Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Su Jalila dake daf da bakin Layin suna tafe suna hira itada halima, sukaga motar Jalal ya dannota a guje, ga uban kura ya tayar ko gane motar ba ayi saboda gudu
“Tab anya Jalal kansa daya, wannan gudun yanzu inya bige wani fa?” Jalila tayi maganar cike da mamakin wannan mahaukacin tukin na Jalal
“Hmm kema dai kya fada, shi kota ransa ma ba yayi”
“To Allah ya shirya”
“Ameen”
Haka sukaje inda zasuje suka dawo, daf da magariba ne Dan haka suna idar da salla suka Dora sanwar dare
Ana idar da sallar magariba Jawwad Yakoma gurin Jalal yaga ya bude kofar, da sauri ya shiga amma Jalal baya ciki, ya duba bedroom dinsa da toilet baya cikin, se tarin kwalaben giyarsa, ya sha wasu, ya zubarda wasu, ya farfasa wasu kwalaben yayi kaca² da dakin tundaga palour har bedroom
“Ya salam”
Jawwad ya furta ya dakko wayarsa ya fara kiran Jalal amma seyaji wayar tana ringing a kasan pillows akan gado
Cikin gidansu Jalal ya shiga a rude, ya tarar da mummy tana kallo a palour
“Mummy Dan Allah kokinsan inda Jalal yake?”
“Kamarya nasan Inda yake, ai kai yakamata in tambaya, baya part dinsa?”
“Baya can na duba, kamaar akwai abunda yake damunsa mummy tun jiya baya cikin nutsuwa,”
“Ni rabona da shi yau kusan kwana hudu”
Dan zaro ido Jawwad yayi
“Kwana hudu mummy, kuma baki nemeshiba yana part dinsa baya zuwa ko ina, yau kawai yafita kuma be gayaminba”
“To kai kenan daya daukeka da mahimmanci kana sanin inda yake, ni ko inda nake seya ga dama zezo, ina gani kuma Duk inda yaje ze dawo”
Jikin Jawwad ne yayi sanyi jin abinda mummy ta fada,
Da sauri Ilham ta karaso palour da sauri
“Au wai kaima baka San inda yakeba, na dauka kana tare da shi”
Ilham tai maganar a firgice
“Eh amma ki kwantar da hankalinki zanje nemansa insha Allah ze dawo nasan ba nisa yayi ba, ni abinda yafi dagamin hankali dana je na tarar ya farfasa abubuwa a dakinsa”
Zare ido mummy tayi
“Haba dai?”
“Eh mummy shiyasa ma nazo na tambayeki, narasa meyake damunsa”
“Watakila giyar ya sha tagaya masa karya, amma muje bangaren nasa”
Tare suka tafi da mummy da Ilham suna zuwa suka tarar da mugun aika² da Jalal yayi duk wani abu me fashewa Jalal ya fasashi, hankalin mummy ya ta shi sosai
“Na shiga uku Jawwad meyasami Jalal hakane? Be taba irin wannan abunba fa”
Ita kanta Ilham abun yabata mamaki sekace dakin mahaukaci ya farfasa abubuwa
Jawwad ne cikin muryar rarrashi yafara magana
“Ki kwantar da hankalinki mummy, insha Allah ze dawo gida, amma yanzu bari in fita in dudduba inda yake zuwa na San tabbas akwai abunda yake damunsa”
Gyada kai mummy tayi tana share hawaye
Bayan mummy da Ilham sun koma cikin gidane mummy se kuka take “Allah yasa yaron nan ba haukacewa yayi ba,”
“Haba mummy ya kike fadin hakane, insha Allah lafiyarsa kalau”
Ilham ta fada cike da kwarin gwiwa sannan ta nufi dakinta tana zuwa dakin ta kule tasaka masa key
Sannan ta kira mahaifiyarta
“Hello maami”
“Na am Ilham, yakike akwai labarine”
“Eh Mami, Jalal ne ya haukace fa”
“Kamar ya ya haukace ban gane me kike nufi ba,”
“To hauka mana kwana hudu yana kulle kansa a daki Jawwad kawai yake budewa, yau kuma shima din be bude masa ba, ya fita dazu da yamma, amma duk ya farfasa kayan dakinsa bakiga dakinba kamar mahaukaci”
“Ina baze yiwuba, bahaka nakeso ya kasance ba, ba hauka nakeso yayi ba, idan yayi hauka Dan gatan mahaukaci ze zama,
Sonake se yazo hannunmu mun wulakanta hadiza, mun tozarta ta, setayi kuka fiye da Wanda tayi a baya”
“Amma Mami ta Yaya kina gani kullum shirinmu rushewa yake, abinda ya kawoni gidan nan shekara da shekaru mun kasa samu”
“Amma kinsan duk laifinkine da rashin kokari Ilham ni narasa ma zaman me kikeyi abu yakici yaki cinyewa tsawon shekaru”
“Maami dukfa abinda kikasani inayi, amma kinsanshi muguwar gaddama CE dashi gashi jarababbe”
“Hakane amma zankoma gurin malamin nan inji mekuma zecemana”
“To Mami, yadda kukayi kya gayamin, amma da gani nake kawai inyi me gaba dayan nan ina fargabar aikinmu ya lalace”
“Har yanzu kina ganin alamar yana da budurwa ne?”
“Eh mana Mami shiyasa duk na tsorata fa”
“Ki kwantar da hankalinki babu abunda ze faru just focus”
“To mamina nagode, amma bakiga kukan da mummy tayiba”
“Ita tasani ni be dameniba”
Haka sukayi sallama da mamanta
Jalila ce ta fito harabar gidan da parker a hannunta taga Jawwad a sukwane ze bude motarsa, da sauri Jalila taje gurinsa
“Yaya lafiya ina Zaka haka naganka a firgice”
“Jalila Jalal ne banganiba gashi ya farfasa abubuwa a dakinsa bansan inda ya tafiba, shi zan tafi nema”
“To ai dazu da nafita raka halima naga fitarsa a mota kamar ze tashi sama, yana ta gudu a mota”
“Are u serious?”
“Of course naganshi dazu, amma Yaya Jawwad ka nutsu mana, duk ka tayar da hankalinka”
“Jalila, Jalal be taba hakaba bakiga dakinsaba kamar ba dakin Dan Adam ba ya fasa komai”
Gabanta ne yafadi “to ko in raka ka ?”
“No kizauna bari inje”
“To adawo lafiya Allah ya kiyaye, amma kayi driving a hankali”
Gyada mata kai yayi ya shige motar yajata da sauri

Share please
More comments more typing…………………..
Inajin dadin comments dinku, kuna comments ina muku typing
Am proud of you all
❤❤❤❤

????️????️????️????️????️
[8/31, 8:30 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE- 32

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

      -MY FIRST NOVEL-

Jawwad ya ja motar yabar cikin gidan, fara zagawa yayi clubs din da yasan Jalal yana zuwa amma be sameshi ba, tun bayan magariban nan yake yawo amma be samu ganinsa ba, Gida ya koma yabar motarsa a bakin layi yakoma part din Jalal ya dakko wayar Jalal ya koma inda yabar motarsa, ya shiga ya zauna cire wayar yayi daga key dayake yasan password din, call log dinshi ya duba yaga kiran Hannah dayawa amma be daga ba lambar Jeje itace ta karshe da aka kirashi dashi kuma shima be amsaba,
Dafe kai Jawwad yayi “ohh my God Jalal ina kashiga ne karka yiwa kanka Illa mana”
Lamabar Jeje ya kira, yai Sa a kuwa Jeje ya daga
“Ina Jalal yake?”
“Kamar Yaya?” Jeje ya tambayeshi
“Kamar yadda na tambayeka”
Jawwad ya bashi amsa
“Ohhh in ka damu da shi seka zagaya mashayar da yake zuwa kaneme shi,”
Jeje ya kashe wayarsa
Girgiza kai Jawwad yayi ya kuma kunna motarsa ya marasa ina ze dosa Neman Jalal
Haka ya dinga zaga clubs har gurin goman dare, club din dayaje da farko ya koma Wanda nan Jalal yafi zuwa, Jawwad ya duba ko ina amma bega Jalal ba,
Yazo ze fita ya hangi motar Jalal a can wani guri da sauri ya fito ya nufi inda motar Jalal take, bude motar yayi da sauri Jalal yana zube a cikin motar ya fita hayyacinsa sosai, gashi nan dai shiba sumamme ba kuma shiba me bacci ba
Dagoshi Jawwad yayi yana jijjiga shi
Da sauri Jawwad ya koma ya bada ajiyar motarsa gurin masu gadin club din ya shiga motar Jalal ya jata ya nufi Gida
Jalila kam tagagara yin bacci tunda Jawwad ya fita tana palour a zaune tana jiran dawowarsa tun suna hira da Halima har Halima ta tafi ta kwanta tabar Jalila a palour
Karfe sha dayan dare taji motar Jawwad ya dawo
Da sauri ta fito setaga motar Jalal, tana nan tsaye taga Jawwad ya fito daga motar
“Yaya lafiya kuwa naga ka Dade?”
“Baby da kyar Nagano Jalal, yanzu dare yayi bari inkira Me gadin gidansu Jalal ya kama minshi in kaishi part dina”
“To shike nan”
Jawwad ya juya da sauri, Jalila takarasa bakin motar ta leka, Jalal yana kwance Kamar gawa, ba a dadeba Sega Jawwad sun dawo dame gadi
Suka fito da Jalal suka shiga dashi suka kwantar da shi akan gadon Jawwad
Jalila ta kalli Jawwad “yaya wai meyasameshi? Bashi da lafiyane”
“Wallahi ban saniba Jalila inaga giya ya sha dayawa”
Dan zare ido Jalila tayi
“To se yaushe ze tashi”
“Se lokacin data sake shi, amma akwai abunda yake damunsa a rai, Wanda bansaniba”
Jawwad yafada cike da damuwa
“Yaya kalli yadda yake numfashi ko bashi da lafiya, kalli jijiyar kansa fa duk sun daga”
Jawwad ya kai hannu goshin Jalal yayi zafi sosai
“Da alama kansa yana ciwo ma”
Kafarsa Jalila ta kalla ta mike da sauri
“Yaya Jawwad kalli kwalabe sun fasa masa kafa”
Da hanzari Jawwad yazo ya duba kwalabe duk sun shige kafarsa
“Ya salam inaga bari in fita akwai wani abokinmu likitane, bari inga in yana nan yazo ya duba shi inba ya nan kuma, inzo in kaishi asibiti”
Ya Ciro wayar JALAL ya ajiyeta akan side bed
“To kayi sauri danni tsoro nakeji palour zan koma danaga ya taso in zura da gudu”
“Jalila da hankalinsa ba haukacewa yayiba kinji, ki zauna a parlour kiji rani”
Gyada masa kai tayi, ta fito parlour ta zauna shikuma Jawwad ya fita lokaci² Jalila seta leka dakin taganshi a kwance yadda a aka barshi, motsi taga yafarayi a hankali yana yamutsa fuska yana surutai cikin maye
“Hannah meye hakane, bakida hankaline,? Mtseww nace miki bana so fa, bana son yimiki rashin mutuncine amma ba kya ganewa”
A hankali Jalila ta Dan shiga dakin tana kallonsa
“To wace kuma Hannah,”
Jalila tayi maganar a zuciyarta
Cigaba yayi da surutai idonsa a rufe ya cigaba
“Nifa Jeje giyar nan yau kaman ba irin wadda nasaba sha bace kamar akwai wani abu a ciki, mtseww, nii ban San meyake damuna ba Jawwad baya son giyar nan danake sha fa”
Jalila ta kalleshi
“Kai ni dalla ka isheni ka cikamin kunne, kayimin shiru, nina aikeka ka sha kalleka Dan Allah, mutum har mutum amma ba hankali, ko kunya bakaji kake shan giya kai ko tsoron Allah bakaji ma bana tunanin kayi sallar isha’i, kana kwance kana maye, kasa Yaya se wahala yake in bakayimin shiruba nida kaine”
Jalila se rashin M takewa Jalal shikam baya hayyacinsa, yacigaba da surutansa
“Ko wace kuma Hannah oho masa”
Wayar Jalal ce tafara ringing ta kalla sunan Hannah ta gani a kan screen din wayarsa,
“Hmm kishiyar Ilham ce Ashe”
Tayi banza da wayar takoma palour, wayarce ta cigaba da ringing ta cikawa Jalila kunne Dan haka ta mike ta koma bedroom din ta kai hannu ta daga wayar
“Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, me wayar kin ganshi a kwance, tunda kika kira be dagaba ai seki hakura ko, saboda shirme a tsohon Daren nan haba, kinkira ba adagaba sekace mayya duk kincikamin kunne”
Jalila tai tsaki ta kashe wayar ta kai hannu zata aje wyar ya rike hannunta gam ya bude Jajayen idanuwansa fes akan JALILA
Kwalalo ido Jalila tayi ta firgita matuka
“Meye haka kacikamin hannuna”
Ko kyafta idonsa bayayi akanta gashi ya riketa gam ko motsa hannun bata iyawa, idonsa tsoror yake bata
“Na shiga uku nika cikani, dama ance watakila ka haukace”
Kara karfin rikon yayi mata
“Wai meye hakane”
Setaga hawaye na bin gefen idonsa can yayi wani yunkuri se yafara amai kumface kawai take fita daga bakinsa, yasaki hannun Jalila a hankali
Zare ido tayi dataga irin aman dayakeyi
“Nikam ina Yaya Jawwad ya tsaya haka”
Itakam Hannah mamakine ya cikata wace ta dauki wayar Jalal a Daren nan, OK ko Itace kanwar tasa da Jawwad yake fada, to me take masa a wannan lokacin haka?
“Tabdijan to wallahi da sake akwai matsala”
Jalila ta koma bakin kofa ta zuba masa ido Dan tarasa meya kamata tayi can jimawa Sega Jawwad ya dawo shida wani
“Sorry Jalila kinganni ban dawo da wuriba, seda naje Asibiti na dakko likitan”
“To gashi can dai wani irin amai yakeyi yana surutai”
Da sauri Jalal da likitan suka shiga cikin dakin
Likitan ya kalli bakin Jalal duk wannan kumfar fara
“Subhanallah” ya furta yasaka abu ya goge masa kumfar yayi masa wasu allurai
Jalal ya dinga aman abunda yaci
Likitan ya kalli Jawwad
“Jawwad Jalal wasu miyagun kwayoyi yasha Wanda besaba shan irinsu BA, suke nema suyi masa illa”
“Bayan giyar kuma hada kwayoyi”
Jalila tafada cikin mamaki
“To gashi nan dai, kuma da alama ya Dade beci abinci ba”
Likitan yabata amsa, girgiza kai kawai Jawwad yayi, Jalila ta koma palour
Shida likitan suka gyara gurinda Jalal yai aman suka canzamasa kaya zuwa Jallabiya
Kafar Jalal aka ciremasa kwalaben daya taka, sannan yasa masa drip, ya rubuta magunguna yacewa Jawwad da safe yaje ya siyo masa,
“Yaya ni Bacci nakeji seda safe”
“To baby mungode sosai, kiyi bacci me dadi”
“To Yaya kaima ka kwanta haka dare yayi”
Ya gyda mata kai likitanne ya kalli Jalila
“Baby ni baza ayimin sallama ba?”
Dan murmushi tayi
“Seda safe tafada a takaice”
Jawwad kam Dan hade rai yayi, ya kalli likitan “muje in maida kai”
“Jawwad dan Allah wannan babyn fa nifa na faller wallahi, Yar gayu da ita ga iyayi”
“Ina ruwanka da wacece, nifa banason irin wannan abun salis, muje in saukeka ni”
“Tuba nake sirikina amma nikam naga guri”
Fusata Jawwad yayi “kaga wuce muje”
Haka suka tafi ya maida doctor, se bayan karfe daya sannan Jawwad yasamu nutsuwa lokacin drip din jikin Jalal ya kare ya cire masa, sannan ya kwanta
Bayan sallar asuba Jalila take gayawa Nana a gidan Jalal ya kwana, yanata a man kwayoyin da yasha
“Tab to indai wannan ne sun saba, amma iya sanina baya shan miyagun kwayoyi, sedai giya da taba, watakila Suma yafara watsa abunsa wayasani, kice hadake akai jinya”
Nana tafada Dan Neman magana
“God forbid indai Dan ta shine, yaje ya karata ni Yaya Jawwad ne abun tausayi wallahi”
“Mutane dayawa na mamakin kaunar da sukewa Juna, Allah ne ya hada jininsu”
“Kuma a haka Aminiyarki take sonshi”?
” mhmm kema dai kyafada”
“Hakane, amma Nana Dan Allah wace Hannah”
“Hannah kuma? A ina take”
Se Jalila ta fuskanci Nana batasan zancenba Dan haka tace
“OK don’t mind me kwanta kikoma baccinki, Dan nasan yanzu shiya dameki”
“Aikuwa kamar kuwa kinsani”
Jalila kam mikewa tayi ta tafi kitchen Dan sarrafa abunda za a bawa ciki, Jalila tana matukar son harkar girke²
Tunda sauran duhun asuba ta shiga kitchen zuwa bakwai da rabi ta kammala
A palour ta hadu da halima
“Anty leemat barka da safiya”
“Barka dai sayyada Jalila, naji kamshi yana tashi ba dai kingama girkin ba”
“Nagama, kina bacci ne shiyasa ban tasheki ba”
“Sannu da kokari, ke ba kyajin aiki Sam, amma tun asuba kika fara”
“Eh halima, wallahi kinga Jalal ne ba lafiya za a bashi magani da safe nasan Yaya Jawwad ni ze roka in hada musu breakfast, kinga gara ayi tunkafin yayi maganaa”
“Gaskiya kam, bari inje in karasa, aikin da ya rage”
Zuwan Jalila gidan nan ba karamin amfani yake musu ba Sam batada kyuya, ba ta San kazanta Sam, shiyasa Jawwad yake jin dadin sakata aiki ba kyuya, amma Nana yanzu zata bata rai tana tura baki, ga son jiki a cikin Nana, kuma Maama take biyemata
Ta hado kayan Abincin ta kai part din Jawwad, ta tarar yana zaune a palour da Azkar a hannunsa, sallama datayine yasashi dagowa
Murmushinsa ya fadada
“Sannu da kokari baby, yanzu nake tunanin yaza ayi da breakfast, naga jiya baki kwanta da wuri ba kar in takura miki, nagode da kulawar da kike bamu, sannu da kokari”
Karasawa tayi parlour ta ajiye kayan abincin ta kalleshi
“Barka da safiya, Dan uwa rabin jiki,”
“Au bazaki amsa sannun nawa ba”
“Ni lafiyata kalau, wancan mutumin na cikin dakinka zakayiwa sannu, shine Mara lafiya”
“Kinganki baby, Jalal dinne mutumi ko? In yajiki ba ruwana, kinsan boss din ba wasa”
“Hmmm lallai boss naga alama”
Sukayi dariya a tare JAWWAD yace
“Jikin nasa da sauki, ya tashi tun dazu yanzuma wanka yakeyi”
“To Allah ya sawwake”
“Ameen baby”
Kallonsa Jalila tayi sannan tace
“Dan uwana”
“Na am kanwata”
“Bakayi bacci sosai ba idonka ya nuna”
“Kema bakiyi bacci ba gashi kuma nasan kin gaji”
“Ni bangajiba”
“Dagaske”
“Eh mana, kasan wani abu”
“A a baby sekin fada”
“Yayana kaina mussamanne a cikin mutane, halinka halin Abba, kanada kirki yayana, Allah yaabamu itaku”
“Baby ni banga wani kirki danake dashi ba, kinfini kirki baby, sedai ince Allah yabamu itaku”
Zumbura baki Jalila tayi
“Nida ake cemin masifaffiya, uwar Neman magana,”
Dariya Jawwad yake sosai
“Wayagaya miki haka”?
Bude kofar bedroom din Jalal yayi ya fito yana dingisa kafarsa Jallabiyar Jawwad ce a jikinsa tayi masa kyau sedai fuskarsa ta rame
Karasowa yayi ya zauna a kusa da Jawwad
“Sannu Jalal ya jikin naka?”
Jawwad yafada cikin damuwa
“Da sauki, Nagode Jawwad”
Jalal yafada a hankali
“Kasan zamuyi fada ko tom yanzu ga breakfast baby ta kawo, ka karya se inje in gayawa mummy kadawo daga nan in siyo maka magani”
Gyada masa kai kawai Jalal yayi
“Baby bakiwa Jalal ya jiki ba”
“To ai naga ya warke tunda gashinan da kafarsa”
“Jalila sarkin magana yanzu dai jeki kawo mana ruwan dumi Wanda za a gasa masa kafarsa”
“To” ta mike tabar parlour, Jawwad yahada masa breakfast din sannan ya mike “bari inje in siyo maganin, in ta kawo ruwan dumin in bazaka iya gasawa ba kabari in dawo”
Jinjina kai Jalal yayi, har Jawwad ya nufi hanyar fita ya tsaya ya waigo
“Yawwa idan na dawo kuma zaka gayamin meyasa ka fasa kwalabe ka taka seka gayamin meyake damunka”
Still dai bece komai ba
Jawwad seda yaje yagayawa mummy yaga Jalal yanzu haka ma yana gidansu, amma bashi da lafiya
Mummy taita godiya tana sawa Jawwad albarka, Ilham kuwa najin haka ta gashi ta tafi gidansu Nana domin ganin Jalal, Jawwad kuma yatafi karbo magun gunan
Jalila ta kawo ruwan zafi a flask tai sallama amma yamata shiru tazo ta dire flask dina gefen Jalal
“Wai ba nace ka dinga amsa sallama ba,
Gashi nan ruwan zafine in kaga dama ka dumama ka gasa kafar taka in baka ga damaba ka zuba a haka” har zata fita dawo ta tsaya a gaban Jalal
“Saboda wauta waya gaya maka in abu na damun mutum haka akeyi kafasa kwalabe kabi ta kai, kuma kaje ka sha kwayoyi, kakusa kashe kanka daka mutu haka zaka farka a kabari
Ga laifin sabawa iyaye, ga shan giya, ga kashe kanka dakayi da abun yamaka yawa, in abu yana damun mutum a zuciyarsa addu a yakeyi ya koma ga Allah, ba ya aikata wannan shirmen da kakeyiba, duk Wanda be kiyaye salollinsa akan lokaciba haka kunci zeta damun rayuwarsa”
Yana jinta ya cigaba da cin Abincinsa dukda bawani ci yakeba cakala kawai yake, yana tausayawa ranar daze hukunta Jalila,
se yanzu ta kai duba ga cin abincin dayakeyi, da hannun hagu yakecin Abincin
“Subhanallah Kaikam komai naka na dabanne, komai naka ba irin na mutane ba”
Tasa hannu ta karbe cokalin hannunsa daga hannun hagu ta zira masa a hannun dama
“Shedan ne yake cin Abinci da hannun hagu, Allah yasa kayi bisimillah kan kafara cin abincin”
Dago idonsa yayi yasaka a cikin na Jalila
“Kin manta waye Jalal ko?”
“Eh namanta seka tunamin”
Ilham ce ta shigo palourn ba ko sallama a tare suka waigo suka kalli Ilham
Ilham ce tayi mutuwar tsaye ganin Jalila a tsaye a gaban Jalal shikuma yana kallonta ga abinci agabansa kamar wasu masoya
Watakilama a baki take bashi abincin wani sashi na Zuciyarta ya zigata
“Mezan gani haka? Yaya Jalal menayimaka haka, kake kokarin cin amanata wannan itace sakamakon soyayyar dana dau shekaru inamaka, lokaci daya kayimin haka dama abunda na Dade INA zargine yau Allah ya nunamin”
Saroro Jalila tayi tana kallonta
Ilham ta dawo da idonta kan Jalila
“Munafuka kina cemin Yar wahala Ashe kece babbar Yar wahala, Ashe hasashena ya tabbata son Jalal kike, to wallahi baki isaba kinyi kadan kiyi takara dani akan abunda nakeso bans…..
” enough malama karkiga nayi miki shiru kicigaba da zagina, mezanso anan” ta nuna Jalal
“Ni abu na kawo nake masa magana akan abunda ya aikatawa kansa banda haka ni babu abinda ze hadani da shi”
Shidai Jalal bece musu uffan ba sema mamakin hakikancewa da Ilham take, yakeyi
“Karya kike wallahi ko duk jikina kunne ne bazan yaddaba kuma wallahi Jalila sekinyi danasanin abunda kikayimin, sena baki mamaki
” ya isheki malama”
Jalila ta karaso gaban Ilham “bude idonki da kyau, ki bude kwakwalwarki kiga da wacce kikeyi, inkin manta bari in tuna miki Jalila ce dawo hayyacinki, Dan kinga ina lallabaki ba amin hauka wallahi yanzun nan zan saukemiki abunda yake damunki
Me akai akayi Jalal meye abinso a tareda Jalal wannan makakken Mara tarbiyya, shi kike nufi Jalila taso, ko ta nuna a matsayin uban yayanta, a tunaninki zan tsaya ina daga murya saboda shi
Yadda yake a maken nan ai se makakkiya Yar uwarsa, badai Jalila ba ni mutumin arziki zan aura Dan babu uban me hankalin daze bawa wannan yarsa a haka
Kema da kike sonnashi kinada manufar hakan badan hakaba yadda yake wulakantashi yaci ace kin hakura useless and hopeless creatures dagake harshi”
Tirkashi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button