sha da Kofi Zainab bazata kara taba kofin ba datayi abu zata fara cemata tubabbiya ta baro danginta ta taho yawon ta zubar indai Jawwad yaje inda take har dukansa takeyi amma kullum shida Jalal suna manne da maryam
Maryam bata taba kulata ba, ita soyayyar da Aliyu da iyayensa suke mata yafiye mata komai dayake Allah besa ta samu haihuwa da wuri ba
Aliyu ya maida ita makaranta takuma yin waec bata samu admission ba dan haka se ta shiga poly ta karanta catering
Rashin haihuwar da batayiba ya dameta matuka Aliyu ke kwantar mata da hankali, yana cemata gasu da Jawwad ga Jalal suma yayan sine
yayinda Zainab take cewa tunda an saba zubar da ciki sannan akai aure ya za ayi yanzu asamu haihuwa tunda angama barar da kwayayen a titi sannan aka tsallako aka taho wai an tuba,
Itakam maryam bata tanka mata, se dai in Aliyu yaji yazo ya kare mata tas,
malam imam ya sha Jan kunnen Zainab akan wannan abubuwan data ke wa maryam amma bata fasa ba dan ba kunyace da ita ba.
Katsam maryam tasamu ciki ta fara laulayi tayi farinciki sosai da wannan cikin dukda kasancewar cikin na wahalda ita Aliyu shiyake mata komai har cikinta ya fara girma sannan tasamu sassauci
Amma bangaren cin mutinci daga yan uwan Zainab da sauran yan unguwa se abinda yayi gaba yayinda
Zainab ta dinga cewa watakila ma cikin bana Aliyu bane cin zarafi daban²
Babban bakin cikin Zainab maryam bata kulata kome zatayi

Wata tara cif Allah y sauki maryam lafiya ta haifi ya mace me matukar kyau kamanta daya da Yaya mairo kalar Fulani sosai

Tunda aka haifi yarinyar nan JAWWAD da JALAL suka zama yan raino JALAL baya tafiya Gida kullum yana manne da jaririyar nan,
JALAL Ya dinga bin Aliyu yana cewa Abee (yanda JAWWAD take kiransa) yana cewa dan Allah Asama jaririyar JALAL dariya Aliyu ya dinga yi yana cewa JALAL kataba ganin ansawa mece sunan maza
Shidai ya dage asawa babyn sunansa
“Kar ka damu yarona ko dan kaunar da kakewa dana Jawwad zanyima yanda kakeso”
Ranar suna ta zagayo akasawa jaririya suna Jalila
Watan Jalila 3 Zainab ta haihu itama ta haifi ya mace lokacin Jawwad yana da shekaru Tara
Ranar suna akasama yarinya Nana Fiddausi sunan Jakarta
Nana da JALILA suka tashi kamar yan biyu
Jalila ba abinda ta bari bangaren halin mahaifinta na fada da Neman magana in tafita bata da aiki se Neman magana da cin zalin yayan mutane, sukuma iyayensu su kamata su daka tare da yimata gorin Yar tubabbiya jikar arena
Abin yana bakantawa maryam da shikansa Aliyu maryam ta dauki son duniya ta dorawa Jalila in dai aka taba Jalila ji take har cikin zuciyarta amma se ta kauda kai,
A cikin Gida ma Maman jawwad yimata take ko Yaya Jalila ta kwace Abu a hannun Nana, in dai Nana tayi kuka Zainab ta dinga zage² kenan tana cin mutuncin maryam
Wata rana hakan ya kuma kasancewa inna mairo bata nan, Jalila tasaka Nana kuka Zainab kuwa ta wankawa Jalila mari sekace sa’arta, Jalila seda ta fadi tana kuka, sannan Zainab ta dinga zaginta tana cemata Yar gaba da al fatiha jikar arna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button