ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ilham ta gayyaci kawayenta gurin birthday din Yayanta kuma masoyinta wato Jalal, se wani rawar kai take tana shirye2, ta gayyaci su yaseera da sauran kawayenta, se shiri takeyi, taje sabon gari ta sha kitso, tayi booking din make up, hatta shigar da zatayi sabon kaya ta siya.
Jalila ma nata shirin takeyi, saboda mugayen mafarkan da take da Jalal, dan haka da shirinta, zataje gurin birthday din nan, tanason tayi taka tsan2 sosai a gurin nan dan ita sam bata yadda da wannan birthday dinba, tana so taga suwaye abokan Jalal ne, mussaman Jeje, dakuma wasu abubuwa da take shirin yi a gurin, tanason tabattar wa Ilham Jalal baya gabanta, Bangaren Jeje ma shidasu hannah da abokan shaye2 sun shirya tsaf domin gudanar da mummunan kudirinsu akan ABDUL JALAL.
Ranar juma a da daddare, wanda yakama jajibir din birthday din Jalal, Jalila ta tafi Dakin Jawwad domin tana son magana dashi, tai sa a kuwa shikadai ta tarar a palourn, taje tasamu guri ta zauna, Jawwad ya kalleta”Babyn Yaya Jawwad, ya akayine?”
“gurin Yaya nazo” “to Yar gidan Yaya, ina jinki”
“Yaya Jawwad , gaskiya abokinka tunda mutane masu hankali zasuje gurin nan, dan Allah ka kaishi a rage mai gashin kansa, sannan kar kabari yasaka sarkan nan dayake sakawa sekace wani kare, ga wan….. Kai tsaye ba sallama sukaga Jalal ya shigo, hade rai Jalila tayi” a dai dinga yin sallama” banza Jalal yai mata, ya kalli Jawwad “kai gurinka nazo” Jawwad yace”ai gani, Allah yasa lafiya” wayar Jawwad tafara ringing “excuse me bari in amsa waya” yadaga wayar yasaka a kunnensa tareda yin sallama “Assalam Alaikum”
Muryar Hanan Jalila taji “wa alaikum salam barka da yamma Taurarona fatan kana lafiya?”
“lafiya kalau Hanan, ya gida, yasu Abdallah da daddy?” “suna lafiya, nice dai bani da lafiya” “yasalam meyasameki” “kewarka mana, itace take damuna, yanzu yaya queen take, naga kwana biyu haushina takeji” “tana lafiya, yanz… Juyawa yayi da nufin yabawa Jalila wayar, yaga Jalila ta cika ta batse, ta hade rai sosai, fasa bata wayar yayi, yace
” Queen dinki tana lafiya” “Masha Allah ina sirikata Nana, kodayake ita muna waya, dan Allah Yaya Jawwad yaushe zakuzo Kaduna ne, inaso inkuma ganinka, kullum senayi mafarkinka fa” Jalal dake gefe ya kalli fuskar Jalila kawai ya kwashe da dariya ganin yadda ta hade rai, Jalal ya tashi ya fita daga palourn, yana kuma yin dariya, ba karamin kyau Jalal yakeba idan yana dariya, Jawwad seda ya sha jinin jikinsa yakuma kallon Jalila, muryar Hanan ya kuma ji “my Haidar bakace komai ba, dan Allah yaushe zakuzo?” mikewa Jalila tayi ta fice daga palourn dan bazata iya cigaba da jin wannan hirar ba, ashe Hanan dagaske take son Jawwad tajeyi, kishi ya lullube Jalila ta fito ko ganin gabanta batayi, tazo fita taga Jalal a tsaye, a kofar fita, shiru tayi ba ta cemasa komaiba ya kalleta, yadda ta hade rai, tuntsurewa yakumayi da dariya, “kinji abunda Ilham takeji ko? Kinji yadda takeji idan taga kinamin shishshigi ko?, are u jealous of your brother” wani mugun harar tayi masa “ni matsa in wuce” Jalal yace”in naki fa? Ji yadda kike wani hade rai” sekuma ya hade rai kaman bashi yake dariyar nan ba yace “to bari in gayamiki, dakaina zan dauki Jawwad in kaiwa Hanan, ubanme Jawwad zeyi dake gaki mummuna gaki kwaila, se tsabar iyashege da rashin kunya da kikasa a gaba, ni zan tsayawa Hanan seta auri Jawwad, in yaso kije kinemi me tsautsayin daze aureki, wanda ze iya tolerating wannan nonsense din naki, sokuwa kawai, wuce ki ban guri” murguda masa baki tayi, tazo zata wuce ya kuma rufe hanyar, ya kalleta
“Kashedina dake na karshe, gobe in Allah ya kaimu kika sake na ganki gurin birthday na, duk abunda ya sameki kekika jawa kanki, idankuma kinkiji kinje gurin, idan kika sake kikayi wannan karambani a gurin, shima kome ya biyo baya ke kika sani,”
Cikin bacin rai tace” waini kadai ka tsana zakace bazanje ba, wallahi senaje, sedai in baza ayi ba, kuma wallahi niba mummuna bace ba, Mummuna tana gidanku wato Ilham” kallonta ya kumayi tsaf, sama da kasa, be kuma cemata komai ba, yabata hanya ta wuce, tana tafe tana mita, harta je dakinsu, Nana ta kalleta “lafiya dai, naganki kina fushi hada mita” “Ke rabu dani ba komai”
Sallar isha i tayi ko Abincin dare bataciba, tanemi guri ta kwanta, banda kishi da bacin rai ba abunda yake damunta, “haba Hanan yazaki min haka, meyasa kikeson Jawwad din, kema ina sonki, zan iya sadaukar miki da komai nawa da kikeso, saboda kaunar da nakemiki, amma banda yaya Jawwad dina” haka taita juye2 da kyar bacci ya dauketa
Jalal yana tsaye se fara a yakeyi, ga wani katon cake ???? agaban sa, ga mutane nata hada2 Hannah ta yanka cake ta dakko tasaka masa a baki, cake din na shiga bakinsa yazama baki, jini yafara zuba daga bakinsa ya fadi a gurin, da gudu Jalila ta karasa ta kifar da tebur din da cake din kafin ta juyo ba kowa a gurin daga ita se Jalal, ta tafi tana lekawa taga koda wanda ze temaka mata ya dauki jalal a kaishi Asibiti tana dawowa taga, Ilham ta shake Jalal tana kokarin kasheshi
“Subhanallah!!!” ta furta da karfi
Share please,
More Comments More typing………………………….
????️????️????️????️????️????️????️
[9/28, 8:10 PM] Ayshercool: ????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
_ABDUL JALAL_
_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)
PAGE- 52
PART 1
_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what’s app akan wannan lambar wayar
07063065680
_My First Novel _
A firgice ta mike zaune tana waige2, Nana ta tashi zaune itama, “lafiya Jalila, meyasaki ihu haka” Jalila ta hada zufa, se haki take hannu tasa ta dafe kanta “bakomai Nana, yi hakuri na tasheki, kwanta abunki, na dan tsorata ne kawai” “to shikenan, ki kwanta kema, darene sosai yanzu” “to zan kwanta” Nana ta cigaba da baccinta, yayinda bacci ya kauracewa idon Jalila, se tunani da yacika mata zuciya, da taga baccin ya gagareta, ummi ce ta fado mata a rai, dan tasan da ummi na nan da yanzu tana sallar dare, tashi tayi itama taje ta dauro alwala ta tada salla, tayi addu a sosai wanda galibin addu’ar ta ta, tana fatan Allah ya bayyana mata Ummi, dakuma fatan Allah ya shiryi Jalal, ya bata nasara akan makiyansa, a haka tasamu bacci yakuna daukanta.
Yau Saturday yakama ranar birthday din ABDUL JALAL, shirye shiryensu suke yayinda Jalila banda aikin tunani ba abunda takeyi, Jawwad ma a wani bangaren ya damu ganin yadda Jalila kishinta ya fito karara a fuskarta, duk ya damu gashi ya kira layinta amma a kashe, gashi yana tsoron ummi dayaje da kansa gurinta.
Ilham se shiri take kaman wadda zata biki tun safe take hada2, tana waya da kawayenta akan yadda abun ze kasance,
Abun duniya duk ya ishi Jalila dan haka ta dau mayafinta ta fita, se azahar ta dawo, ba wanda tagayawa ina taje, tana dawowa ta hadu da Jawwad a harabar gidan, yaji dadin ganinta sedai besan mezece mata ba yana ganin har yanzu tana fushi dashi,
“Baby daga ina haka da ranan nan?” fuskarta a sake tace masa
“Yaya na dan fitane, ai ban dade da fita ba”
“to shikenan kidena yawo a rana, kar kanki yayi ciwo, bazan so hakan ba” murmushi Jalila tayi
“to Yaya, amma kaima ai naga a ranar zaka fita, kaima bazanso kanka yayi ciwo ba ai”
“Baby dolene yasa zan fita ai”
“Amma ranar da zafi fa” ta fada a shagwabe, dariya yamata “zaki fara rigima ko” tuno wayar da sukayi da hanan jiya tayi, nan da nan taji ba dadi, ranta ya baci dan haka ta wuce cikin gida ta barshi a gurin.
Jeje yanata jadaddawa Hannah, karta bari a samu matsala akan aikin dazasu gabatar yau akan Jalal babbar dama ce suka samu, karta bari ta kubu cemusu.
Allah ya temaki Jawwad ya lallaba Jalal ya kaishi aka rage masa sumar kansa, anyi masa gyaran fuska yayi kyau sosai, amma shi Jalal se mita yake wai Jawwad yasa an masa aski an maida shi mummuna, bayan sun dawo daga gurin askin ne suka hadu da Nana da Jalila a hanya sunje sunyo siyayya suka dakkosu, Jawwad yace “in anjima tare zamu tafine kokuma yaya?”
Jalila tai farat tace “A a tafiyarku daban tamu daban”
Jawwad yace “meyasa?”
“bakomai amma bazamu tafi daku ba, ka dau abokinka ku tafi, dan bana son mita da korafi” “Wane me mitar da kuma me korafin” “nidai ban kama suna ba” dariya Nana tayi
“hmm Allah ya shirya Baby Jalila”
“Ameen” duk abubuwan nan da takeyi karfin haline, dan ji take duk jikinta yayi sanyi,
Bayan sallar magariba, Ilham ta shirya tsaf, ta dawo daga gurin make up, tayi kyau ba laifi abunka da farar mace ga kwala2 idanuwa inji Hanan, dogon wando tasaka baki, da
t shirt blue wadda tazo har cinyarta, kanta ya sha kitson attach, ta dakko dan karamin bakin mayafi tasaka akanta, wrist watch dinta ma baki ne ga wani takalmi me uban tsini shima baki, se dan karamin jakarta data rataya, tayi kyau matuka, ta fito palour ta tarar da mummy, mummy tana ganinta tai murmushi
“Masha Allah, uwargidan Jalal kinyi kyau fa” murmushi Ilham tayi “Mummy har kinsa naji dadi wallahi”
“se tafiya” “eh mummy tafiya zanyi” “to a dawo lafiya, kikula da kanki” “to mummy, ki bani key din” mummy ta mikomata key din mota tace gashi nan “ayi tuki a hankali” Ilham ta karbi key ta fita
Nana ma tayi kyau ba karamin haduwa tayi ba, dan ita high west tasaka baki da jan body hook se ta kawo mayafi tayi rolling din kanta dashi,
Har Nana ta gama shiri Jalila bata da niyyar ta shi ta shirya tayi wankanta tsaf amma ta nemi guri ta zauna, seda Nana ta fara mita sannan ta tashi, Nana tasata a gaba tayi mata light make up, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki Jalila ta tashi ta dakko wata doguwar riga purple wadda ta sha adon duwatsu, ta taje gashinta tasaka masa ribbon, kasancewar kanta ba dan kwali, gashin gaban kanta me laushi irin na fulani ya kwanta kai dagani kasan kan akwai gashi, ta dauki mayafin rigar ta dora akanta, Nana tai murmushi “fa tubarakallahu ahsanil khalikin, wallahi Jalila kinyi kyau sekace y’ar sudan, dressing din ya miki kyau” “ke rufamin asiri, wani irin larabawa ana zaman lafiya, da an cuci larabawa” “amma kinsan fulani koba mu kai larabawa ba da kyanmu” “ji wani cika baki ina kyan anan” dariya Nana tayi “ni karasa shiryawa mutafi” Jalila ta dau Jakarta purple, se takalmi me tudu. Tayi kyau kaikace wata yar hamshakin attajiri ce. Suka jero suka fito
Maama ta kallesu, sedai hassada amma ita kanta tasan Jalila ba laifi tayi gadon dangin mahaifinta sosai a kyau, kamanta daya da babanta, mahaifiyarta ma ba baya ba wajen kyau, Nana ma ba laifi tana ds kyau amma sam bata kai Jalila ba
“har kunfito?” “eh Maama zamu tafi” Nana ta bata amsa “to Allah ya kiyaye, kar kuyi dare ku dawo da wuri” Jalila tace Insha Allah ” suna fitowa harabar gidan Driver su yake jira, suka bude mota suka shiga, suna tafe Nana tana ta musu hotuna, ana zuwa wani guri Jalila tace a tsaya zata karbi sako, ta fita ta karbo sakon tabude boot ta saka, sannan ta dawo mota tace a tafi, Nana tace” mekika karbone? “
” abune “” abu wane iri”
“kinji mace kin aikenine?” “a a ban aikeki ba jarababbiya” “eh naji jarababbiya” haka suka tafi suna fada
Suna zuwa gurin Nana ta bude mota ta fita yayinda Jalila ta kame a cikin mota taki fita
“fito mana” “yi gaba zan taho” Nana ta wuce cikin gurin.
Abunda ya daurewa Jeje kai be wuce ganin yan uwan Jalal dake ta zuwa ba, dukda matasane amma abun ya bashi mamaki, dole sukara shiri su saka ido sosai, saboda kar a samu matsala. koda Nana ta tafi Jalila tacewa driver
“manu dan Allah karkayi nisa akwai ajiyata a cikin motar nan anjima kadan zanzo in dauka”
“karkiji komai Uwadakina, ina nan ina jiranku harku gama”
Jalila ta bude motar ta fito seda ta karewa harabar gurin kallo, taga yanayin mutanen dasuke shiga suna fita, mutanen kirki dana banza, wasu daga cikin wanda tagani suna kama da mummy dan haka ta tabattar yan uwan su Jalal ne, dama Jalal sunada yan uwa haka, amma basa zuwa gidansu Jalal, gakuma yan iskan abokansa nan wanda da gani base an gayamaka ba kasan yan giya ne, kowa se hada2 yake, a hankali ta bude jakarta ta dakko katon glass baki tasa a idonta, tafara wannan tafiyarta ta me daukan hankali, hall din ya hadu yana da girma, kaikace biki ake ba birthday ba, an kawata gurin matuka guri ta samu a gefe ita ka dai ta zauna a wata kujera tana kallon kowa one by one, ta hangi table din da Ilham take ita da kawayenta su yaseera da wasu yan uwansu, se hotuna suke suna dariya, Hannah ta hango tasha kananan kaya tana up and down cikin maza ko kunya bataji, murmushi Jalila tayi a ranta tace “yakamata hanna su san juna itada Ilham” tanata kalle kallenta wani matashi yazo ya zauna a kujerar kusada Jalila, “sannu yan mata” banza tayi masa tama kara dauke kanta
“haba yazaki dauke kai haka, nazone in tayaki hira kawai kafin a fara, naga ke kadaice” juyowa tayi “to cemaka nayi na damu senayi hira da wanine” gani tayi yana dan kaama da Jalal, hakan yasa ta gane dan uwansane
“to in bakyason hirar ni inaso, muryarki da dadi gaskiya, gashi kinyimin kyau sosai” shiru takuma yi masa
Hannah ce tazo wucewa taji anata Ilham, da sauri ta dan tsaya ta juyo, amma setaga ba wadda take tunani bace, “may be sunan ne dai yazo daya”
Jalila gani tai wannan gayen ya cika mata kunne da surutu, dan haka ta mike ta bashi guri ta tafi gurin Nana, ta ajiyewa Nana jakarta “Nana ina zuwa dan Allah” daga haka ta tafi dan nesa dasu Ilham, Hannah ce takuma dawowa taji Ilham tana “kai wai ina yaya Jalal ya tsaya haka, by now yaci ace anfara fa, Yaya Jalal kenan, zuma seda wuta” Hannah tsayawa tayi cak ta dan dawo da baya tace
“dan Allah kece Ilham, kanwar Jalal fa” Ilham ta mata kallon up and down “yeah nice, kanwarsa kuma matar daze aura” Hannah tace “anya kuwa, last time kaman ba dake muka haduba”
“ke wai meye haka zakizo kinamin tambayoyi hakane, ke wace niban taba ganinki ba se yau, meye hakane”
“Hannah manyan mata, kuma me da’awar soyayya a gurin ABDUL JALAL, gaskiyarki wannan itace Ilham ba niba” Jalila tasa hannu ta cire glass din fuskar ta,
“yes itace Ilham nikuma Jalila” gaba daya suka tsaya suna kallon Jalila, suka ma rasa abun cewa
“dama ya dace kusan juna, Ilham ga Hannah, Hannah ga Ilham yanzu kusan juna, so u should count me out of your troubles, Ilham, Hanna, niba budurwar Jalal bace, bani da lokacin da zan bata akan soyayya da wani Jalal, dan haka idan kuna abunku to ku cire Jalila a ciki” tana gama fadin haka tai tafiyarta ta kyalesu, kallon kallo aka shigayi tsakanin Hannah da Ilham, wani shu’umin murmushi Hannah tayi, Ilham tace “ashe kece Hannah, ni na dauka zanga wata hamshakiyar mace meji da kanta, ashe ma karyar bariki ce kawai” Hannah ma tayi wata shu umar dariya sannan tace “ashe kece opponent dina ba waccan ba, thank God kece, bazam sha wahala ba, da waccan me siffar aljanunce da sena damu, dan ba karamin daukar hankali zatayi ba, amama me ban daukeki cikakkiyar mace ba ma balle in damu kaina, dan dake da namiji ba ku da banbanci” taana gama fadar haka ta wuce tabar Ilham,
Jalila kam tafita harabar gurin, tana waige2, tana tsaye taji ance Jeje da sauri ta waiga, tana ganinsa taga yaci sunan nasa jeje kai kace wani kasurgumin arne ne, gajeren wandone a jikinsa, da riga amless duk damtsensa a waje sekace dan dambe, gashi ya tara suma duk yamata kala, haka wani dan gemunsa shima ya samasa wannan kalar, ga katon sarka a wuyansa, lebensa baki kirin kaman gawayi, idonsa jawur, jeje ne ya tsaya suna gaisawa da wasu abokansu, muryarsa ba dadin ji, muryarsa a bude take, kai da kaji kasan kasurgumin dan shaye2 ne, ajiyar zuciya Jalila tayi tace “No wonder, wannan ko kisan kai akace yayi bazatayi musu ba” tana shirin komawa cikin hall din taga Hannah ta fito ta tafi inda yake, suka tsaya suna maganganu, Jalila bata iya jiyo me suke cewa, sun jima suna magana sannan taga Hanna ta koma cikin hall din, Jalila ma komawa tayi cikin hall din, tana zuwa taga an shirya high table cakes sun kai biyar manya2 kuma kala2, ga wasu manyan kwalabe, gurin Nana ta koma ta zauna, Nana na tayi mata mita ta cika yawo, ita dai tai mata shiru. da Jalila ta bada fuska da samarin da zatayi a gurin dayawa daga na kirkin har na kwarai, kowa se kawomata farmaki yake, ita kuma ta tsare gida, ta hade rai ba raini, suna nan zaune aka sanar da karasowar Jalal, mutumin naku ya hadu, suka shigo shida Jawwad kaman twins, sedai Jalal yafi Jawwad murdewa sosai, kuma shi Jawwad kalar ustazaine, shikuma Jalal kaman wrestler, yau anci sa’a da fara’arsa ya shigo, Jeje ji yayi kaman yai tsuntsuwa yaje ya shake Jawwad, ganinsu tare, ba karamin bata masa rai yayiba, gaba daya hall din ya dauki tafi, ana shewa cikin takunsa na kasaita yaje har kan stage din ihu aka dingayi ana masa tafi, akaita daukarsa a hotuna, MC yace to kafin Jalal ya yanka cake za a dan shakata tukuna. Nan aka shiga cashewa maza da mata ana watsin kudi a gurin.
Jalila dai na zaune tana kallon stage din amma tunaninta baya kan me akeyi kamar an mintsineta ta waiga, tana waigawa tayi tozali da Jeje ido hudu sukayi da ita, kwata2 bashi da kyan gani a idon Jalila, se yanzu ta lura da zanen tatoo a damtsensa na hagu da kuma gefen wuyansa, harda pink dasu blue a kalolin gashin kan Jeje, wai yanzu wannan ne abokin Jalal, gaban Jeje ne yayi mummunar faduwa da yaga Jalila, kallon kallo suka shigayi, ko kyafta ido ba yayi akanta, haka nan yaji be yadda da itaba musamman dayaga kallon da take masa, amma fa yarinyar ta hadu iya wuya, komai yaji a jikinta, idanun nan nata ma kawai sun isa daukar hankali, wayarsa ce tafara ringing ya kalli wayar ya kalli Jalila ya juya ya fita, yana fita Jalila ta rufamasa baya, harabar gurin ya fita Jalila tana binsa a baya, dan nesa kadan ta tsaya daga inda yake
“Hello oga KB, ina nan nasaka ido komai ze tafi yadda ya dace, nasaka ido akan komai, kuma Hannah ma tana lure da komai, yanzu dai fatanmu yafara cin cake din nan, zakaji Labari me dadi a daren nan” Jeje na gama wayar ya juyo yayi tozali da Jalila a tsaye kyam tana kallonsa, wani murmushi yayi na rikakkun yan iskan duniya
“Hi beb what are you looking for?” shiru tayi ta cigaba da kallonsa
“kinada damuwa ne, can i help you? “
“u have nothing to help me with” jin muryarta ba karamin burgeshi tayi ba “wow muryarki da dadin sauraro”
“Kai dakata, am not here to listen to your useless and dramatic words, am here for a porpose, waye kai meye hadinka da ABDUL JALAL kakeson cutar da rayuwarsa”
Kallon tsaf yayi mata, sannan yafara takowa a hankali gabanta yace “Kekuma wacece? Haba beauty why trying to involve your self in this case, gaki little baby with beautiful body, baki dace da shiga rigimar manya ba da babu ruwanki”
“na fuskanci kai karamin dan iska ne kai kake mun kallon yarinya, bari kaji ingayamaka ni bana fadar abu idan zanyi sedai kaganshi a aikace, wallahi indai da raina sena ga bayanka daga kai har wanda ya tsaya maka” hade rai Jeje yayi “da farko na dauka abun naki wasane, meyasa kikeson shiga abunda babu ruwanki, a kaf dangin Jalal ban sanki ba, meye hadinki dashi da kikeson kare rayuwarsa, kekin isa ki rusa shirin da aka dade anayi kusan shekaru goma sha biyar ke awa, kodai kina sonshi ne? Baki dace dashiba da irina kika dace musaki a harka ba karamin wuta zakiyi ba a duniyarmu ta manyan yara, da ina ganin kaman da Ilham zan tafi, amma kinfita haduwa”
“Ni a mutum, duniyar ku ta dabbobi dai, marasa amfani, and i will show you what am capable of doing, wallahi sena rusa shirunku ko shekara dubu kukayi kunayi, Allah ya tsayamin muzuba mugani, sha3 dan asara, Allah yayi min tsari da kai, banza whalalle mara imani, ni ba son Jalal nakeba ina tausayin rayuwarsa ne da iyayensa, zanbaka mamaki, ka tsaya kagani a yau base gobe ba zan fara nuna maka, waceni useless and hopeless creature” ta juya tai tafiyarta,