ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar
07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din
????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
I want comments not stickers or just thanks????????????????
Your comments give me courage
-My First Novel-
Not Edited
Jinine ya wanke mata fuska ta fasa kara yarinyar tayi, itako Jalila ko ajikinta, hakan yayi dadi² da isowar class mastern su Jalila hankalinsa ne ya tashi ganin duk saurin da yayi Jalila ta riga tayi aika² be kara tsurewa ba seda ya tabbatar da wadda aka fasawa goshi salati yayi, Hanan Abdurrasheed Yar gidan babban captain din sojan ruwa da aka kawo ranar litinin ita Jalila ta fasawa kai shi kansa ba yadda beyiba ya canzawa Hanan gurin zama saboda yasan me gurin tafi kashi doyi wato queen J, amma hanan yarinyar akwai izza da jin kai, tace ita dole nan gurin takeson zama,
yanzu yasan ba Jalila ba su Kansu makaranta Ta janyo musu
“Jalila mene haka kika aikata, wannan wane irin shirme ne, yaushe ma kika dawo ne bansaniba memakon kizo kigayamin seki dauki doka a hannu kalli haukan da kikayi”
“Niba hauka nayiba daba ta mareni ba inaga da hakan bata faruba”
“Shut up zaki gane kuranki ubanta sojane insuka casaki inaga daga yau kindena Neman magana”
“Wai da anyi magana se afara maganar babanta sojane,
Allah sarki mukuma ‘ya’yan Allah bani marasa gata, wallahi ko Yar gidan rocket ce bata isa ta mareni in kyaleta ba”
Ya fuskanci babu alamar nadama tareda Jalila Dan ko kadan bata tsorata da abinda tayi ba itakuwa Hanan tuni aka tafi da ita school clinic akaimata dressing daga nan Hanan bata saurari kowa ba ta fice daga makarantar duk yadda akayi a dakatar da Hanan amma tayi waje ta tafi gida
Jalila aka kira office din director
Aka dinga mata fada kowa da abunda yake fada a cikin malamai wasu abun kirkinta wasu akasin haka ciki hadda wata malama ta zage ta dinga zagin Jalila matar a bayan layinsu Jalila take, Jalila ta taba fada da Yar malamar, Dan haka dama tanajin haushin Jalila
“Dama wannan yarinyar ba tarbiyyace da ita ba, bata da mutunci Sam dama ina za a samu wata tarbiyya a gurin Yar mace”
Jalila ce ta daga kai da sauri ta kalleta
“A’a madam adinga hakuri Jalila yarinyar kirkice, tana da tarbiyya ita dai matsalarta da students ne ga tarin alkhairanta ga makarantar mu dabazamu manta ba”
Cewar director
“Hmm yallabai baka San yarinyar nan bane uwatta Sam bata son laifinta ita ta sangarta ta lalace, amma yarinya sekace Yar daba, takama Yar mutane ta fitar mata da jini, dama charity begins at home duk abunda yarinya takeyi to haka taga uwatta tanayi”
“Sir kaimata magana kartakuma zaganmin uwa duk zaginta ta tsaya kaina takuma zagina sena rama, uwa ba tafi uwa ba”
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Jalila ta daban ce
Jalila koma class dinku yanzu”
Cewar director ita kuwa Jalila ta mike ta koma ajinsu
“Dan Allah kalli yadda take ikrarin zata zageni yarinyar nan kawai a koreta shine mafita”
Inji malamar dazu
“Korarta ba shine mafita ba yarinya ce me matukar kwazo in muka koreta munyi asara babba”
Cewar wani malami
“Hakane kam wan mahaifinta abokina ne bazan taba korar masa ya ba, kuma duk fitinarta bantaba ganin tayiba se yau yanzu dai mahifiyarta zamu gayyota tazo mu zauna da ita dakuma wakilinta Dan na tabbatar, Yar gidan sojan nan se sunzo makarantar nan”
“Allah yasa suci kaniyarta sumata dukan tsiya”
“Haba madam in “yarkice fa baza kice haka ba ai shi da na kowa ne addu’a yakamata ayi mata Allah ya shirya Allah kalli dai yasan abunda zata zama nan gaba”
Inji director
Hanan ce ta shiga tangamemen palour tana kuka wata babbar mace ce zata yi shekaru arba’in da takwas amma Hutu yasa in ka ganta seka zata batafi shekaru talatin da biyu ba, gefenta kuma ga wani babban mutum shima yana shan tea
“Ke Hanan meke faruwane ne yasameki haka a fuska”
Matar Tai maganar cikin iyayi da isa
Mutuminne ya kalli hanan shima
“Auta meyasami goshinki haka meyafaru?”
Hanan kuma fashewa da kuka tayi ta kwashe abinda yafaru da karya ta fada tace Jalila tamata duka ta dinga gwarata da bango tana zaginta
“Amma auta kin bani kunya kamar ba Yar Dana Haifa a cikina ba ki tsaya wata yarinya tamiki duka hada fasa miki goshi kamata yayi insa bulala in zaneki ai”
“Wannan wace irin magana ce kakeyi haka a dakar min yarinya haka daga shigarta makarantar, wace Yar marasa galihun ce ta isa tayiwa y”ata haka in kyaleta wallahi senaga gatanta a gurin nan senaga uban da ya tsaya mata, se nasa an kulleta daga ita har ubanta”
“No ban yadda ba kinsan ita Hanan din metayi yarinyar tayi mata haka mubi komai a hankali ki bari gobe in Allah ya kaimu da kaina zanje makarantar indai yarinyar ce bata da gaskiya semusan abinda yakamata muyi’
” daddy ance mata baba na soja ne fa amma secewa tayi wai ko Yar gidan bullet ce, Allah yasa Kaine AK47″
Abun ma dariya yabawa baban Hanan
“Lallai yarinyar nan tana da karfin hali”
Itakam Maman Hanan iya wuya ta kulu taso ace baban Hanan ya kyaleta data nunawa yarinyar banbancin civilian da kuma kaki, zata so taga uban daya tsayawa yarinyar nan ko baban Hanan be saniba seta koyawa yarinyar nan darasi seta nuna mata banbancin dake tsakanin yayan farar hula dakuma “ya’yan rainon bullet.
Tun kafin a tashi daga school wannan malar taje gidansu Jalila tagayawa Ummi abunda Jalila tayi bayan haka hadda cewa itama Jalila ta zageta tsaf
Hankalin Ummi yayi matukar tashi da jin abunda Jalila tayi taita bawa malamar hakuri
Ilham ta dawo daga makaranta amma har taje ta dawo bata fuskanci komai ba, kamar yadda Daren jiya batayi bacci ba tunda Jalal ya nuna mata messages din wayarsa da yake tuhumarta akai, hankalinta yaki kwanciya tun jiya take takura kwakwalwarta domin kokarin gano wadda ke turowa Jalal wannan sakon amma takasa tuna komai, a iya saninta ba ya muamala da mata, to ta Yaya? wacece wannan take kokarin rusa nawa shirin ita ta kafa kanta,
Jikinta a sanyaye taje tayi wanka amma takasa cin abinci “ko gurin Nana zanjene ko zata tayani gano wacece ta, tambayi kanta
Kodayake yanzu ta dawo daga makaranta kar in takuramata koma inje tana wayar da wannan sha³ Yar uwatta ta
Da sauri Ilham ta mike JALILA tafada a fili, tabbas JALILA ce itake turomasa wannan sakonin dan babu Wanda yakewa Jalal shishshigi in ba itaba iya sanina Jalal baya kula mata ko a family
Amma indai na kara bincike na tabbatar Jalila ce sena yi maganinta babu wata “ya mace data isa tayi takara dani a soyayyar Jalal, wallahi JALAL nawane ni kadai, duk macen datayi yinkurin yin takara dani senaga bayanta
se yanzu nagane wato duk wannan shishshigin da take masa Ashe sonsa take
To ba ta isaba wallahi
Koda aka tashi daga makaranta Jalila hankalinta kwance ta taho gida tare da kudurcewa a zuciyarta setaje gidan malaman nan data ce mata ‘Yar mace ta mata warning dan bata hakura ba,
Gida ta tafi ta shiga da sallama amma Ummi bata amsa mata ba dan haka kai tsaye dakin Ummi ta nufa
Ummi nakan sallaya ta idar da salla tana lazimi Jalila ta wuceta ta canza kaya zuwa towel taje tai wanka tai salla tasaka uniform din islamiyya amma still Ummi bata kulata ba
“Ummi wai baki ganni bane, yau ko sannu dazuwa bakice minba se fushi kike wai mena mikine?”
Still Ummi batace mata komai ba gaban Ummi taje ta zauna
“Ummi wai meyene”?
Janyota Ummi tayi gabanta ta zuba mata kyawawan maruka guda biyu
” wato Jalila duk kokarin danake akanki inkika fita abinda zuciyarki tagaya miki shi kikeyi,
Kin fasawa Yar mutane goshi, kinzagi malamanki wannan itace tarbiyyar danayi miki ko?
To yanzu zankira Abban Jawwad in aka kashe case din nan gobe in Allah ya kaimu,
Koshi ko Jawwad wani yazo ya daukeki sukoma can kanon dake,
Lokaci yayi dazan koma dangina kema kikoma hannun wan ubanki tunda ba kya tausayina,
“Yar gidan babban captain fa na sojoji Jalila me nake dashi da Zan iya wannan rigimar dakika dakko, kano zaki koma nagaji, gaskiyar mahaifinki kafin yarasu da yace tarbiyyar mace seda tsayayyen namiji bazan iyaba Jalila nagaji”
“Har anzo angaya miki karya da gaskiya kekuma kin yadda ko Ummi to walla…..
” rufemin baki Dan ubanki”
Da sauri Jalila ta kalli Ummi bata taba jin Ummi tayi zagiba
“Akan kujerar zama ko? kikayi wannan aikin ko ubankine ya sassaka kujerar kokuma akai na haifeki dazaki daki Yar mutane akai kujerar banza,
Kuma saboda baki da kirki ki dubi malama ramatu Dan an miki magana ki zageta ko Jalila”
Se yanzu Jalila ta gane malama ramatu CE tazo tagayawa Ummi
“Wallahi Ummi malama ramatu munafuka ce bafa haka..
” Ai bazaki canza ba, hali indai nakine bazaki canza ba agaban nawa ma kuma zagin malamar ki kike ko?
“Wallahi niba malama ta bace yan primary take koyarwa bata taba koyamin uwar komai ba”
“Yayi miki kyau ina fada kina fada”
“A’a Ummi Dan Allah kiyi hakuri karkiyi fushi bazan karaba”
“Aini nagama yanke hukunci Abbanku zan kirawo azo a maidake kano, nima gurin nawa dangin zan koma”
“Ummi wai dagaske kike, dan girman Allah kiyi hakuri nace mikifa bazan karaba ni wallahi bazan koma kano ba”
“Sekuma kiyi ai tunda ni kin rainani gara kikoma gaban Zainab itace daidanki”
“Na shiga uku wallahi Ummi kafata kafarki ko bangon duniya zaki tafi ko a kafa sena biyoki, wallahi bazan kuma ba dan Allah Ummi, wallahi banason zuwa kano”
Banza ummi tayi mata ta dakko wayarta tana kiran Abba yayinda Jalila ke gabanta tanata faman kuka