Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Jalila hartayi shirin kwanciya Abdallah ya kirata suketa hira dashi da ita da hanan, a wannan lokacin kiran JAWWAD yaita shigowa amma line busy, Jawwad ransa babu dadi ya kwanta, yana tunanin dawa Jalila take waya tsawon wannan lokacin

Tunda Jalal ya tafi yake tunanin ya akayi Ilham ta daga masa waya, meya kaita part dinsa shabiyun dare ( besan Jalilace ta amsa wayarba, lokacin da bashi da lafiya”)
Shi babban takaicinsa ma cewar da tayi inta hanashi abu be isa yayiba, yaushe yake shiga harkarta dazatayi masa karya, ta zubar masa da kima a gurin wata mace daban aikuwa se ya hukunta Ilham Dan baya son karya (Ilham zata amsa query maimakon JALILA ????????)
Ya koma Gida yana zuwa ya tafi part dinsa don kuwa by now yasan mutan gidan sunyi bacci, yanazuwa yai wanka ya canza kaya sannan yasha giyarsa iya son ransa sannan ya kwanta bacci
Daren ranar Ilham tayita sake² yadda zata canza takunta na zama a gidan, domin Janyo hankalin Jalal kanta Dan wannan karon ta sawa zuciyarta lallai seta cika burinta.
Da safe Jalila kaman yadda ta saba tayiwa halima Karin karatun Qur’ani sannan suka tashi sukayi aikace² daya kamata suka hada breakfast
Kamar kullum Da sassafe Jalal yake zuwa saboda suna motsa jiki, in sukayi suka gamane we yayi wanka ya canza kaya, a gidan,
Ya lura da rashin walwala na Jawwad amma bayaso yafiye takura masa, bayan sungama exercise ne Jawwad yai wanka yaketa shirin tafiya makaranta, saboda ze shiga lectures karfe tara
JALAL ya kalleshi ” wai yanaga Janata shirin tafiya makaranta breakfast dinfa”?
“Nakoshi”
Dan zare ido Jalal yayi
“ka koshi kuma, me akayi maka ne? Naga se fushi kake, meyasa kake so ka tafi makaranta bakayi break fast ba”
“Haka nan, yau bana son cin abincine”
“Ban yadda da abunda kafada ba, baka fiye yin fushiba, kana iya boye damuwarka, amma tunda nagane kana cikin damuwa nasan matsalar babbace,”
Dan murmushi kawak Jawwad yayi “meyasa bazaka yadda ba ne?”
“Shikenan naji amma ban yadda ba”
Jawwad ya cigaba da shirinsa, Jalila ce tai sallama
Jawwad ya amsa tareda basar da ita yacigaba da shirinsa, dama JALAL ba amsawa zeyiba
“Barka da safiya Yaya Jawwad”
“Yawwa barka”
“Naga kana shirin fita abincinfa?”
“Nakoshi”
“Meyasa?”
Shiru yayi mata yasamu guri ya zauna yana kokarin daura agogonsa,
JALAL yana kallonsu bece musu uffan ba
kan hannun kujerar da Jawwad yake JALILA ta je zauna, tasaka hannu ta karbe agogon hannunsa
Dagowa yai yana kallonta, ba tareda ta kalleshi ba tace
“Gayamin meyasa yau bazakaci abincina ba? Laifin menayi maka?”
Y miko mata hannunsa tareda fadin
“Babu abinda kikayimin, ban agogona kar in makara”
janye hannunta tayi
“Ko shine yayi maka wani ABU?”
“Shiwa”
“Wancan” tafada tana nuna JALAL, gaskiya JALILA Yar rinin hankali ce
Jawwad yace “ba sunansa wancanba,”
“Yaya Jawwad na fuskanci ninayi maka laifi, Dan Allah kayi hakuri”
Dan kuramata ido Jawwad yayi, ta damu sosai
“Jalila me kikeso ayi yanzu?”
“Kaci abincin, sannan ka dinga kulani”
Murmushi Jawwad yayi Wanda seda hakoransa suka fito yanayin yadda tayi maganar ya birgeshi matuka
“Baby meyasa baki daga wayata ba jiya da daddare for more than 30 minutes wayarki busy”
“Yasalam Yaya Jawwad Hanan ce fa kasan gobe in Allah ya kaimu zasuzo, ita ta kirani taketa min surutu labarin makaranta, Gida, da sauransu, muna gamawa siyama ma takirani, naso in kuma kiranka, se nayi tunanin kayi bacci ne,
Amma tuba nake yayana bazan kumaba insha Allah”
“Baby bazan iya fushi dakeba Sam, kawo abincin”
Jalal ji yayi kaman yasamu bulala ya zanewa Jawwad jikinsa, saboda bacin rai dama akan wannan, shugabar marasa mutuncin yake ta wannan fushin gaskiya Jawwad Dan wahala ne
Tea Jalila ta hada masa ta zuba doya da miyan sos ta bawa Jawwad
“Nagode sisyna, amma kinsan mu biyune yaya Jalal fa, shima a bashi”
“Ya jira Ilham in tazo ta hada ta bashi,”
“Kai Baby, meyasa hakane nida Jalal dayane, indai zakiyiwa Jalal haka nima zaki iya yimin”
“A gurinka ne daya ni….. Bata gama maganar ba
Kamar yadda yai mata jiya yanzunma Jalal zuwa yayi ya kwace na hannun Jawwad yai tafiyarsa kan kujerar da ya taso
“Yaya kana kallonsa ko?”
“To Baby ya zanyi indai bazaki bashi Abinci ba abun akaina ze kare, nawa ze karba ya cinye”
Zuciya Jalila tayi ta mike tareda fadin
“Ai sekuyi tayi,”
Murmushi Jawwad yayi sannan ya kalli Jalal
“Bros meyasa ba kwa jituwa da baby ne, why”?
” saboda bazan iya wannan shirmen da rashin aikin yinba, kalli saboda abunda be taka kara ya karyaba kake ta fushi, na dauka wani abun akayi maka, Ashe saboda wannan uwar rashin kunyan ne, shirme kawai”
“Allah yabaka hakuri, amma bazaka ganeba Jalal”
“Ameen naji bazan ganeba din”

Jawwad yagama breakfast dinshi ya tashi ya shiga cikin Gida suka gaisa dasu Abba, sannan yacewa Halima Dan Allah in Jalila tagama abunda take ga dakinsa nan a temaka a gyara masa daga nan yai waje domin tafiya makaranta
Ilham da kanta ranar tayi breakfast, bata bari masu aiki sunyiba, dukda ba wata kwararriya bace a fannin girki, tagama tayi kwalliya ta kai part din Jalal amma baya nan ta ajiye masa takoma dakinta, har gurin karfe Tara ba Jalal babu alamarsa, se zarya take koya dawo amma bata ganshiba
Halima taje daki ta sanarwa da Jalila sakon Jawwad
Nana ta kalleta
“Aifa ke yanzu kin kade haka zasu maida ke kamar baiwarsu”
“Nana kenan meye abun bauta a ciki,?”
“Tab lallai aikuwa zasu rainaki, tun yanzuma gashi, ke zakiyi musu girki, ki gyara musu daki, agaisheki nikam bazan iya wannan wahalar ba”
Jalila tayi murmushi
“Nana kenan, meye a ciki, duk abunda nayiwa Yaya Jawwad ko wani Wanda ya rabeshi ban fadiba, kaina nayiwa”
“Hmm Allah ya temaka, kema wataran zaki gaji Dan matsalarsu bata karewa”
“Ai bazan gajiba Hajiya Nana, kema gara kisaba gaba akeji”
Jalila ta mike ta tafi gyarawa Jawwad daki, ta tarar Jalal yagama karyawa ya bar kwanukan a gurin, ko tartare kwanukan guri daya beyiba
Jalila ta kalleshi ta kalli gurin da
Jalal ya bata
“Mtsewww Dan Allah malam in an gama cin abinci hade kwanukan akeyi ba a cinye abincin ciki a bajesuba,”
Jalila tafada a fili tareda kwashe kwanukan tai cikin gida, kodaga kai beba Balle ya kalleta
Ilham tagaji da jiran da Jalal, tasan dai baze wuce gidansu Jalal ba Dan haka ta dau mayafi ta nufi gidansu Nana, tana zuwa part din Jawwad ta nufa, kaitsaye Dan tasan baze wuce nan ba tunda motarsa tana Gida, taje ta tura kofar palourn
Jalal ta hanga a zaune a kan carpet din palourn Jawwad, da remote a hannunsa, shiga tayi cikin palourn da sallama ya Dan dago ya kalleta, ta karasa shigowa cikin dakin
“Ina kwana Yaya Jalal”
“Lafiya kalau”
Ta Dan gyara zama, “Yaya na hada maka breakfast ne shine…..
” da can ke kike hadamin?”
“A a Yaya amma….
” tsaya dama ina son magana dake, me kika cewa yarinyar da tazo nemana jiya”?
“Ni kuma?”
“Akwai wata a gurin nan bayan ke?”
“To aini jiya ban hadu da kowa ba”
“Nima rainamin hankalin zakiyi”?
“A a Yaya Jalal ni ba wata wadda tazo nemanka damuka hadu”
“Ilham wallahi zan tattakaki,
Sa anki ne ni? Nace me kika cewa Hannah jiya, nizakiyiwa karya!!!”
Hade rai tayi itama dan bata gane inda rainin hankalin Jalal na yau ya dosa ba, ta mike tsaye ta kalleshi
“Ni ban San mezance maka ba kuma, nagayamaka abunda nasani ni ba wata wadda muka hadu jiya, kasake dai tambayarta”
“Ni kike gayawa haka?”
“To me kakeso ince?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button