Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Share please
More comments more typing………………………

Comments dinku nabani nishadi am proud of you masoyana masoya wannan littfi

????️????️????️????️????️

[8/31, 8:30 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE- 38

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

      -MY FIRST NOVEL-

Ransa ne ya kara baci ya kalli Ilham
“Ni kike kallo kike gayawa wannan maganar? Ke kinyimn laifi kuma ki tsaya kina gayamin magana, kuma uban wayasaki kika dagamin waya har kike zagin Wanda ya kirani? Kwana biyu kinga nayi sanyi shine kikemin rashin kunya ko?”
Mamakine yacika Ilham wannan wace kasurgumar makaryaciyar ce take mata sharri haka, to mema zatace masa ne
Maganar yaseera ce ta fado mata “kidena jin tsoransa”
“Au to kar in kare kaina, kana gayamin magana akan abunda bansan nayiba, sekuma inyi shiru wannan lokacin ya wuce Yaya Jalal nima nadena daga maka kafa ina kallonka kana min wulakanci, se wasu maganganu kake Wanda bangane inda suka dosaba, duk saboda kawai ina sonka, so fa ba karya bane ba, kuma ina nan akan bakana, duk macen datayi gangancin shigowa rayuwarmu senayi maganinta, ka dawo hayyacinka Dan ni……
Tas ya dauketa da mari, dafe inda ya mareta tayi, tana kallonsa
” ke kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama, kinje kinyimn karya, kina cewa wai ban isa inyi abunda ba kyaso ba ke a wa? Wani matsayi kika taka a gurina da kike da wannan ikon,”?
Sauke hannunta tayi daga kuncinta, ta kalli cikin kwayar idonsa
“Matsayin kanwarka kuma masoyiyarka na taka, ka gayawa ita wadda ta gaya maka hakan, ta tinkareni ni da ita tayimin, ba wai ta koma bayan fage ba, kuma wallahi daga yanzu kadena jibgata a banza kasawa zuciyarka bashi kakeci seka biya wannan abun da kakemin, kuma wallahi indai ina raye baka da wata mata in baniba seka aureni, baka da imani Jalal ko sau daya yakamata ka dubeni da idon rahama, kodayake kai babu tausayi a zuciyarka”
Kuma harzuka yayi,
“Ni kike gayawa haka, ke wace irin Jaka ce da ba kya ganewa ana so dolene, bana sonki kuma bazan taba sonki ba, Jahila kawai fita kibani guri kafin in sauya miki, kamanni, kinsanni sarai bana son hauka amma kullum ke haukanki kara yawa yake shiyasa ko shirginki bana shiga fita dallah”
Tundaga waje Jalila take jiyo hayaniyarsu Dan haka da sauri takarasa,
ILHAM ta kalleshi sannan tace
“Jalal duk haukan da yake kaina be kai Wanda yake kanka ba amma na dage nakesonka a haka wani irin mutum ne kai”
Wani Marin yakuma bata,.yana shirin karamata ne Jalila ta shigo da air freshener a hannunta, zata gyara dakin Jawwad ganin abunda yake faruwa yasata rugawa da sauri ta shiga tsakanin Jalal da Ilham, ta janye Ilham baya, sannan ta kalli Jalal
“Wannan abun kunya kake aikatawa karasa inda zaka zage kwanjinka se akan mace, macen ma kanwarka, me yake damunka haka”
Daka mata tsawa yayi
“Matsa ki bani guri ko in hada dake, in tattakaki”
Itakam Ilham gefe tayi tana maida numfashi saboda taji zafin marukan da yayi mata,
JALILA ta kalleshi up and down
“To ka tattakanin mana ragon maza, karasa inda zaka nuna karfinka sekan mace, in karfi kakeson nunawa seka tafi gaidan dambe, jarumin namiji bada zuciyarsa yake yanke hukunciba da kwakwalwarsa dakuma hikima yakeyi, ba wai jibgar mace ba”
Kallon JALILA yayi idonsa cikin nata yana nazarin meze mata
Ilham daga inda take tsaye sukaji tace
“Wallahi Yaya kowace tayimin wannan sharrin idona idonta kagaya mata senaga bayanta, kuma Marin dakayimin bashi ka dauka, don ka dauki alhakina, niba wadda muka hadu jiya amma ka hukuntani akan abunda bani nayiba, duk laifukan nan ba Wanda nasan nayi maka kowace karya tayimin,
Tayi nasara wannan karon nima ta saurari abunda zan mata koma wace munafukarce dani take zancen wallahi” ta karasa maganar tana hawaye, se yanzu JALILA tagane inda fadan nasu ya dosa, amma ta juyo ta kalli Ilham
“Kekam Iska na wahalar dame kayan kara, kalli tun ba yauba kike shan wahala a hannunsa ya dakeki, ya zageki, sekace ubanki kekuma dayake zuciyarki kin Yar kare ya cinye se manne masa kike kumayi, ni banga abun mannewa a gurin wannan abunba”
Tafada tana kallon Jalal, wani irin huci Jalal yakeyi, yama rasa me yakamata yayi,
“Ke saurara, ba ruwanki a cikin rayuwarmu, uwar shishshigi, kuma ma inda Sa hannunki acikin abunda yake yimin zan baki mamaki wallahi,”
Ta daga jajayen idanuwanta ta kalli Jalal
“Wallahi Jalal wahalar dani din nan dakake shekara da shekaru, wallahi se ka biya duk randa kazo hannuna seka zubar da hawaye fiye da Wanda na zubar, zan fito maka a ainihin Ilham dina babu daga kafa ko ragawa tsakanina da kai, koni ko kai kokuma duk wani munafiki dake shiga tsakaninmu”
Yinkurowa yayi zeyi kan Ilham, JALILA takuma shan gabansa
“Dan girman Allah ka kyaleta”
Hannu daya yasa, yai wurgi da Jalila daga gabansa tayi gefe
Ilham kuma ta tsaya kyam taki tafiya
Tas! Tas! Guda biyu a jere
“Dan kaunar da kakewa manzon Allah karka kuma dukanta, jininka cefa, kanwarka ce, indai so yana zama laifi, Ashe wataran zaka iya rabuwa da Jawwad”
Cak ya tsaya be juyoba amma
Jalila tacigaba da fadin
“Kome tayi maka kishinka ne yasa tayi, baka tunanin alhakinta yakamaka ne, at least kaima ka sota mana koda irin na yan uwantaka ne kalli yadda ta……………..
(Zancigaba da hakuri, har lokacin da burinmu ze cika akan JALAL da mahaifiyarsa)
Wannan kalaman da Jalila ta haba ji Ilham ta tabayi a wayane suka dawowa Jalila Wanda hakan yasa takasa karasa abunda tayi niyyar fada
Juyowa yayi ya nufo inda Jalila take, Ilham na ganin haka ta sulale ta gudu, yazo gaban Jalila ya tsaya
” meyasa ba kyajin maganane? Ke dole sekin gayamin me zanyi? Rayuwarki daban tawa daban, meyasa kike hakane, ke in dai baki shiga harkata ba ba kyajin dadi, meyasa ba kya ganewa ne, kinsan metayimin ne?
Ya karasa maganar cikin shouting, Dan ja da baya Jalila tayi kadan
“Eh nasani, nasan me tayi maka, kuma ba ita tayiba nice nan nayi”
Kallon Jalila yayi
“Kana mamakine? Ni ce nan matar tagani tace in kirawoka nace bazakazoba, ban damu da koma me tagaya makaba, saboda zatayi hakane dan tasa kamin wulakanci, Dan mace irin wannan dayawa maganganunsu karyane dakuma makirci, a zatonta nice Ilham shiyasa tagaya maka karya da gaskiya, abun kunyane a ganka da mace irin wannan,
Haba Dan Allah koba ka dena abunda kake Dan komaiba kabari Dan Allah, dakuma kare mutuncinka, abokananka dayawa, wasu suna karatu, wasu suna sana a, kowa na kokarin Gina rayuwarsa amma kai kullum kokarin wargaza taka kakeyi, kaji tsoron Allah kuma ka kiyayi matan bariki, wannan data zo gurinka kowa ya ganta yasan mutuniyar banzace, amma kalli abunda kayiwa kanwarka saboda ita, kukwana Gida daya Ku tashi amma baka da abokin gaba se ita dakuma mahaifiyarka Wanda hakan shine babban abun kunya, kayi tunani maana, kayi wani abu akan rayuwarka,”
Idanuwansa ne suka kuma yin ja, jijiyoyin kansa suka daddga, ya rintse ido kalaman Jalila na cigaba da dukan zuciyarsa, wani irin huci yake kaman kumurci, wani abu yake kokarin tunawa amma yakasa, sema jiyayi kansa yana jujjuyawa, bude idonsa yayi akan Jalila
Gabanta ne ya fadi! Ganin idon Jalal yana caccanza kala, daga Ja zuwa baki, gashi kuma ta kasa matsawa daga inda take,
“Fita ki bani guri, bana son irin wannan maganar, kifita nace!!!”
Ya dinga maganar cikin karaji daga baya kuma ya sulale, ya yanke jiki ya fadi
Tsorata Jalila tayi ta Dan ja da baya amma taga ko motsawa beyiba daga inda yake, a hankali ta tako tazo inda yake kwance, ta leka fuskarsa, taga idonsa a rufe amma fuskarsa tayi Ja sosai ga jijiyoyin kansa duk sun daga sun kumbura, sekuma hawaye da yake fita ta gefen idonsa, se sauke numfashi yaketayi hankali, a hankali ya Dan motsa yasa hannunsa biyu, ya danne kansa yana girgiza kan nasa
“Wai meyasameka?” Ta tambayeshi
Bece mata komaiba, sema numfashinsa da yake fita da sauri yanzu
“Yasalam na shigesu toni ya zanyi, kar ace wani abun nayi masa”
Ta kuma kallonsa “kanka ne yake maka ciwo?”
Shiru bece komaiba
Tarasa ma mezatayi, ko Yaya Jawwad zan kira a waya wata zuciyar tace A a karki daga masa hankali yanzu yana makaranta
Ruwa ta debo a kofi, ta karanta wasu ayoyi saga cikin al Qur’ani
Ta daga kofin ta Dan dinga zuba masa a kansa
A hankali numfashinsa yafara komawa normal, a hankali ya sauke hannunsa daga kansa, sekuma yafara bacci
“To ko aljanune da shi in ba hakaba ya za ayi idon mutum ya dinga canzawa”
Tashi tayi ta fara gyra inda yakamata a dakin tanata tunani kala² yana nan yanata bacci a gurin ta wuceshi ta fita ta Koma cikin Gida
Tana zuwa dakinsu Nana ta dubeta
“Kekam INA kika zauna haka tun dazu nake nemanki fa”
“Yaya Jawwad na gyarawa daki daga nan, na zauna a gurin flowers nayi tilawa”
“Hmm yayi kyau”
Daga nan JALILA ta bar dakin in bahakaba Nana zata cigaba da yimata tambayoyin Daba tasan dame zata bata amsa ba
Tunani ne yacika zuciyar JALILA to dama maza ma suna da Aljanu, Dan tafi kyautata zaton JALAL aljanu ne dashi,
Jalal kam bayan wani lokaci ya tashi daga baccin da yayi, ya mike yaje yayi wanka, ya koma kan gadon Jawwad ya kwanta abunda yafaru dazu yake tunawa, ji yayi zuciyarsa na kokarin fara bugawa da karfi Dan haka da sauri ya kauda tunanin daga zuciyarsa
Koda Jawwad ya dawo daga makaranta, ras ya Tarar da JALAL kaman ba abunda ya faru
Jalila kokari take ta kauda tunanin Jalal tayi harkokinta, takoma shirin karbar bakinta dazatayi, amma abu ya gagara abunda tagani yau tareda Jalal yau yabata mamaki, a hankali mafarkan da ta dingayi akansa a baya suke dawo mata kaman lokacin takeyi, yau Sam bata da nutsuwa kaman wata Mara lafiya haka take gudanar da
al amuranta na yau.
Hankalinta ya karkata akan son sanin waye Jalal dakuma son gano ainihin abunda ke ran Ilham game da son Jalal da ta keyi
Tayi nisa sosai a tunaninta Halima ta dafata
“Sayyada Jalila meyake damunki yau naga ba kya walwala, ko akwai matsala ne?”
Jalila ta danyi firgigit
“Leemart ba wani matsala,”
“Gaskiya ban yaddaba akwai abunda yake damunki”
“Kawai tunanin ummina nake”
“Allah sarki, ai kince tana zuwa sati me zuwa ki kwantar da hankalinki”
Murmushi Kawai Jalila tayi, suka cigaba da aikinsu
Da daddare Jalila ce ta kaimusu abinci amma taga Jalal normal kaman ba shiba, ko kallon inda take beba, balle ya kulata itama batasa akanta ze kulatanba amma se kallon mamaki take masa mussaman in ta tuna yadda idonsa ya dinga canza kala, ga kumburowa da jijiyoyin kansa suka dingayi
Jawwad ne ya dinga tsokanar Jalila wai duk murnar zatayi bakine yasa jikinta yayi sanyi haka ita dai sedai tayi murmushi kawai tai musu seda safe
Bayan sun gama cin Abinci ne Jalal ya tafi Gida Dan soyake ya kwanta da wuri bacci yakeji, yana kwanciya maganganun Jalila suka dinga dawo masa
Tashi yayi ya zauna, yai shiru ya Sa hannunsa a sumarsa ya rike yana Dan juya kansa a hankali
“Why meyasa nake aikata wannan abubuwan, meyasa bazan dena ba, nima banaso,”
Bugun zuciyarsa ne yafara karuwa yaji kansa yana kokarin fara juyawa
Da hanzari ya mike ya nufi fridge dinsa ya cika cikinsa da giya ya baje a gurin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button