Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Jawwad ne yakuma dawowa gurin Jalal amma Jalal yayi masa banza yaki kulashi, haka ya hakura ya tafi ya kyaleshi

Bayan an tashi daga makaranta Jalila ta dawo Gida amma ummi bata nan wani bakin ciki Jalila taji ta tsani ta dawo Gida taga ummi bata nan
Waya ta dakko ta kira ummi
“Ummi ina kika tafi ne?”
“Kinganmu a asibiti Hawwa muka kawo ta haihu Dan ba rai yanzuma Karin jini ake mata”
Zaro ido Jalila tayi
“Wace hawwan dazu fa da safe tazo”
“Bayan tafiyarki tafara nakuda”
“To meyasa akayimata aure yanzu se wahala takesha?”
“Aa seki bari in danginta sunzo ki tambayesu”
“Allah yabaki hakuri itakuma Allah yabata lafiya amma Dan Allah ki dawo Gida”
“Bazan dawo ba din a can zan zauna”
Ummi ta kashe wayar

Seda Jalal ya shafe sati baya kula Jawwad, sekuma daga baya Dan kansa ya sakko, suka shirya
yayinda kullum se Jalal yaje mashaya, Hannah tasamu damar cigaba da cusa kanta, a gefe daya itama Ilham tanata nata kokarin, sunsaka Jalal a gaba, Jalal dai se kara shirircewa yake

Alhamdilillah Neman maganar Jalila daga Islamiyya har boko yayi sauki, ta fara nutsuwa, yayinda mahaifin Hanan keta kyautatawa Jalila, amma Jalila ta takurawa Hanan, kullum tana manne da ita, Hanan ta zageta ta gaya mata bakaken maganganu amma Jalila batajin haushi takance mata”Hanan mahaifinki yana da karamci, yana kyautata min, komai zakiyi min bazanji haushi ba, shiya hadamu kawance kuma ni na karba”
Hanan mulkinta take zubawa a cikin makarantar daga malamai har dalibai shakkata sukeyi,amma banda queen J

Watarana anayiwa wata Yar ajinsu Jalila birthday a aji, kunsan yayan masu kudi aka dinga jijjiga champaign suna sakinta a sama, suka dauki turare suka dinga fesawa a ajin sun ware kida suna cashewa
Hanan ce ta nufo ajin ta shiga tana shiga wannan kamshin turaren da akasaka ta shaka nan take ta fadi kasa dama tanada asthma, da sauri Jalila taje kanta tana jijjiga ta
Yan ajin tsayawa sukayi suna kallon Hanan data ke ta fama da numfashi,
Jalila ta dinga jijjigata “Hanan meyafaru, ki tashi”
Jalila taga hakan bazeyiba tasa ta dago Hanan ta rungumeta zata fita da ita amma jikinta yariga ya saki yan ajin suna kallo ba Wanda yabi takan Hanan saboda rashin mutuncinta balle ayi tunanin me temakamata
Jalila ce kawai taketa kici² da hanan, ana haka Sega siyama
“Jalila meyasameta?”
“Nima bansaniba amma kaman asthma ne,”
Jalila da siyama ne suka kama Hanan suka kaita school clinic akaimata abunda yakamata amma babu wani cigaba duk ta fita hayyacinta
Aka kira gidansu hanan aka sanar dasu, sukace akaita wani asibiti private anan likitan dayake duba hanan yake,
a motar makaranta aka saka hanan Jalila tana rungume da ita tana mata fifita
Suna zuwa aka karbeta aka fara yimata abunda yakamata har tasamu bacci
“Likitan ya kalli Jalila yace sister din kice”
Gyada masa kai tayi
“Ya akayi bansanki ba kuna kama sosai”
Banza Jalila tayi masa tacigaba da kallon hanan har cikin zuciyarta ta kejin ba dadi halin da hanan ta shiga, saboda bata manta lokacin da hakan yafaru da ita a kanoba lokacin da Jalal ya duramata sigari, ta sha wahala amma condition din Hanan yafi worst
Se da baccin Hanan yayi nisa sosai, ga lokacin ta shi yayi Dan haka Jalila ta mike ta tafi Gida aka bar Hanan da wata malama a harabar asibitin taga daya daga cikin motocin gidansu Hanan ta shigo,
Ba ta tsyaba tayi tafiyarta Gida,
Ummi ke tambayarta ina ta tsaya tagaya mata abunda yafaru
Dan kallonta ummi tayi taga duk ta damu a ranta tace Allah sarki baby halinki halin abbanki ba kya riko sam,
“To Allah ya sawwake yabata lafiya”
“Ummi zakije dubata?”
Hararar Jalila tayi ta cigaba da aikin ta,
Washe gari da safe Jalila ta shirya ta dama kunun gyada ta zuba a flask ta tafi asibitin da aka kwantar da hanan, room din da Hanan take taje ta bude kofar ta shiga, mum Hanan ce a zaune tana ta fama da Hanan taci abinci taki, “ina kwana”
Jalila ta gaida Maman Hanan
“Ke mekikazo yi nan”?
“Hanan nazo dubawa”
“Waya nemeki, munji mungode, jeki Allah yabada lada”
“A a mummy dubanifa tazo, shigo kawata”
Hanan tayi maganar tana kallon Jalila,mikewa Jalila tayi taje gefen gadon Hanan ta zauna
“Sannu Hanan ya jikin baki”?
” da sauki Jalila, yau za a sallamemu ma”
“Allah yabaki lafiya, ga kunun gyada na kawomiki ni zan tafi makaranta”
“Jalila nagode sosai da abunda kikayimin jiya,”
“Bakomai manta kawata, Allah yabaki lafiya”
Jalila ta mike ta kalli mummy Hanan
“Mummy se anjima”
Dauke kai mummy tayi batace komai ba, Jalila na waigowa zata fita taci karo da Abdallah abakin kofa a tsaye, yaga duk abunda yafaru gaisawa sukayi ta ratseshi ta wuce
Bakin gadon Hanan yaje ya zauna”sannu autar mummy “
“Yaya kasan wani ABU?”
“A a sekin fada”
“Yanzu nakejin ban kyautaba abunda na dingayiwa Jalila a baya ba, bakaga yadda ta dinga kula dani jiyaba, kaman Yar uwata, ban tabajin naji babu dadi ba saboda na wulakanta mutum ba se akan Jalila”
Murmushi yayi”auta kinga illar wulakanta mutum ba, yanzu dai kwanta ki huta”
Tsaki mummy tayi ta tashi tabar dakin
Tundaga wannan ranar Hanan ta sake da Jalila har ziyara take kaiwa Jalila, ga kyautatawa da mahaifin Hanan yake yiwa Jalila, a sanadin Jalila Hanan ta dena wasu daga cikin halayenta marasa kyau

Haka lokacin ya dinga tafiya Jalal ya cigaba da fuskantar barazana a cikin rayuwarsa ga Hannah tasashi gaba, gefe ga Ilham da itama take uzzurawa rayuwarsa danma ita Ilham yanacin kaniyarta, ga Jeje da yake ta kuma rusa rayuwar Jalal, lalacewa har tafi baya, danma Jawwad yana kokari akan Jalal
Lokaci² Jalila takan yi miyagun mafarkan data sabayi da Jalal
Abun yana damunta sosai a rai,
Duk mafarkan da take dashi se dai taganshi a mawuyacin hali.

Yaune ake taron iyaye da yan uwa na kimanin dalibai arba’in na set dinsu Jalila, taron ya kunshi manyan mutane da iyayen dalibai, taro yayi taro inda aka karrama dalibai da dama, can na hango Jalila cikin graduation gound tayi kyau matuka takara girma tayi wani irin kyau, Jalila tana cikin dalibai naga ba da aka karrama da iyayenta, ta karbi kyautuka da dama sunyi hotuna da malamai da dalibai yan uwanta, mussaman Hanan da siyama ga Jawwad da Abba gefe ga ummi sunji dadin yadda sukaga ana ji da Jalila a cikin dalibai, a matsayinta na shugabar dalibai tayi speech me matukar ma’ana, ta birge mutane da dama, sunyi kukan rabuwa da dalibai sakamakon shakuwa da sukayi, haka taro ya tashi farin ciki fal zukatan dalibai
Bayan sunkoma gidane Jalila da Jawwad suka tafi yawo cikin garin Kaduna yayinda Abba da ummi suke tattaunawa akan makomar rayuwar Jalila, Jalila taji dadin fitar da sukayi da Yaya Jawwad sunsha yawo sosai tare da hira
“Baby naji dadin ganin yadda aka karrama ki gashi kinkara kyau kin girma u look so beautiful”
Murmushi Jalila tayi
“Yayana na kaina, jajircewar Abba ce tasa na taka duk wani matsayi a yanzu bazan manta karamcin Abba ba Allah yasaka masa da alkhairi”
“Ameen baby?”
“Amma Yaya Jawwad,Ina Jalal?”
Subucewa maganar tayi taji ta fito ba tare da ta shirya ba
Kallonta Jawwad yayi
“Meyasa kike tambayarsa bayan ba kyayimasa addua”
“Kawai tambaya nayi amma ina yimasa addu’a”
Gyada kai Jawwad yayi
“Jalila al amuran Jawwad se a hankali abun nasa sedai addu a kawai
Yana nan yadda kika sanshi, yama fida”
“Kuma har yanzu kana tareda shi?”
“Eh muna tare Jalila bazan iya rabuwa da shiba”
“Amma meyasa?”
“Kin manta alkawarinmu sekinzo kano zan gaya miki”
Gyada kai Jalila tayi sannan suka nufo Gida
Bayan sunkoma ne Abba da Jawwad suka tafi, tun bayan tafiyarsu Jalila ta fuskanci ummi bata da walwala tana cikin damuwa sosai lokaci² takan share hawaye
“Ummi wai meya farune me akayi miki, meyasa ki damuwa haka, kona bata miki Raine?”
“A a Jalila lokacine yayi daza a cika wasiyyar mahaifinki, zaki koma gurin wan mahaifinki, nima zanje ganawa dangin, munyi magana da Abba sati me zuwa insha Allah zezo ya tafi dake”
Ummi tayi maganar cikin kuka
“Gaskiya ummi ni ba inda zani ina tare dake, bazan iya zuwa wani guri in rayu ba tare da ke ba,”
“Am sorry baby wannan karon dole kiyi hakuri, nima zani inga iyayena, komawarki kano ba yana nufin mun rabu baneba”
“No ummi seda na rayu da soyayyarki for all this years lokaci daya acemin wai sena barki dama dagaske kike, ummi dama uwa zata iya Barin yarta?”
“Baby illa ne ga ratuwarki a matsayin ya mace ace kin girma an ta shi aurenki amma ace babu namiji tsayayye akanki, kiyi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa,
Zankoma ahalina kicigaba da zama a dangin mahaifinki ya aurar dake”
Kuka sosai Jalila ta dingayi ranar da take ta farinciki a gareta ta koma mata ta bakin ciki tayi kuka har ta gaji, haka nan yan kwanakin nan ta dinga yinsu ba kuzari se aikin kuka kawai ummi kuma se rarrashinta take tare dayi mata nasiha
“Baby duk inda kika samu kanki kizama me tsoron Allah, ki rike mutuncinki, kizama me tsoron Allah ki rike amanar tarbiyyar danayi miki, ina kaunarki baby nima ba a son raina hakan zata faru ba”
Ita dai Jalila jin ummi kawai takeyi
Saura kwana biyu tafiyar Jalila taje yiwa Siyama sallama sun sha kuka sosai Maman Siyama tai ta bata hakuri tayiwa Jalila alheri
Siyama ta tafi raka Jalila gidansu Hanan, Hanan rudewa tayi
“Jalila meyasa zaki tafi Zuwanmu Kaduna na kiyi abubuwa da yawa a gurin ki, meyasa zaki tafi bani da wata Yar uwa sama dake”
Duk yadda Jalila taso dakewa kasawa tayi suka dinga kuka Hanan tai musu jagora har gurin daddy, haka nan yaji ba dadi mussaman yadda yaga sunata kuka
Jalila tasoyi masa godiya kan alkhairan da ya dinga yimata amma kuka ya hanata nasiha yayi mata shima sannan yace insha Allah har kano zasu dinga kawo mata ziyara
Haka ta koma Gida ummi ta hada mata kayanta cif, data kalli kayan seta kuma fashewa da kuka
“Baby kukan nan ya isa haka, kirike abubuwan danake gaya miki, kizama me hakuri da rayuwa duk inda kika tsinci kanki, ki zauna da kowa lafiya, ki rikemin amanar kanki da tarbiyyar danayi miki,
Baby duk mijin da Allah yabaki ki masa biyayya, kiyi hakuri dashi”
“Ummi wai ya kikemin magana kamar me wasiyya”
Murmushi kawai ummi tayi tanaji a jikinta akwai wani abu daze faru da Jalila a kano amma ta dake taketa kokarin kwantar da hankalinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button