ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

            _MY FIRST NOVEL _

Tunda suka doshi gidansu Jalal gaban Jalila ke wata irin mummunar faduwa ta dinga karanta duk abunda yazo bakinta, suna tun karar kofar da zata sadar da kai da cikin gidan gabanta na cigaba da faduwa kirjinta se bugawa yake da karfin gaske.
Anty ce tafara sa hannu ta murda handle din suka shiga a babban parlour suka zaunar da Jalila, Hajiya Salma ta kira daddy a waya tasanar masa sun iso amma basu ga kowa a parlour ba, da yake daddy ya koma, dan haka ya kira Mummy a waya yace taje parlour tana da baki.
Abun ya bata mamaki sosai, wani irin bakine haka da bazasu kirata ba, fitowa tayi ba tareda tayi tsamanni ba tayi karo dasu Hajiya Salma a zaune a palour, rabon da taga hajiya Salma tun lokacin da ta bar mata gidan, Salma tana nan da gayun ta ba kace ta haifi Mahmud ba.

A fusace Mummy ta dube su a wulakance tace “lafiya daga ina? Mekuka zo yimin?”
Hajiya Salma tace “kwantar da hankalinki mana Hajiya khadija, ba abun zafi bane ba, Matar danki muka kawo miki, ki musu Addu’a ki sa musu Albarka zamu kaita gidan danki”
Wani tsinannen Kallo Mummy taiwa Hajiya Salma tace “Albarkata ake nema a wannan Auren munafuncin, da kuka haďa kai kuka aura masa yarinya ba da izinina ba, shine zakuzo wani wai im sa muku Albarka, bazasu taba samun Albarkata ba, saboda bana son yarinyar nan, na tsaneta tun kafin ta Auri ďana take juya shi, abunda takeso shi zeyi danme zan kaunace ta? Auren nan baze taba Albarka ba, kuma wallahi sena ga bayansa, senaga bayan Auren nan “

Anty tace
“Allah sarki, abunda kike gudune se ya faru, sannan Jalila taimakawa Ďanki take, kin san ba dan mutunci da girmamawa ba, Baza’a dauki nutsatsiyar yarinya abawa ďanki ba”

“tunda ansan ba nutsatsen bane, uban meyasa a lika masa wannaan yarinyar, se a kyaleshi da halinsa in aura masa yarinyar da nake so, wallahi bazan taba son yarinyar nan ba, da nake mata kallon mutuniyar kirki amma tunda tafara bin dana nagane makira ce mara mutunci “

Rirrike Hajiya Salma Jalila tayi ta kara sautin kukanta, Hajiya Salma tace
” ko ki sota ko karki sota Allah ya riga ya haďa Auren nan, zuwa yanzu yaci ace kinyi laushi kinyi hankali amma babu alamar hakan a tare dake, Allah shaida ne ba abunda yarinyar nan ta miki da ta cancanci wannan kiyayyar da mugun bakin daga gareki”

“kinga sauraramin bana son salon munafurci, nafada bana sonta, kuma bazasu taba ganin haske ko albarka a rayuwar Auren nan ba, kuma wallahi sena kashe Auren, babu wani alkhairi ko amfani da take da shi a gurin Jalal, wannan dunkiyar tasa kawai take kwadayi, shiyasa ta aureshi ta juyamin shi, to wallahi bata isa ba, tunda nina haifi ďana, shida abunda ya mallaka nawane, muddin ta shiga gidan Jalal tafara kirga ranakun bakinciki a rayuwar ta har seta kyalemin ďana, shegiyar yarinya mara usuli”

Tunda ake fadawa Jalila rashin mutuncin Mummy bata taba zaton ya kai haka ba, wata hira da suka tabayi da halima ta fado mata rai da halima take ce mata “Sayyada karki bari wani abu ya hadoki da matar nan dan bata da mutunci” sosai Jalila miyagun maganganun Mummy suka daki zuciyarta.

Hajiya Salma tace “Shikenan mungode da wannan karbar da kikayi mana muda matar ďanki, Amma ki sani idan kin rabani da gidan mijina kin zauna lafiya, bazan taba bari ki lalata auren nan ba, Allah yafi ki sannan a wannan karon dai2 nake dake, Aure an riga anyi shi kuma mutuwa ce zata raba shi”

“Se ayi in gani ai”

Anty tace “Jalila tashi mu tafi”
Jalila ta mike wani irin jiri na kwasarta, se rarrashinta Anty take,
Ilham ce ta shigo palourn da alama daga wani gurin take, wani kallon banza Ilham tayiwa su Hajiya Salma kafin idonta ya dira akan Jalila, dukda Jalila tana cikin lafaya, amma Jalila tayi kyau, jikinta yayi sumul sosai ga wani kamshi da dakin yake yi, hannunta ya sha kunshi ja da baki.

Ilham na ganin ta wani azababben kishi ya taso mata, gurin Jalila ta nufa gadan2 idonta ya rufe gaba daya tace

“Wallahi bazan taba yafe miki ba, kin rabani da ďan uwana abunda na dade ina so shekara da shekaru, wallahi zakigane baki da wayo, munafuka kece me cewa babu abunda zakiyi dashi, kinsha kiransa namiji mara daraja, mara tarbiyya da yake makirace kika zagaya kika Aureshi, algunguma…. Sosai Ilham take kuka tana kokarin fizgo Jalila

Hajiya Salma a fusace ta sa Jalila a bayanta tace “Ke lafiya meya haka?”

“ban saniba wallahi sena yi mata rashin mutunci, seta gane ni ba kanwar lasa bace, naga ta yadda zatayi zaman Auren a kwanciyar hankali”
Jalila tasa hannu ta ďaga lifayarta ta kalli Ilham ido duk hawaye, ga idanunta sunyi jawur, kallon da Jalila tayi mata seda gabanta ya fadi yadda taga Jalila ta hade rai tana mata wani irin kallo.

Sunkuyar da kai Jalila tayi ta cigaba da zubda Hawaye, Jan hannun Jalila su Anty sukayi suka fice waje.

Anty tace “Anty Salma su dangin su khadija tun asalinsu basu da mutunci, masifa acikinsu kamar barkono”

Hajiya Salma tace “Allah dai ya kyauta, ki kwantar da hankalinki Jalila komai ze wuce Insha Allah”

Suka sa Jalila a mota zuwa gidan ABDUL JALAL.

Dukda kan Jalila na cikin mayafi amma gidan ya tsaru sosai, suka kaita daki suka ajiyeta, akaita mata nasihohi, daga nan suka tafi suka barta a gidan, sakkowa tayi daga kan gadon ta nemi guri ta zauna a kasa, tana tuno irin maganganun cin mutuncin da Mummy ta dingayi mata da wulakanci, take taji mugun danasanin Wannan Auren yakara rufeta, Hawaye kawai takeyi, Mummy ta riga tayi mummunan furuci akan Auren nan, dama gashi bata tabaccin shi kansa Jalal din yana sonta, ga Ilham ma miyagun maganganun da ta dinga faďa, shikenan ni kowa na raba nazama abar kyama, Allah ka yafemin in wani laifin na aikata.

Har wajen goma na dare sannan Jalal ya shigo gidan, milk din yadine a jikinsa me laushi, da hula akansa, dakin da aka kai Jalila ya nufa dauke da ledoji a hannunsa, yana shiga ya tarar tayi zaman dirshan a kasa tanata zubar da Hawaye, dan tsayawa yayi yana kallinta dan be san ta ina ze fara ba, a hankali ya karasa gabanta, tana jinsa amma ta share ta cigaba da kukanta, ya sa hannunsa ze janye nata daga dukunkunewar da tayi a mayafi, da sauri ta janye hannunta ta ja da baya sekace taga dodo.

“Wai kukan me kikeyi hakane? Ke kullum duk inda kika zauna sedai kiyi kuka ne?”

Kallon shi tayi da rinannun idanuwanta cikin kuka tace “dole kace haka mana, me ya ragemun a rayuwa inji dadi banda kukan? Ka gayamin me ya ragemin? Mahaifiyarka bata sona, bata kauna ta, kaima kasan hakan amma ka Aureni, mahaifiyarka tace; bazata taba kaunata ba, seta kashe Auren nan, kasan da haka amma ka Aureni, anata kwallo da rayuwata daga nan zuwa can, dana fita daga wannan matsalar in fada wannan, zamana da kai nasan wani sabon shafin kaddarar ne, dan Allah ka sakeni in auri wanda yak sona, wanda mahaifiyarsa zatayi farinciki da shigata rayuwarsa,”

Shiru Jalal yayi ya tsura mata ido yana kokarin gano ko har cikin zuciyarta take maganar nan, mikewa yayi ya juya ya fice yabar ďakin zuciyarsa a cunkushe.

Daya bedroom din ya nufa, yana shiga ya sauya kaya, ya ajiye wayoyinsa ya nemi guri ya kwanta, tunani daban2 ya ziyarci zuciyarsa, Kenan Mummy ciwa Jalila mutunci tayi? Shiyasa tun farko be so akaita gurin ta ba, ga shi ta bata komai, Amma ta wata fuskar Jalila tanada gaskiya, babu wanda ya tuntubeta aka yanke mata wannan hukuncin, aka daura mata Aure ba tareda Amincewarta ba, shikenan wannan zaman ze yi a rayuwar Aurensa? Zuwa yaushe Jalila zata yadda da shi a matsayin miji? Haka ya dinga tunani abun duniya yabi ya isheshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button