ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

“Tun dazu na shigo kina kallo amma kin tsaya kina surutu a waya kin barni ina zaman jiranki kuma kinsam gurinki Nazo”
“Wayar da nake ne surutun JALAL?”
Tafada tana kallonsa
“Munyi waya da megidan nan dazu yace in gaya miki yana dawowa jibi”
yafada a takaice batare daya bata amsan tambayrta ba, inba hakaba yanzu zata fara masa fada Takara masa wani takaicin, kuma shi a rayuwarsa ya tasani fada.
Ilham datake kitchen taga shigowarsa Dan haka ta aje abinda takeyi ta dakko juice da cup ta dorosu a tray ta fito palour tana yauki ta nufi India Jalal yake
Cikin iyayi tafara magana
“Yayana ga juice na kawo maka”
Bece komai ba sema Kafeta da yayi da ido ko kiftawa ba yayi
Nan ta sha jinin jikinta saboda kallon da yakemata
“Mtsewwwww” yaja wani dogon tsaki ya mike ze bar palourn
“Haba Jalal meyasa kake hakane? Ilham fa kanwarkace koba komai ai yakamata ka karba kasha” mummy tayi maganar adan hasale
Ko takansu be biba seda yaje bakin kofa ya tsaya batare da ya waiwayo ba
“Yace in gayamiki jirgin karfe hudu ze biyo” (yana nufin mahaifinsa)
Yayi gaba abinsa
“Na shiga uku mummy meyasa Yaya Jalal yakemin haka kwata² bana gabansa mommy kiyi wani abu Dan Allah wallahi ina son Yayana amma ni meyasa baya sona”
Ilham takarasa maganar cikin sheshsheka kuka
Rungumota mommy tayi tana rarrashi
“kiyi hakuri Ilham ina iya kokarina ni kaina fama nake Jalal kinagani ina mahaifiyarshi amma ban isheshi komai ba
Amma in dai ina raye Jalal bashi da wata matar inba keba insha Allah”
Aikuwa daga ranar da burina yacika kingama yawo mummy dan sekinyi kuka da hawayenki Dan ba lefi bane in anmaka abinda kayi tafada a ranta amma a zahiri kuma secewa tayi
“Allah yasa mummy kitemaka min burina yacika in mallakeshi Dan Allah wallahi in ba shiba bazan iya auren kowaba”
“Karki damu Ilham keda Jalal duk abu dayane a gurina insha Allah zanyi duk meyiwuwa inga kin auri Jalal”
“Nagode sosai mommyna inkikamin haka kingamamin komai”
Wai ni Jalal yarinyar nan take cewa innayi zuciya indena kula yayanta saboda muna da banbancin tarbiyya
Zanyi maganinta ai rana dubu ta barawo daya tak itace tame kaya zan kamata a hannu
Haka yayi ta wannan zancen zucin
Bayan kwana daya
Gidansu Jalal suka tashi da aikace² saboda shirin dawowar magidan,
sedai aikin yayiwa mummyn da Ilham yawa saboda me aikinta ta tafi kauyensu za ai bikin yayarta ga Ilham da shegen son jiki.
Dan haka mummy ta Yanke shawarar kiran maama a waya tace Dan Allah tabata Aron su Jalila su tayata aikin dan yayi musu yawa,
kimanin wata hudu kenan rabon mahaifin Jalal da Nigeria Dan haka dole ayi shiri na mussaman domin tarbarsa.
A waya ta kira maama ta sanarda ita Dan Allah inba abinda su Jalila suke ta turo su tayata aiki ayyukan dayawa
Itakuma tace zata turomatasu
Dakinsu mama taje ta sanar dasu sakon mummyn Jalal
Nanace tace
“To maama zamuje insha Allah”
Itakuwa Jalila cikinta ne yayi wata kara me sauti kuuuuuuuu!!!
“Na shiga uku ni Jalila !!?
” me yafaru ne Jalila?” Nana ta fada tana kallon Jalila
“Au tambayata ma kikeyi yanzu in Jalal ya ganni fa? Yanzu ni yazanyi”
“Tab yanzu meye abunyi ainamanta da kinmasa rashin M,
shiyasa nace miki ba ruwanki dashi Jalila yanzu ga irinta nan”
(Nikuwa nace hmm danma bakomai kikasani ba jiyama tamasa rashin kunya” Jalila sarkin rawar kai da shishshigi)
“Kinga ni ba wannan ba ko ince kawai bani da lafiya? Se in zamana base naje ba”
“Kai Jalila wannan ba shawara bace yanzu fa Maama ta shigo ta ganki ras dake sannan kice baki da lafiya wannan ba shawara bace Sam”
“To ya zanyi? Inkuma muka hadu fa ?”
“Bazaku haduba insha Allah kitsaya a waje in leka in baya nan seki shigo”
“To amma nikam ina jin tsoro Nana”
“Ba abinda ze faru insha Allah, kwantar da hankalinki taso mu tafi”
A kofar Gida Jalila ta tsaya tana waige² itakuma Nana ta shiga domin dubawa in Jalal yana nan minti uku Sega Nana ta fito ta kalli JALILA ta girgizamata kai
“Shigo baya nan”
“Kin tabbata”?
“eh na tabbata banganshi a ciki ba,
Hmm waike dama kinsan kina jin tsoro amma kika tsokano shi”
“Ke ni matsa in wuce tun kafin ya dawo ya ganni anan” Jalila tafada a gaggauce
Tare suka shiga cikin gidan Jalila tana ta faman rarraba ido
A palour suka ci karo da Ilham rike kwanuka zata shiga kitchen, bata kula suba tai shigewarta batace musu komaiba ta shige kitchen ta ajiye kwanukan sannan ta fito sewani shan kanshi take tana hura hanci
“Waike Ilham har yanzu abinda yafaru be wuceba a gurinki kike ta wani kallonmu kina hade rai
Indai Jalila CE ita tamanta ma kunyi kiyi hakuri Dan Allah”
Jalila kuwa a ranta cewa tayi
Tab lallai aiki yaganki indai nice bana gani inyi shiru
“Hmm bakomai ya wuce kuzo mukarasa mummyn tana ciki”
Suka bita gaba daya wani part suka nufa Wanda tunda Jalila tazo a rufe take ganinsa tana kyautata zaton shine part din mahaifin Jalal
Shigarsu yayi dai² da fitowar mummyn dauke da labulaye a hannunta, Nana daga inda suke ta Dan rusuna ta gaisheta ita Kuwa Jalila seda ta durkusa har kaasa, sannan ta gaisheta, fuskarta a sake ta amsamusu
Har cikin ranta taji inama Jalal din tane haka yake girmamata
Karasawa Jalila tayi gurin mummy ta karbi kayan hannunta
“mummy kawo ina za akaisu?”
“Dama wasu za a canza wannan zan badasu wanki biyoni seki karbo wasu a canza tace to”
Juyowar nan dazatayi taganshi zaune akan kujera, alamu ya dade a gurin itace bata lura dashi ba
Nana kuwa tun shigowarsu taganshi a zaune amma ta lura JALILA ba ta Ganshi ba,
Be dago ya kalleta ba seda mummy tayi gaba tabiyo bayanta, sannan yayi mata kallon zamu gauraya dake
Itakuwa kallon up and down tayi masa hada murguda baki tayi sauri tabi bayan mummy
Akajima Jalila ta dawo da labulaye a hannunta suka fara gyaran part din yana zaune beje ko ina ba
” mummy tace Nana da Ilham suzo su siyo abinda babu saboda girki tunda taga Jalila tafisu rashin son jiki”
“Mummy indai Jalilace intaga dama batajin aiki “
“Ainima naga alama Nana”
ILHAM da Nana suka tafi cefane yai saura Jalal, Mummy, se Jalila
Mummy ce take kokarin Jan wata durowa na litattafai amma takasa,
Jalila tazo ta tayata amma suka kasa,
Takaici ya ishi Jalila ganin ga JALAL a zaune amma yakasa temakawa tsaki taja
“Mtsewww mummy wannan Dan naki bashi da amfani Sam wallahi yana kallo muna fama amma ko a jikinsa”
“India JALAL ne kadan kika gani bari in dakko bagco a rage litattafan mugani ko zamu iya janye durowan”
Ita Jalila a hankali tayi maganar batai zaton yajiba,
Sedai kawai gani tai yana kallonta
Mummy na Barin dakin,
ya tashi ya tako har gabanta yana muzurai yana mata wani irin kallo, yana zuwa gabanta yatsaya yadan kura mata ido
Nan da nan jikinta ya dau rawa
“Mara tarbiyya, Mara amfani, mutumin banza, mekama da yan daba, Dan shaye² Niko?” Yanuna kansa da yatsansa
“To bari ingaya miki wani abu ba tsoronki nakeji ba Dana kkyaleki ban kakkaryaki ba,
bana son in batawa Dan uwana rai sedai kawai zan maidake Irina ne, shize tabbatar miki bani da tarbiyya kinga in mukazama mu biyu semunfi dadin kwatance
Sha³ Jahila kawai dakikiya na tsani ganin ko fuskarki”
Ya juya da nufin yafita yabar dakin
” duk jahilcina nasan girman iyayenaa kuma inazuwa makarantar islamiyya,
a islamiyyarmu ma nasan akwai ukuba game sabawa iyaye tundaga duniya, dukda Jahilcina bana zuwa mashaya ina girmama manyana, kaga sekanemi waye jahili”
Yana jinta kalamanta suna dukan zuciyarsa amma ya fice ya kyaleta da sannu ze maganinta.
Haka sukayita aiki har yamma tayi suka shirya girke² suka gyara ko ina Wanda yakasance Jalila ce karfin aikin
"Karfe hudu da rabi dai² Jawwad da Jalal sukaje airport suka dakko Alhaji Habib Kamal,
mahaifin Jalal ya karaso gidansa cike da farincikin ganin tilon dansa cikin koshin lafiya, dukda yawan korafin da mahaifiyar D`an nasa kanyi masa game da miyagun halayen yaron nasu.