ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ba a dau dogon lokaci ba Jawwad ya karasa airport Jalal ya hango a zaune jeje yanata lallaba shi
“Tir da wannan dan iskan bawan, mtseeww”
Jawwad yafada a hankali
Jalal yana hango Jawwad ya mike
“Dan uwa dagaske ka fasa tafiya”
“Nafasa Jawwad kona tafi bazan samu nutsuwa ba zuciyarta tana Nigeria tare da Dan uwana”
Rungume juna sukayi kaman zasu shige jikin juna
Wani mugun kallo Jeje yayiwa Jawwad
“Wai dagaske fasawar zakayi?”
Jeje ya tambayeshi a fusace
“Jeje nafasa tafiya bazan juri ganin kwalla da bacin rai a idon Jawwad kamar yadda nafada maka kona tafi dubai zuciyata tana Nigeria”
Jawwad ne yaja trolley Jalal yasaka a boot, ya bude masa motar ya shiga
Jeje ne ya zagayo gaban Jawwad yai masa magana kasa²
“Yadda ka bakantamin yau ka rubuta ka ajiye komai Daren dadewa se na bakanta maka fiye da yadda kayimin”
“Allah ya fika”
Shine amsar da Jawwad ya bashi
Ya shiga ya kunna mortar suka tafi Jeje kaman yayi hauka gaba daya shirunsu ya rushe shi beasan meze gayawa boss dinsa ba
Naushi ya kai cikin iska kamar mahaukaci
“Fuck you Jawwad, indai muna raye sena kuntata maka kamar yadda kayimin “
A hankali wani bacci me dadi ya dauke Jalila akan cinyar Ummi se ajiyar zuciya take kaman wadda ta wuni tana kuka
A hankali Ummi ta shafa kanta Allah yayi miki maganin abunda yake damunki baby na
Duk da yamma tayi Ummi bata tashe ta ba ta kyaleta saboda in tayi wannan farkawar cikin dare bata komawa bacci
Se gefin magariba Jalila ta farka tana farkawa da bugun zuciyar nan ta farka
“Ya salam”
ta fada a hankali
“To dagani tunda kin tashi”
“Ummi ki Dan kyaleni mana in gama hutawa ni dama xaki goyani”
Ture kanta Ummi tayi ta mike ta tafi dauro alwala
A hankali taji bugun zuciyarta tana komawa normal
Ringing din wayarta ta jiyo a dakin ta da sauri ta mike ta tafi ta daga wayar lambar siyama CE
“Aminiya ya ake ciki kuwa ?”
“Oho”
“Kaman ya oho ya tafin ne? Kinkuma tambayar Yaya Jawwad?”
“Aminiya mezan tambayeshi ne ?ya rigada yacemin ya tafi se dai kuma addu’a kawai”
” banji dadi ba aminiya
Allah ya kiyaye ya tsare se mucigaba da addu’a amma ina ji a jikina kaman betafi ba”
“Tab wannan uban taurin kan to Allah yasa amma tunda ya furta seya tafi”
“Insha Allah be tafiba gobe in Allah ya kaimu ki shirya da wuri mutafi islamiyya karki jamana dukan makara”
“Insha Allah aminiya”
“Wani irin sha³ ne kai jeje why do you failed this mission, after all u know na Dora burina akan wannan tafiyar dazukuyi meyasa?’
a wannan tafiyar naso dawwamar da bakin ciki a zukatan ahalinsa na har abada”?
Mutumin dazune da ya kai jeje airport a motarsa yake maganar cikin fada
“Am sorry sir amma ba laifina bane wannan abokinnasa ne ya hana shi”
“Wa kenan”
Mutumin ya fada cikin fada
“Wannan mayen nasa Jawwad, saboda shi ya fasa tafiyar”
“Jawwad ko? Yayi kyau zan tabbatar masa da ba a shiga hanyata semun bar masa mummunan tabo a cikin zuciyarsa Wanda har gaban abada baze goge ba, dama shine yakemana karan katsaye a al’amuranmu zamuyi maganinsa”
“Hakan shine mafita ayi maganinsa kawai”
Jeje yayi maganar da sauri
Har cikin Gida Jawwad Yakama hannun Jalal yashiga dashi yan gidan duk suna parlour ILHAM.tana zaune tayi shiru tana tunani
Yayinda mummy keta rusa kuka daddy yana rarrashinta
Jawwad ne yayi sallama gaba daya suka daga kai domin amsa sallamar
Kawai sesuka ga Jawwad tare da Jalal
Jawwad ya janyo hannunsa zuwa cikin palour
“Gashi nan ya fasa tafiyar hankalinku ya kwanta, mummy kukan ya isa gashi ya dawo”
Jawwad ya fada yana kallon mummy
To Alhamdilillah nima ba a son raina ya tafi ba, ba yadda zanyi ne tunda ya dawo se muyiwa Allah godiya
Ita kam Ilham bakinta ne yaki rufuwa
Mummy da gudu ta mike taje ta rungume Jalal tana cigaba da kuka hada sheshsheka
Kunsan d’a da uwa karo na farko bayan lalacewar Jalal da yaji kukanta ba dadi a zuciyarsa
“Kukan ya isa ai tunda gani na dawo
Ki godewa Allah ki godewa Jawwad Bazan iya tafiya in barshi da kewata ba”
Jalal yai maganr yana kallon Jawwad
Mummy kasa magana tayi se daddy da yake kokarin godewa Jawwad
“Haba daddy kar kasa inji kunya mana bakomai “
Nima Jalila ce takara fargar dani abu me mahimmanci Dana kusa mantawa thank you sweetheart Yayi maganar a zuciyarsa
Sannan ya mike yai musu sallama ya tafi Gida
yana zuwa ya dau wayarsa Layin Jalila ya kira domin ya gaya mata Jalal ya fasa tafiyar amma bata dauka ba
ILHAM tana Shiga daki tayi wani tsalle tare da jefa hannunta sama tace yes key tasaka wa kofar dakin ta sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira layin mahaifiyarta
“Hello Mami”
“Na’am ya ake cikine?”
“Albishirinki”
“Goro”
“Yafasa tafiyar nan dazu Jawwad ya kawo shi Gida yafasa”
“Ke dan Allah dagaske koda wasa”
“Wallahi mami ya dawo”
“Kai amma Jawwad din nan ya kyauta, ya saukaka mana aiki”
“Wallahi kuwa mami”
“To yanxu dai ba sanya zamuyi ba, ki kara dagewa Ilham duk randa burinmu ya cika sekin fini amfana”
“Insha Allah mami zan dage”
“Yawwa yarinyar kirki se na jiki”
“To mami ki gaida mutan gidan”
“Yawwa zasuji”
“Jalila kinga gidan Maman annur ta haihu ban samu na shiga naga babynba zo muje,
Muyi mata barka”
“Ummi wai ita barkan nan dole ce tunda dai bata mutu ba da ranta”
“Ohh ni maryam Jalila mutum ya dau ciki wata Tara ya sauke lafiya tsakanin mutuwa da rayuwa ai aje acemasa barka”
“Ummi naje gobe in Allah ya kaimu yanzu bana jin dadin jikina”
“To Allah ya sawwake miki zo ki rufe kofar gidan”
Jalila tabi Ummi ta rufe gidan sannan dawo cikin Gida ta dakko wayarta ta dawo palour ta Missed call din Jawwad ta gani
“Yasalam yaushe Yaya Jawwad ya kirani ban Sani ba”
Kiransa tayi ya katse kiran sannan ya kirata
“Abunda zan gaya miki ya Riga ya wuceki tunda baki daga wayar ba, se yanzu”
Cike da shagwaba Jalila ta fara magana
“Haba yayana na kaina bangani ba ne se yanzu amma tuba nake ranka ya Dade”
Murmushi yayi
“Sisyna ta wa ni kadai”
“Nanan fa?”
“A’a banda ita”
“Sena gaya mata”
Dariya sukayi gaba daya
“Yayana me yasaka farinciki hakane labarta min”
“Kece Jalila”
“Nikuma”
“Eh mana”
“Ya akayi nasaka farincki”
“Saboda kin tunatar dani abu me mahimmanci
Jalal wani abokinsa ne ya zigashi yayi tafiyar nan Wanda ni da Sam banyi tunanin hakan ba kuma nasan da wata manufar ya zigashi, kuma wai tare zasu tafi
Yanzu dai zancen danake miki Jalal yana Gida yafasa tafiyar ya dawo”
Wata nannauyar ajiyar zuciya Jalila tayi
“Alhamdilillah am glad to hear this from you Allah yakara kiyayewa ya shiryeshi”
“Ameen sisyna muna godiya da gudunmuwarki
Allah yasaka da mafificin Alkhairi ya jikan Abeenmu”
“Ameen dan uwan da babu irinsa”
“Ki gaida ummina”
“Zataji insha Allah na gaida maama,”
Sukayi sallamaa Jalila tace Alhamdilillah
Siyama ta kira ta labarta mata sukayi ta murna tare bakin Jalila yaki rufuwa
Bayan Ummi ta dawo ne ta lura da farin cikin da Jalila take sewani walwala take
“Waime ya farune naga kinata wannan farincikin haka baby gayamin mana”
Dariya Jalila tayi
“Hajiya Ummi ba komai kawai tsintar kaina nayi cikin farin ciki Mara misaltuwa”
“To Allah yasa alkhairine”
“Ameen ummina”
Haka Jalila tayi kwanan farin ciki Allah ya temaketa yau batayi mafarkan ba balle a tsorata ta
Lokacin tafiya islamiyya yayi yan matan sun dau guga a cikin dogayen hijjaban makaranta suna tafe suna hira yau fuskar Jalila fes ba wata damuwa Dan haka yau ajinsu suka tabbatar ta dawo banda hira da surutu ba abinda sukeyi ana hirar yaushe gamo wasu na mata tambayar meyasa randa tazo bata walwala kwanakin nan sunyi missing dinta
Hayaniyar ce ta ishi malam Naziru ya fito Dan ya tsawatar musu
Yana zuwa Jalila yayiwa kashedi
“Yau malam baya nan balle ya ceceki wallahi naji surutu a ajin nan babu ruwana ke zan zanewa jikinki”
Befi yan mintuna da tafiya ba Jalila tabasu sabon topic suka barke da hira hada shewa itakuma ta silale ta gudu ta bar ajin ta nufi babban aji
Malam Naxeeru ne yakuma komawa domin casa yan ajin kuma ya kudiri takan Jalila ze fara
Yana zuwa ajin ya nemeta yarasa ya tambayi tana ina sukace basu saniba aikuwa suka sha jibga yayinda uwar gayya ta fece sun daku ragwaye na kuka, yayinda masu karfin hali kena zuci Dan malam Naziru ya iya bulala,