ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Hannah ma abun yabata mamaki ya akayi, Jalal da suka bugar da kwaya ya akayi ya iya barin gurin nan, waye da wannan aikin haka, kuma taga tafiyar Jawwad shida Nana, ba bu Jalal, to ya akayi lamarin nan yazo a haka, ya akayi Jalal yabar gurin partyn nan ba wanda ya ganshi.
Ilham ma bacci ya gagareta, kwana tayi kuka da tunani, da tufka da warwara akan me zatayiwa Jalila da Hannah ta huce, nan ta kudurce wani mugun abu a zuciyarta.
Washe gari da safe, Jawwad yakoma gurin Jalal, amma Jalal ko tashi beba yana kwance yanata fama da bacci, ya gwada tashin Jalal amma still be tashi ba yanata fama da bacci, Jawwad ya tabbatar da Jalal ba karamin buguwa yayi ba.
Jawwad ya koma gida yakira manu direba suka gaisa sannan yace masa “manu ya akayi ka kawo Jalal gida jiya ban saniba”?
“nima Jalila ce ta sani na dakko shi an bashi giya ya sha, wani yana gadinsa, shine tace zata dauke hankalin me gadinnasa, nikuma in dauke shi, in kaishi gida” Jawwad yai ajiyar zuciya yace “to shikenan nagode” daga nan ya tafi
Jeje ya kudurce wa ransa cewar ko da yaya se ya gano, wace ce yarinyar nan kuma seya gano ya akayi Jalal yabar gurin nan ba tareda kowa yasani ba, tabbas idan hasashensa ya tabatta itace to tasaka kanta a cikin mummunan hatsari, dan seta karbi hukuncin Jalal.
Seda la’asar sannan Jalal ya tashi daga baccin da yakeyi, Jawwad yasa shi a gaba da kyar yai salloli, sannan ya tafi dashi gidansu ya bashi abinci yaci, Jalal yace “Jawwad ya akayi muka dawo jiya”?
“Kai zan tambaya, me yasa kasha giya jiya?”
“ai kadan na sha bansan zan bugu haka ba”
“kai kasani, seda namaka kashedi amma saboda taurin kai seda kasha”
Banza Jalal yai masa yacigaba da cin Abincin sa
Jeje ne yake ta masifa “Hannah wane irin hauka ne wannan, mun shirya komai amma kin bari komai ya tafi a banza, saboda tsabar shirme irin naki wannan wane irin haukane, kinsa oga KB yacimin mutunci jiya hada marina, wane irin sakarcine haka, meyasa ba kya abu da tunani” cikin tsawa tace
“Kai dakata, ka iya bakinka wallahi, karka sake ka zageni ka tuna da wadda kake magana Hannah ce, baka isa ka zageni akan wani banzan oganka ba, ai nayi iya abunda nace zan iya ko, to dan haka nagama nawa daga jiya, nagama yimuku aiki, tunda damar ta subuce muku, yanzu kaina zanyiwa aiki, zannemi soyayyar Jalal ta gaskiya dan duk Dunia babu namjin da yayimin sama da shi, dan haka zan tuba auren Jalal zanyi, bayan na tabattar danayi maganin wannan banzar kanwartasa, sannan in Gano wacece wannan hatsabibiyar yarinyar, dan in har da ita nasan Jalal baze aureni ba”
A fusace yace
“Hanna kidawo hayyacinki, tawaye zakiyimin, kinsan dagani harke ba tsira zamuyi daga sharrin oga KB ba muddin asirinmu ya tonu”
“Kai ta shafa kuma wannan, dan daga kai har ogannanka ban daukeku tsiyar komai ba, bari inkuma tuna maka dawa kake magana, Hannah ce duk hatsabibancin da kukeji dashi na fiku wallahi”
Tirkashi!!!!
Share please
More Comments More typing…………………………
Laifin dadi karewa anan na kawo muku karshen littafin ABDUL JALAL (2020) kashi na daya, zan dan huta na takaitaccen lokaci domin cigaba da kawo muku wannan littafi, ina godiya da yadda kuka jure bibiyata sannu a hankali a wannan littafi n farko, yanzuma ku biyoni a hankali, domin warware muku kulle kulle, da tarin tambayoyin da suke cikin wannan littafi
Yan group din ABDUL JALAL NOVEL FANS masoya wannan littafi wanda nasani da wanda bansaniba masu turomin sakkoni da addu’oi ina alfahari daku inakumabkaunarku nima, dukda kasancewar shi littafina na farko amma kuna bibiyata kuna bani kwarin gwiwa nagode kwarai masoya na da yan uwana ina matukar godiya
Se mun hade a littafi na biyu, taku har kullum Aisha humaira (daddy’s girl)
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a tuntubeni a ta what’s app akan wannan lambar
????️????️????️????️????️????️