Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Cigaba da shirinsa Jal yayi yasaka kananan kaya wando jeans da T-shirt blue, ya taje sumar kansa ya daura agogo sannan ya dakko bakin glass yasaka
Yayi kyau matuka, duk abin nan da ake Jawwad yana zaune yana kallonsa,
“Dan uwana kazama me min addu’a aduk inda kake kaman yadda kake min abaya Jawwad bazan manta da kai a rayuwata ba”
Jalal yafada jikinsa a sanyaye

“Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni,
Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,
Da second daya bantaba kyamarka ba amma sekai akan wani dalili naka Mara amfani
Zaka tsallake ka barni,
Akan wannan Mara imanin zaka tafi kabar kasarka ta haihuwa iyayenka yan uwanka ka tafi, wannan shine sakamakon abota wannan shine yan uwantakar dake tsakanina da kai
This is what I deserve from you nagode da kauna Jalal”
Jawwad yayi maganar cikin fada

Jalal ya tako gaban Jawwad ya dafa kafadarsa idonsa dauke da kwalla, muryarsa na rawa yafara masa magana

“Am sorry dan uwana baka cancanci haka daga gareni ba but am sorry ba yadda na iya”

Yaja trolley dinsa yayi waje da sauri

“Siyama nifa wallahi gabana faduwa yake ganinake wallahi seya tafi
Bakisan halin Sa da taurin kai ba”
“No kwantar da hankalinki, kome zezo da sauki insha Allah yanzu kira Yaya Jawwad din muji ya ake ciki”
“Anya zan iya magana kuwa bakiji bugun da zuciyata take ba”
“Calm down kirashi kiji”

Layin Yaya Jawwad takuma kira
Sedata kusa tsinkewa sannan ya daga
“Yaya Jawwad ya ake ciki ne yafasa tafiyar kuwa”
“Jalila ya tafi bashi da niyyar fasawa ya tafi yau ze bar kasar nan”
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

Share please
More comments more typing……
Love u all my fans

????️????️????️????️????️

Daga Alkalamin Yar baba
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  16&17

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks????????????????
Your comments give me courage

Aimin afuwa the page is not edited
-my first Novel-

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un shine abinda Jalila ta fada jikinta a sanyaye
A hankali ta sauke wayar daga kunnenta ta kashe wayar
Takalli siyama
“Aminiya ya tafi”
Yasalam shine abinda siyama ta furta

“Kwantar da hankalinki har yanzu da sauran lokaci ai”
“Kwanciyar hankalifa babu shi Aminiya dan bakiji yadda zuciyata take min bane
Bari in tafi Gida uumi tace kar in dade kuma kinga nabata lokaci bari in tafi kawai”
Har gate Siyama ta rakota tana bata kwarin gwiwa, tare da bata shawarar cigaba da addu’oi
Sannan ta mata alkawarin zatazo har gidan taji yadda akayi
Haka Jalila ta tafi Gida jikinta a mace
Yanayin fuskar Ummi ya nuna mata tayi fushi da ita
Dan se basar da ita take Jalila ta rasa meyake mata dadi

Jeje ne a tare da wani mutum a cikin mota me tint glass yasaka wando three quarter da wata Yar Riga Mara hannu suman nan tayi tsage²
Kai daka ganshi ka ga dan iska

“Katabbatar kayi abinda yakamata in kukaje kasan abinda ya dace kayi shima wannan aikin naka akwai kaso me tsoka ka tabattar da aikin nan ya tafi dai² “
Mutumin yayiwa jeje maganar

“Considered it done my boss zan tabbatar da aikin nan ya tabbatat”
Jeje yafada yana dan risinar da kai
“Good”
mutumin yafada cikin Isa
Sannan jeje ya bude kofar motar ya fita ya dauki akwatinsa
Inda sukayi zasu hadu da Jalal yaje ya tsaya ya kirashi a waya yan mintuna kadan sega Jalal ya karaso
Shima
“hmm yau kayi abun arziki ka cika alkawari”
Murmushi Jeje yayi
“ba dole ba my boss ina ciki farin ciki”
“Good yanzu se mu tafi ko”
Gaban Jalal ne yai mummunar faduwa
Meyake damuna ne haka, menake shirin yine”
Jalal yake maganar a zuciyarta

“Yanaga kana tafiya kuma a hankali yanzu ko akwai abunda yake damunka” Jeje ya tambayeshi
Girgiza kai Jalal yayi
Jeje ne yafara mika passport dinsa aka duba aka bashi ya danyi gaba yana jiran a duba na Jalal,
Jiki a sanyaye Jalal ya mika passport dinsa

(Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni,
Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,!!!!!)

Maganganun Jawwad ne suke dawo masa dakuma tsantsar damuwa da hawaye da ya gani kwance a idon Jawwad su yake tunowa se yaji zuciyarsa ta cunkushe bakin ciki ya ziyarci zuciyarsa, gaskiya ba karamin kauna Jawwa yake masa ba in ya tafi beyiwa kansa adalci ba Jawwad wani bangarene me mahimmanci a rayuwarsa ga kuma mahaifinsa, anya inyayi tafiyar nan yayiwa kansa adalci
jikinsa ne yayi matukar yin sanyi, hannu yasa ya karbi passport dinsa ya juya dabaya yafara tafiya
“Jalal ya haka lokaci fa inazaka jene”
Jeje ya tambayeshi
Bebashi amsa ba yacigaba da tafiya da gudu Jeje ya taho ya sha gabansa
“Man wai meyafaru ne ?
Ina zakaje yanzu fa jirginmu ze ta shi”
“Zaka iya tafiya nikam na fasa”
Zaro ido Jeje yayi “why meyasa zaka fasa”
“Saboda haka naga dama nace in zaka ka tafi ni na fasa”
Ya bashi amsa
JALAL yayi maganar a tsawace

Wayarsa ya dakko ya kira Jawwad, amma be daga ba taita ringing
Jawwad yana kallon kiran yaki ya amsa seda takusa katsewa sannan ya daga wayar
“Kazo ka daukeni a airport”
“Kamar ya?”
Jawwad ya tambayeshi
“Ina airport nafasa tafiyar kazo ka daukeni”
“Bazan zo ba dacan ni na kaika”
“Idan bakazoba zan tafi u know I mean what I said”
“Ohh sorry gani nan zuwa”
Wai dagaske ya fasa tafiyar Jawwad ya tambayi kansa da sauri ya mike ya dau mota ya nufi airport

Ummice take lazimi akan dadduma gidan shiru kaman ba me rai a cikinsa
Jalila tana can dakinta tana duniyar tunani
Ummi ce ta dinga kiranta takirata ya kai sau uku sannan taji ta amsa
“Jalila zonan”

“To Ummi gani nan zuwa”
Mikewa tayi ta nufi dakin Ummi taje gabanta ta zauna
“Ummi gani”

“Naganki ai, Jalila wai meyake damunkine kwata² yan kwanakin nan kaman baki da lafiya baki da walwala Sam
Meyake damunkune baki da Wanda zaki gayawa matsalar ki fiye dani baki da aiki se tunani
My dear tell me what’s actually wrong with you bana jin dadin ganinki a haka”
Tausayin ummine yakamata taji kaman ta gayamata gaskiya amma seta fasa
“Ummina babu abunda yake damuna kawai surutan danake da daddare ne da mafarkai bana so”
“Eyyah sorry my dear kinji tunani baze hana faruwar komai ba addu’a zaki dingayi nima inayimiki Komene Allah zemiki maganinsa”
Haknan se Jalila taji hankalinta ya Dan kwanta
Zame jikinta tayi a hankali ta kwanta akan cinyar ummi
Tanata ambaton Allah a zuciyarta domin tasamu zuciyarta ta rage bugun da take

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button