ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Yana fita Jalila ma ta cigaba da kukan, karshe a zaune a kasan nan tayi bacci, ko kayan jikinta bata canja ba.

Koda gari ya waye bata bi ta kansa ba, tai sallar asuba tai kwanciyar ta, ta cigaba da baccin ta, lokaci2 idan ta tuna yadda Mummy ta dinga cin mutuncin ta se taji gaba daya haushin Jalal ya kamata, dan me ze yadda da Auren ta bayan ya san maman sa bata so, gaba ďaya Mummy ta gama kwashewa Auren nan Albarka, yunwa ce ta ishi Jalila dan haka ta tashi tai brush tai wanka, ta dauki ledar da ya shigo da ita jiya, ta bude kajine a ciki gasassu, se fresh milk, ko warming dinsu batayi ba ta ci abunta ta kora da madara, ta cigaba da zaman ďaki.
Tun ranar da’aka kawota da Jalal ya shigo bata kara ganinsa ba. A kayanta akwai tarkacen biscuit su ta cigaba da ci, kusan kwana biyar bata kuma haduwa da Jalal ba, da safe tayi wanka ta sa kaya ta fito, tana dan zazzagawa tana fitowa main palourn ta ci karo da katon hotonta da nashi, Hajiya Salma ta sa sukayi, an rubuta Happy marriage life, hoton yayi kyau sosai, ďan tabe baki tayi ta cigaba da za gayawa, gida yayi kyau masha Allah, Amma kwata2 takasa farinciki da hakan, saboda bacin rai da yake cin zuciyarta.

Koda ta duba store Jalal ya aje komai na kayan Amfani, hatta omon wanki akwai, duk abunda yasan na amfanine kona kayan masarufi ya ajiyeshi, fitowa tayi ta fita harabar gidan tana kuma kallo, katuwar haraba ce sosai, tana zagayawa ne ta fara jin kaurin sigari, tunkarar inda take jin kaurin tayi, tana zuwa ta tarar Jalal yanata zukawa cikinsa, yana fesar da hayakin a iska, ta dade a tsaye a gurin be sani ba, kamar an taba shi kawai ya juyo, yaci karo da ita a tsaye tana kallon sa

Jikinsa yayi sanyi da irin kallon da Jalila ke masa, amma ya basar ya cigaba da shan tabarsa, juyawa tayi ta koma cikin gidan ba tareda tace masa uffan ba.

Kusan sati biyu da tarewar Jalila amma ko maganar kirki bata haďata da Jalal, Abun ya damu Jalal matuka, be taba zaton Jalila zatayi watsi da shi haka ba, girki ma batayi, se yunwa ta addabeta zata hada cornflakes ta sha, gashi mafi yawan lokutanta tana karar dasu a kuka se bacci wani lokacin, ya damu sosai da wannan hali da takeyi.
Ko yayi niyyar yi mata magana idan yaga fuskarta da yadda take basar da shi se jikinsa yayi sanyu.

YauDa Asuba da Jalila ta idar da sallah tana zaune akan dadduma ya shigo dakinta, bata ce masa uffan ba, yasa hannu a Aljihu ya dakko sabuwar waya ya ajemata akan side bed, ya dakko kudi ya ajiye mata, sannan yace “ga kudin mota nan kikoma makaranta, ni zan wuce lagos”
Dagowa tayi ta kalleshi, ta kalli inda ya aje kudin

“wai nika dai zan dinga kwana a gidan nan? Gaskiya ni bazan iya kwana ni kadai ba tsoro nakeji”

“to ya kikeso ayi?” ya tambayeta

“Sedai in koma gida in zauna, in dinga tafiya school din a can”
Wani mugun kallo ya mata
“ba inda zakije, daga makaranta ban yadda kije ko ina ba”

“to Amma nifa bazan iya kwana ni ka dai ba, inajin tsoro”

Cikin ko in kula yace “se kisan yadda zakiyi, ni yau zan koma” ya fice ya barmata dakin

Haushine ya isheta, ta yaya zata iya kwana a gidan nan ita ka dai? Zuwa tayi tai wanka tafara shirin makaranta hankalin ta ya kai kan wayar daya ajiye mata, sabuwar wayar daya ajiye mata, dauka tayi ta kunna ta, komai nakan waccan wayar tata yana nan, da lambobinta, amma ya canza mata layi.
Ajiye wayar tayi ta gama shirinta ta tafi makaranta.

Tunda taje take shan tambayoyi daga gurin ‘yan ajinsu akan dagaske tayi Aure?
Haka ta dinga basu amsa dai2 da tambayoyinsu,’ yan jin kwaf kuwa sukace tunda basuje bikinta ba zasu kawo mata ziyara har gida.

Koda ta dawo gida ta tarar baya nan, ya tafi, da ranan ma tsoro takeji, tasaba ko yaya tana jin motsinsa, tun kan magariba ta kulle ko ina ta koma daki ta rurrufe ko ina ta sa key, Tana sallar Isha’i ko Abinci bata ciba ta haye gado ta lullube tana rarraba ido, sam takasa bacci.

Shima sam Jalal yakasa bacci, yana ta tunanin ko yaya zatayi? Ko tayi bacci oho? Tunani yayi ko ya kirata ne, amma ya tuna a halin da suke shida ita dan haka ya fasa kiranta dan karma ta bata masa rai.

Jalila kam bacci da kyar tayi shi, cike da tsoro, ko yaya taji faduwar abu zata firgita ta tashi. Alla2 ta dingayi gari ya waye saboda tsoro, gari na wayewa take shiryawa ta tafi school.

Wasa2 Jalal seda yayi sati biyu bata kuma jin duriyarsa ba, gashi ita ba lambarsa ce da ita ba, inma tana da lambarsa ta kirashi tace masa me? Amma tasan shida ya canza mata waya yana da lambarta, Amma be iya kiranta yaji wani hali take ciki.

Seta kunna karatun qur’ani a speakun palourn ta take iya bacci, yanzuma tana kudundune a gado ta dau wayarta ta kunna data, taga Hanan ta mata magana ta what’s App, chatting suka dingayi can Hanan takirata a waya suka cigaba da hira

Hanan tace “ke by now kamata yayi a ce kina tareda mijinki, Amma kina nan kina chatting”

“ke meya hana kije ki kula da naki mijin?” Jalila ta bata amsa

Hanan tace “Wallahi ya fita siyomin cashew ne”

“cashew kuma a daren nan?”

“Eh mana, ba mijina bane”?

Jalila tace “haba Hanan, ya kike garamin ďan uwane, dare fa yayi zaki tura shi siyan cashew”

“to ya zanyi, wallahi nakasa cin Abinci ne, shi nake son sha”

Jalila tace “hmm kodai kodai abunne?”

Hanan tace “au to ku zamu tsaya jira, kifara saimana feeder da pampers”

Jalila tace “wow masha Allah, Allah ya in ganta”

Hana ta amsa da “Ameen, ke kije ki kula da mijinmi seda safe”

Jalila tace “wai wane miji? Yana lagos fa”

Hanan tace
“dan yana lagos bazaki kula da shiba, keep him busy, kuyita chat kina zuba masa kalamai har yayi bacci”

Dan guntun tsaki Jalila tayi.
Hanan tace “Jalila kaddai har yanzu ba kwa jituwa? Jalila me yasa?”

“Hanan babu wani Alkhairi a wannan Auren namu, Hanan mahaifiyarsa tacimin mutunci fiya da yadda kike tunani, wallahi jin gidan nake kaman kurkuku”

“Haba Jalila, to Jalal ne yayi miki? Meye laifinsa anan, wannan Auren iyaye ne suka hada shi ba Jalal ba, yakamata ki tausaya masa Jalila, ranar suna video call da Haidar ya rame sosai, wallahi ina tunanin bashida lafiya ma, sedai kinsan ba lallai ya fada ba, saboda zurfin cikinsa, in Allah ya dubi niyyarki akan sa seya temake ki, mijinki ne Aljannarki zaki nema, shi wanda kike tunanin kina so din sekiga ba shine Alkhairi ba, kiyi tunani ya zakiji idan ninakewa Haidar abunda kikewa Jalal? ” shiru Jalila tayi, Hanan tace

” yakamata kiyi tunani, Jalal mutum ne shima, wannan shareshin da kikeyi ze iya jefa shi halaka fiye da baya, kuma zakiji kunya idan dangin mahaifinsa da suka yadda dake suka gano irin zaman da kike da ďansu, ke hatta Abba bazeji dadi ba”

Haka Hanan ta cigaba da da yiwa Jalila nasiha, sukayi sallama ta kwanta, shiru tayi tana nazarin maganganun Hanan, da kyar tayi bacci tanata tunani, Hanan ta ce mata ya rame kaman bashida lafiya, Ta danyi Ajiyar zuciya, a haka har bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari yakama Friday, da wuri ta shirya dan ta wuce makaranta, Amma tana fitowa parlour da uwar safiyan nan kawai taga Jalal a parlour, ta tsorata sosai, shigowar dare yayi, dan haka bata san ya dawo ba, ya ďaga kai ya kalleta, ya sunkuyar da kansa ya cigaba da abunda yake, ba tareda ya kalleta ba, Jalal ya rame sosai ta bakin Hanan kaman bashida lafiya, bredi yake ci babu ko tea se lemo me sanyi da yake sha, yana ci yana bata rai, gaba daya tausayinsa ya kamata, Amma yadda yayi kaman be ganta ba yasa itama tai wuce shi a parlour tai ficewarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button