ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Da safe Jawwad yaita zuba ido yaga Jalila ta kawo musu breakfast amma shiru, ga Jalal ma bezo ba daga karshe ma Halima ce ta kawo breakfast din, Jawwad ya tambayi Halima,
“Halima ina Jalila?”
“Tana cikin Gida”
“Meyasa bata kawo Abincin da kanta ba”?
“Wallahi bansaniba, kawai tacemin in kawo”
Ya gyada kai
“OK shikenan, Nagode”
Daga nan ya mike ya dau kayan Abincin zuwa gidansu Jalal dan yau be zoba,
Kamar yadda yai tsamanni, Jalal be tashi daga bacci ba, yana kwance a parlour, ko kayan jikinsa be canza ba, ga kwalaban giya da yasha da ragowar sigarin da ya zuke, Dan girgiza kai yai sannan ya tashi Jalal yasashi yai wanka yai sallar asuba,
Jawwad ya kalli Jalal
“Jalal baza kayiwa kanka fada ba ko? Lafiyarka fa Jalal, zasu iya yi maka illa”
Kallon Jawwad yayi ya sunkuyar da kai
“Jiya nayi iya kokarina kar in sha matar gidan nan tabata min rai, shiyasa na sha”
“Haba Dan uwa, in rai yabaci hankali baya gushewa, ka dinga hakuri, Mummy mahaifiyar kace, ka dinga hakuri da ita”
“Jawwad kasan komai Dan haka karka kuma batamin rai”
“Shikenan yi hakuri bari mu karya”
Jalila ta na gyara gadon su dan Nana ta tashi daga baccin ta shiga wanka, wayar Jalila ta fara ringing, tana dubawa taga Hanan setaga bata kyautaba bata kira Hanan tayi mata ya hanya ba, tasa hannu ta daga wayar
Hanan tace “Queen shine ko ki kirani kimin ya hanya ko?”
“Am sorry Hanan nakira Yaya Abdallah”
“Shi daban ni daban”
“To Allah yabaki hakuri”
“Ameen kin temaki kanki da kika bani hakuri, da baki banba ko hmmm”
“To ai ya wuce tunda nabada hakurin”
“To naji, yanzu dai ya Yaya Jawwad dina fatan ya tashi lafiya”
Jimm Jalila ta yi taki cewa komai
“Magana fa nake Jalila, nace ya Jawwad dina, kwana nayi ina mafarkinsa, yanamin wannan kasaitaccen murmushin, kaman inyi tsuntsuwa inzo in kuma ganinsa”
“Mhmmm” shine kawai abunda Jalila ta ce
“Tunda bazaki gayamin ya yake ba shikenan, ni nakirashi inji, ya Jalal dinki”?
“Jalal dina kuma?”
“Eh mana, tunda bazaki gayamin ya, Jawwad Dina ba, se in tambayeki ya Jalal, tunda bakya iya danne kishinki queen”
Dan dabarbarcewa Jalila tayi
“Kin fiye shirme Hanan, wane irin kishi, ya Mummy da Yaya Abdallah”
“Ya kike kokarin canza maganar ne, anyway kowa lafiya, hau what’s app kiga status dina”
“To naji, saura inga shirme”
Hanan ta yi dariya
“Koma dai meye zaki gani”
Jalila ta bude what’s app dinta taga Hanan ta turomata messages, ta bude hotunan dasukayine, hotunan sunyi kyau, tana duba dp din Hanan taga hoton Hanan da Jawwad, gashi be iya hade raiba, yayi murmushi, sunyi kyau shida Hanan, Jalila ji tayi kaman ta buga wayar da kasa
Dagaske kishin Yaya Jawwad nake, “yasalam” status din Hanan ta bude hotunan ne dai akan status din nanma ta rubuta kalaman soyayya, akan hotunanta da Jawwad
“Wai dagaske Hanan Yaya Jawwad takeso ko wasa, Hanan karkimin haka mana”
Tana kuma shiga daya hoton setaga hotonta da Jalal, wanda hanan tasata tai dariyar dole, shikuma Jalal yana kallonta Hanan ta rubuta
“perfect Match, Jalal and Jalila”
“Kutmelesi baki da hankali, kinci kai Hanan, Allah yayi min tsari, da mutum irin Jalal,”
Ta turawa Hanan daga nan ta rufe data dinta ta kashe wayar gaba daya
Sakkowa ta yi ta karasa gyaran gadon
Sannan tabar dakin gaskiyar Hanan Jalila kishi take, tarasa meyake mata dadi, harabar gidan ta fito, tana son ganin Jawwad, yau ba ta kaimasa abinci ba rabon data ganshi tun jiya da su Hanan suka tafi,
“Maybe ma Hanan ta kirashi suna shan soyayyarsu” wata zuciyar ta raya mata, tsaki Jalila tayi a fili, tarasa abunyi, kawai ta shiga gayaran flowers din harabar gidan, lokaci² tana tsaki
Abba ne ya fito ze fita yaganta tana gyaran flours, yayi murmushi yakarasa inda take yace
“Barka da safiya, yarinyar kirki, da kanki kike gyaran flowers din”
Murmushi ta yi
“Abba barka da fitowa”
“Yawwa Yar albarka, dakanki kike wannan, akin nasaka a nemo wani megadin daze dinga kulada flowers din”
“Abba dan dai gyaran flowers ai ba wuya koni se indingayi”
“A a baza ayi hakaba inkika fara zuwa school fa, wannan ba aikinki bane,
Yawwa munyi waya da umminki, tacemin tana nan tafe next week insha Allah, zatayi tafiyar nan”
“To Abba nima tagayamin,”
“Masha Allah, Allah yakawo mana ita lafiya”
“Ameen Abba”
Abba ya kalleta
“Ina fatan ba wata matsala zamanki a gidan nan ko”?
” babu wata Matsala Abba”
“Masha Allah, in akwai wani abu dai kimin magana”
“To Abba, Adawo lafiya”
“Allah yasa Jalila”
Daga haka Abba ya shiga motarsa ya fita
Bayan sun gama breakfast Jawwad ya kalli Jalal yace
“Am going”
“Where?” Jalal ya tambayeshi
“Gida mana ina son ganin Baby, naga kaman tana fushi dani, tun jiya ban kuma ganintaba, yauma ba ita ta kawo min Abinci ba”
Jalal ya mike kafa ba tareda ya kalli Jawwad ba yace
“Laifin me kamata, zatayi fushi?”
“Nima bansaniba Jalal, zan tambayeta dai, na damu da rashin ganinta”
Tsaki Jalal yayi
“Kafiye abun Haushi,”
“Eh naji, nikam se an nima”
“A sauka lafiya”
Daga haka Jawwad ya tafi Gida a harabar gidan ya Tarar da Jalila ta na gyaran flowers, tabawa gate bata, dan haka batasan ya shigo ba, a hankali ya karasa inda take, juyowa tayi kawai tai tozali da Jawwad, seda ta dan tsorata
Murmushi yayi mata “matsoraciya ga idonki, am sorry nabaki tsoro ko”
Murmushi itama tayi masa ta girgiza kai, kallonsa take ta tuna maganar Hanan
“Kwana nayi ina mafarkinsa yanamin wannan murmushin”
Dan hade rai Jalila ta yi, wata zuciyar ta ce mata “wata kilama sunyi ways da Hanan” kara bata rai tayi,
Karasowa yayi daf da ita ya kalleta
“Baby laifin menayi miki hakane, kike hademin rai, yau duk bana jin dadi ban gankiba”
Rasa me zatace masa tayi dan kuwa babu laifin da yayi mata
“Yayana bakayimin laifin komaiba”
“Are u sure, naga kina fushi dani”
“Bazan iya fushi da kaiba”
“To shikenan kin tashi lafiya”?
” lafiya kalau,?
“Meyasa baki kawomin Abinci ba yau”? dan sunkuyar da kai tayi kasa
“Bakomai”
Maama ce tafito zata fita unguwa ta gansu tare, kallonsu ta yi ta dauke kai, Jawwad yace “Maama fita zakiyi?”
“Ka aikeni ne?”
“A a Maama a dawo lafiya”
Ta amsa da “Allah yasa”
Jalila ma tace “Adawo lafiya”
Kallon Jalila tayi ta dauke kai, taje ta bude motarta, ta shige tai waje,
Jawwad ya dawo da kallonsa kan Jalila
“Baby me yake damunkine naga baki da walwala tun jiya?”
Rasa mezatace tayi kawai setace masa
“Yaya Jawwad, meyasa abokinka bashida kirki? Jiya munje gidansu da daddare Mummy tanata kuka saboda shi Yaya ka dinga yi masa nasiha, ni a ganina tarayarka dashi bata da amfani”
Dan kurawa Jalila ido yayi na wasu sakanni, ya dan sunkuyar da kai sannan ya kuma kallon ta
“Jalila” ya kira sunanta
“Na am Yaya Jawwad” ya mike tsaye sannan yace mata
“Biyoni”
Ba musu ta bi bayansa, har palournsa sannan ya nuna mata guri ta zauna
“Jalila rabuwata da Jalal ba mafita baneba, ina tareda shima kalli halin da yake ciki, inaga inna rabu dashi, babu wasu abokan arziki a rayuwarsa kowa yayiwa dansa kashedi akan mu amala dashi, babu wasu mutanen kirki da yake rayuwa dasu, ko ransa ya baci sune mutanen da suke tarairayarsa, kowa yana kyamarsa shiyasa abune mawuyaci ya rabu da shaye² indai mutanen kirki sukayi karanci a rayuwarsa”
“To Yaya meyasa bazaka masa fada ba ya canza rayuwarsa haka yaga kowa yana yi, babban abun damuwar yadda yake treating mahaifiyarsa, Sam be dace ba” Jawwad yayi ajiyar zuciya
“Abunda yake tsakanin Jalal da mahaifiyarsa sirrine na rayuwarsa, amma dai a da mutumin arziki ne, bahaka yake ba, wani azzalumin aboki ya hadu dashi waishi Jeje shine silar lalacewar Jalal nayi iya kokarina ya rabu dashi, amma yaki, akwai wani mummunan kuduri da Jeje yake dashi akan Jalal Wanda ni kaina ban saniba, yanzu ga wata shedaniyar yarinya data shigo rayuwarsa, wadda nake kyautata zaton bakinsu daya da Jejen wai ita Hannah”
Dan dagowa JALILA tai ta kalleshi “Hannah kuma?”
“Eh Hannah, ta shigo rayuwar Jalal, iatama, Jalal kaman Wanda akayiwa asiri, gashi cutar dashi suke amma baze iya rabuwa dasuba, duk lokacin da nayi yinkurin yi masa nasiha, idan yayi kaman ze dauka seya birkicemin ya dingamin tsawa jijiyoyin kansa su kumbura, wani lokacin seya suma, shiyasa na barwa Allah komai nake masa addu a”
Shiru Jalila tayi wato Jawwad yasan Jalal yana wannan abun
Jawwad yabata labarin nan a dukunkune bata wani gane komaiba amma waye Jeje she needs to know him
Jawwad ya kuma dubanta
“Yana daga abunda yasa bazan iya rabuwa da Jalal ba halaccin mahaifinsa Jalila bayan Abba da Abee, daddyn Jalal yana cikin mutanene daba zan mantaba,Jalal ya kaunaceni tun ina dan talaka na, Jalilalokacin ina zuwa gidansu Jala, y’an fashi suka shigo gidan da daddare, tashin hankalin daddyn Jalal karsu yimin wani abu da sukaga haka se sukai kokarin harbina, Jalal ya taremin harbi, aka sameshi a memakona, Jalal seda yayi jinya a kasar waje, badan ya tureni ba ya tsaya.dani zasu samu “
Zare ido Jalila ta yi, ya gyada mata kai
“Da gaske Baby, idan nafara gaya miki halaccin da yayi min dayawa, dan haka idan na gujeshi nayi butulci, naci amanar kauna da soyayya da yayi min, kitayani yi masa addu a komai ze zama dai² insha Allah”
Nannauyar Ajiyar zuciya Jalila tayi “zan dinga yi masa addu a insha Allah”
“Yawwa baby in kakayi haka kingama min komai”
Daga nan JALILA ta tashi ta koma cikin Gida
Tunani ya hadu yayi mata yawa, Yaya Jawwad be bayyana mata komai sosai ba, yagayamata abubuwan a takaice kuma a dukunkune, ko wazata tambaya
Yana da kyau tasan waye Jejen nan, amma to kuma meya kawo Hannah cikin lamarin nan akwai kanshin bakinsu daya da Jeje kenan
“Kai JALILA karki bari kwakwalwarki tayi bindiga mana kin takurawa kanki akan wannan sha³ dabe masa ciwon Kansa ba mutumin da giyarsa tafiye masa komai inyi rayuwata mana, haka Jalila ta cigaba da takura kanta, seta dena wannan tunanin son sanin waye Jalal”