ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Akayi sallar magariba, da kyar Jalila ta mike tayi salla, tana idarwa ta zube a gurin saboda azababben ciwon dataji kanta yanayi,
Nana takuma shigowa ta tarar Da Jalila ta dunkule akan dadduma, durkusawa Nana tayi ta dafata
“Jalila har yanzu kanne yake miki ciwo”
Jinjina kai kawai Jalila tayi, mikewa Nana tayi ta dakko mata magani ta kawo mata, Jalila ta kalli maganin
“Nana ki bar maganin nan, ni banaso”
“Saboda me haka zaki zauna da ciwo”
“Kibari kawai ze dena, idan na sha maganin nan amai zanyi”
“Ohh my God, sannu amma kina cuta bazaki sha magani ba”?
Har wajen isha doctor salis yana gidan suna hira jefi², ya zauna ne koda Allah zesa yaga Jalila amma shiru be ganta ba,
Halima tayi sallama, ta kawo musu abinci, Jawwad ya kalli Halima yace
” Halima ina Jalila ne?”
“Bata jin dadine, ta kwanta nikadai nayi girki yau”
“Subhanallahi me yasameta haka”
Jawwad yafada a Dan tsorace
Halima tace “Naji tacewa Nana kanta yana ciwo”
“Ta sha magani ne”?
“Wallahi ban saniba”
“OK jeki, ki kirawomin ita, inzata iya zuwa, tunda salis be tafiba seya dubata”
“To bari inje”
Ta mike ta koma cikin gida, Jalal yana jinsu bece komaiba,
Doctor salis ya kalli JALAL
“Wace kuma JALILA, naga Dan uwanka ya damu, nidai nasan Nanace kawai kanwarsa”
“Kabari ta zo sekaga wace”
Jalal yabashi amsa
Halima ta koma cikin Gida, ta tarar da Nana tana bawa Jalila tea,
“Jalila yayanku yace kije likita yana nan ya dubaki”
Nana ta kalli halima
“Daga zuwa kai abinci Harkin gaya masa”
“A a tambayata yayi”
“To jeki angode”
Seda Jalila tagama shan tea sannan ta kama hannun Jalila suka fito
Suna daf da Barin palourn Maama ta hangosu
“Me Nana INA zakuje haka”
“Jalila CE bats da lafiya , shine Yaya JAWWAD ne yace taje doctor salis yazo se yadubata
” Allah ya sawwake”
Shine abunda Maama tace tashige kitchen, itakuma Nana suka fito
Nana ce tayi sallama, suka amsa
Jawwad ya mike da sauri,
“Subhanallah baby, abin har ya kai haka, sannu”
Jin ance baby yasa doctor salis saurin waigowa
Jalilace fuskarta duk tayi ja hawayene kawai ke fita daga idonta
“Subhanallah Ashe babynmuce ba lafiya”
Doctor salis yafada yana mikewa tsaye
Guri tasamu ta zauna,Nana ta zauna a kusa da ita
Nana takalli Jalal
“Yaya Jalal ina wuni”
“Lafiya sannu”
Hada ido sukayi da Jalila ta galla masa harara, kawai se yayi murmushi yacigaba da latsa wayarsa
Jawwad se jera mata sannu yake
Doctor salis ya kalleta
“Sannu baby dama sunanki Jalila, a very sweet name”
Shiru Jalila tayi masa ta kwantar da kanta akan cinyar Nana
Jawwad ya hade rai
“Kaga cewa nayi ka dubata ba ka dinga yimata shirme ba, in bazaka dubataba zan dauketa mutafi Asibiti”
“To ai dubatan zanyi, kake min masifa”
Doctor salis yakuma kallon Jalila
“Baby kidena kukan mana, kinfiye shagwaba in mutum bashi da lafiya ba kuka akeba,
Yaushe kan yafara miki ciwo?”
“Dazune” tafada a kasan makoshinta
Nana ce tayi yinkurin dagota tareda cewa
“Jalila ki tashi kiyi masa bayani, bayajinki fa”
Jalila ji tayi Nana ta fama mata hannunta da Jalal ya murda da sauri ta furta
“Wayyo Allah Nana hannuna”
Jawwad yakuma rudewa
“Baby mekuma yasamu hannun naki”
Jalal ta kalla, amma shi ya maida hankalinsa kan wayarsa, shi yadda Jawwad ya rudene yake bashi haushi
Wani hawayen takaicine ya zubo mata
“Bigewa nayi da kofan toilet”
“Gaskiya zanyi fama, baby haka kike shagwababbiya komai kuka”
Doctor salis yai maganar cikin zolaya
Wani mugun kallo Jalila tayi masa cikin tsiwa tace
“Sunana Jalila karka kuma cemin baby”
“To yi hakuri na dena, yanzu inane yake miki ciwo”?
Murmushi Jalal yai a ransa yace indai wannan yarinyar ce kacigaba dayimata shishshigi, ba karamin aikinta bane ta zageka
Doctor salis yagama yimata tambayoyin daze mata yace a Alluran dayayiwa Jalal akwai guda daya da ze mata sekuma magani daze bata
Zumbur ta mike zaune
” Allura kuma, Yaya Jawwad ina tsoron Allura,”
“Yi hakuri a hankali zeyimiki”
Shidai doctor salis wannan shagwabar ta Jalila birgeshi yake
Nana tace
“To ai maganinma ba sha kike ba gara ayi miki allurar”
Aka zuko Allura, Jalila tace sedai ayi mata a hannu, salis yace ta miko hannun, ta mika masa sannan tace
“A hankali Dan Allah”
“To shikenan a hankali zanyi miki”
Ta mika masa hannun, da kyar akayi allurar nan tana ta kuka,
Shikam goga ko uffan bece musuba dayaga suna biye mata haushi ya isheshi ya tashi yabar musu dakin
Salis yace allurar da yayiwa Jalila ta isa sedai in ciwon kan yaci gaba ai masa magana
Nana takama hannun Jalila suka koma cikin Gida a zaune tayi sallar isha’i saboda ciwon da kan yake mata tana idarwa ko canza kaya batayiba ta haye gado takama baccin wahala, Dan ta manta da batun duba Jarrabawa
(Gaskiya Jalal ya iya rankwashi,)
Da safe bayan tayi sallar asuba takoma baccinta, ranar ko tsinke bata dauke a gidanba balle tayi musu girki
Aikuwa dai Abincin yau da banbanci don Sam be kai dadin na Jalila ba
Har LA asar Jalila bata fitoba, sedai Yaya Jawwad har daki yazo ya dubata ya tarar tana bacci
Salis yakira Jawwad a waya ya tambayi ya jikin Jalila, Jawwad yace masa da sauki,
“Jawwad Dan Allah ka hadani da baby mana in mata ya jiki,”
Jawwad kashe wayarsa yayi, yana mita
Jalila tana daki da yamma, taji hayaniya a harabar gidan, Dan haka tafito dama wunin ranar bata fito ba, Abbane ya dawo daga lagos, ya canzawa Jawwad dankareriyar mota, duk anje an kewaye motar, yayinda Jalal ya kame a cikin motar sekace tasa
Murmushi Jalila tayi Abba sannu da zuwa gaba daya suka waigo suka kalleta, ta Dan rame sosai, idonta yayi wani iri
Abba ya kalleta
“Baby meyafaru ko bakida lafiya ne?”
“Lafiyata kalau bacci nayi”
Nana tai saurin cewa
“A a Abba batajin dadine”
“Eyya Nagani fuskanta ya nuna”
“Abba ciwon kaine fa kuma na warke”
Takalli motar
“Masha Allah, Abba mota tayi kyau Allah yasaka maka da mafificin alkhairi, Allah yakara arziki, amma wa aka saiwa motar naga me motar daban Wanda ya kame a cikin motar daban”
“Lallai yarinyar nan har yanzu bakinta be mutuba ga muryarta har ta dashe saboda kuka”
Jalal yai maganar a ransa
Abba yayi murmushi
“Jalila kayan Jalal aina Jawwad ne, Dan haka tasuce su biyun” Jalila ta kalli Jawwad
“Yaya congratulations Allah yasa rai da lafiya akayiwa”
“Ameen baby mungode”
“Abba to mu se yaushe za a saimana?”
Nana tai maganar a shagwabe
“Ku tambayi yayanku, shize saimuku, gata mamanku can Ku dinga hawa ko Jawwad yabaku tsohuwar tasa, in kunshiga university seku dinga Ja”
“Abba ta Yaya Jawwad dinfa duk ta tsufa wallahi,”
“Yana jinki dai, in kun gama Ku nabaku naku tsarabar a cikin Gida”
Daga nan Abba yai cikingida yana dariya, Maama tabi bayansa
Jalila ta kalli Jawwad
“Yaya muje a danamu a motar, dama zamuje duba exams”
“To ku taho muje daga nanma muje shan ice cream”
“Amma Yaya yaushe zaka fara koyamana mota,?”
Nana ta tambaya
“Ku tambayi Jalal seya koyamuku rigimanmun Abba kawai”
“Tabdijan, waye ze koyamana tukin, ba tukin jirgin sama mukeso akoyamana bafa tukin mota Yaya Jawwad, wannan ai tukin jirgin sama yakewa mota”
Jalila tai maganar tana hararar Jalal, yana kallonta ta cikin mudubin motar
“Ba ruwana ke dashi”
Jawwad yafada yana dariya, cikin Gida suka nufa suka dakko hijjabai, da wayoyinsu suka fito
Tunda Jalila taga, Jalal a mazaunin direba taga shi ze tuki jikinta yayi sanyi, Dan tana ganin yanda yake Jan nasa motar