Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Daga office dinsa ya dinga jiyo hayaniyar Jalila ta dawo daga ajin dake gaban office dinsa
Tsaki ya ja ya kalli dayan malamin
“Aifa bismillahi wannan baki abun maganar ta dawo yanzu bamu da sakat saboda surutun dalibai”
Daya malamin ne ya kalleshi
“Lallai kam malam naziru indai Jalilace baki abun magana, ga surutu ga Neman magana, inda take birgeni kwakwalwarta tana Ja sosai, kuma duk tsiwarta intai laifi akwai bada hakuri”

“Hmm kaidai bari kawai idan nafara lissafo maka halin yarinyar nan ai se dai addu’a”
Murmushi daya malamin yayi sukayi musabiha ya bar office din
Mamakine ya cika shi kodai kunnensa beji dai² ba yaji ana Jalila ta dawo amma yaji ajin shiru kaman an cinyesu se Dan surutu da suke kasa²
Har yayi gaba ya dawo ya leka Ajin aikuwa itance amma fuskarta Sam ba walwala ta koma gefe tayi shiru se Siyama dake gefenta tana mata magana
Kai tsaye ya dawo kofa ya shiga ajin gaba daya suka nutsu
“Baku San me yakawoku nan bane Ku dakko Qur’anin Ku kufara tilawa,”
Ya kai dubansa kan Jalila
“Ke yau kwananki kusan goma bakizo makaranta ba, kuma baki bada wani uzuri ba”
Siyama tai saurin cewa
“Malam Naziru nafa gaya maka..”
“Ke rufemin baki marasa da’a ina magana zaki katseni”

Ya maida dubansa ga Jalila
“in anjima zanzo karbar hadda duk na kwanna Goman nan sekin bani haddasu
Kukama Ku dakko Qur’anin Ku nace”
Kowacce kokarin dakko Qur’anin Sa yake banda Jalila wadda kamar an dasata
“Ke ina naki Al Qur’anin”?
Ya dakamata tsawa
Qur’anin hannun Siyama ta nuna masa
Ya kalli siyama ” ke ina naki?”
Itama Qur’anin ta nuna masa “rainamin hankali zakuyi kenan?”

Fita yayi be dade ba se gashi da wata katuwar dorina yana zuwa ya fara takan Siyama ya zaneta sannan ya nufo inda Jalila take
Zumbur ta mike ta fara ja da baya
“Dawo nan ki tsaya, fara bani haddar yanzu zan karba”
Yafada yana muzurai yana nuna mata gabansa
“Ni wallahi banyi haddan nan ba kuma in kada keni da wannan bulalan suma zanyi”
“Ai ko mutuwa zakiyi yau sena zaneki Dan kun rainamin hankali wai Qur’anin Ku daya Ku biyu”
Aikuwa Jalila ta dage ta kwala ihu tare da fadin
“Malam babba kazo ka temakeni, danka ze kasheni, za a daki amanarka Dan Allah kazo”

Daga ajin da dattijon yake zaune yana biyawa dalibai karatu ya jiyo ihunta tana kiran sunansa
Malam babba shine mamallakin makarantar malam, Naziru kuma dansa ne dabasa jituwa da Jalila
Wataran ya daketa tayi suman karya, aka kaita Gida lokacin Abban su Jawwad yazo, hankalinsa ya tashi sosai yazo har makarantar ya samu malam babba akan dukan da akayiwa Jalila yayi yawa, malam babba yaita bashi hakuri, shine Abban Jawwad “yace malam ga yata nan Amana dan Allah a hannunka marainiya CE adinga hakuri da halinta”
shikuma yace ya karba, indai za a daketa har cikin zuciyarsa yakeji bayason kukanta
Itakuma Allah be hada jininta da malam Naziru ba, kusan kullum Seya nemi abinda zesa ya daketa

Tashi yayi da sauri ya taho ajin dayake jiyo ihunta yaganta ta makale a lungun ajin tanata kuka ga kuma malam Naziru a tsaye da bulala
“Naziru lafiya nakejin kukan ‘yata”
Nan malam Naziru ya shiga gayamasa abunda akayi da Wanda ba ayiba
“To ina nema mata afuwa bana son ana samun ita kuka dukda Yar tawa tafiye Jan magana”

Gyada kai malam Naziru yayi ya fita daga ajin zuciyarsa fal bakin cikin rashin Zane yarinyar nan.
Malam babba ya hada litattafan makaranta yabawa Jalila sannan yace ze aikomata da Jakar makaranta

Itakam siyama har aka tashi daga Islamiyya kukan dukan da akayi mata take Dan tana tsoron bulala, mafi akasari in Jalila tai lefi akanta abun yake karewa.
Da aka tashi Har Gida Jalila ta raka siyama tana ta bata hakuri

Kwana biyu Jalila tacigaba da harkokinta hankalinta kwance amma data tuna mafarkin nan se ta ji jikinta yayi sanyi
Tana kwance a dakinta gidan bakowa tanata tunani bacci ya kwasheta Ummi bata nan ta tafi kasuwa

Jeje ne zaune yana ta busa shisha, shikuma Jalal yasaka Bluetooth a kunnensa ya jingina da kujerar da yake kai
Jeje yadan taba shi alamar yanason zeyi magana da shi cire Bluetooth din kunnensa yayi yana kallon Jeje alamun ina jinka
Jeje yai gyaran murya
“Man wai ya batun tafiyarmu Dubai ne naji ka shiru”

Lumshe ido Jalal yayi
“Tafiya tana nan daddy ya turomin kudi nayi arranging din next week ne insha Allah”

“That’s good my man but a yanmatan nan baka ganin yakamata mu tafi da wasu abun zefi dadi inda mata a harkar”
Hade rai sosai Jalal yayi murya a kaushashe yace

“Amma kasan a tsarina babu mata ko? bana gayyatowa kaina ciwon kai, in kaga bazaka ba seda mata to kawai ka zauna, ba Y’ar Wanda zan dauka in tafi da ita”
Lallai gayen nan, amma a hankali da matan zamu kafa maka tarkon dabaka Isa ka tsallake ba, tarkon daza mu rikeka a wuya jeje yai maganar a zuciyarsa
A fili kuma yace
“As u wish my boss abar maganar mata mutafi kawai”
Jalal bekuma tanka masa ba Yakoma ya jingina da kujerar da yake

“Are u serious Jalal wai damaa dagaske kake tafiya Dubai zakayi, mahaifiyarka fa bata so mahaifinka ma ba a son ransa zaka tafi ba meyasa bazaka hakura ba? Haba Dan uwana kayi tunani mana”
Jawwad ya karasa maganar a sigar rarrashi
“Ina ruwana da rashin yaddata data yadda da karta yadda duk matsalarta ne, daddy kuma tunda ya yadda ya turamin kudin ai ya yadda kenan”

“Haba Jalal duk abunda kayi ba da yadda iyaye ba kosa albarkarsu ba karshen al’amarin lalacewa”
“Indai albarkarta ce banaso ta babana ta isheni”
JALAL yai maganar yana hade rai

A fusace Jawwad ya kalleshi
“JALAL uwa uwace komai lalacewarta balle babu lalacewa a iyaye meyasa kai baka yafiyane? Kamanta mana komai ya wuce hawayenta masifa ne a rayuwarka”

“Idan na tsallake nabar Nigeria seta manta dani kafin na dawo kaga ta huta ta dena hawayen”

“Haba Jalal mahaifiyarka CE fa meyasa kafiye taurin kai ne meyasa baka yafiyaa me”?

“Dole kace haka tunda ba kai kake irin rayuwar danake ba, ba kai ka samu kanka a halin da nake ciki ba, mutane na kyamarka shiyasa kake cewa in manta komai ya wuce,
Idan nabar kasar nan seta ganni zatayi kukan ai lokaci² nazo inga daddy”
“Jalal anya Kasan soyayyar dake tsakanin d’a da uwa kuwa baka tunanin halin daza ta shiga in ka tafi?”
Jawwad ya fada yana kallon Jalal da yake shirya kayansa a trolley
Be dago kai ya kalleshi ba yabashi amsa
“Kai kasanta ita soyayyar d’a da uwar, gobe insha Allah zan bar kasar nan kudena ganina balle ranku ya cigaba da baci akaina”

Jalal ne da Jawwad ke zaune suna hira gwanin sha’awa sunayi suna dariya suna cin yayan itatuwa a wani lambu me matukar kyau da korayen bishiyu
Wani mutum ne ya zagayo ta bayan su Jalal ya rife fuskarsa ba a iya gane waye, yabawa Jalal wani abu, Jalal ya karbi abun yafito da shi ya dubi kirjin Jawwad ya zaro wata siririyar kibiya Yar Karama ya sokawa kirjin Jawwad din saitin zuciyarsa, nan take Jini ya balle, sekuma Jalal ya yadda kibiyar ya rungume Jawwad yana kuka, wannan matar ce ta rannan tazo tafara Jan Jalal,
Nan da nan gurin Yakoma baki bishiyoyin gurin suka bushe,
Ta dinga janshi zuwa wani katon rami ita da wani mutum
Jalal mikowa Jawwad hannu yake
“Dan uwa ka temakeni kar kabari sujani cikin Ramin nan”
Jawwad dafe da Inda Jalal ya sokamasa kibiya jini na zuba yake fadin
Bazan iyaba Dan uwa
Jalila!Jalila!!Jalila!!!
Kitema kawa Jalal karki bari su jashi cikin ramin nan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button