ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Koda taje makaranta tunanin ne yake damunsa ya hanata sukuni, dukda yau juma’a se karfe biyar ta gama lectures.
Da ta koma gida motarsa tana harabar gidan, da sauri ta shiga cikin gidan amma baya palour kamar yadda tasaba in ta dawo tana tarar da shi a parlour, ko baze kulata ba, kullum yana zaune a palour seta dawo yake barin palourn ya shiga wasu sabgogin, Amma yau baya nan, mazewa tayi taje ta watsa ruwa, ta shiga ayyukanta Amma hankalin ta yana kan rashin ganin gilmawar Jalal, wasa2 har dare yayi amma bata ganshi ba, ta sa kayan bacci ta kwanta taji zuciyarta takasa nutsuwa.
Dan haka Mikewa tayi tasa hijjabinta ta nufi dakinsa, seda ta ďan ja wasu mintuna tana nazari, sannan ta murda kofar ta shiga.

Koda ta shiga dakin warin sigari yake, Can ta hange shi akan gado daga shi se 3 quarter da vest, ya rufe ido se juyi yake akan gadon, da sauri takarasa gaban gadon tace “meyake damunka ne?”
Bece komai ba idonsa a rufe, se juya kai yake, ya dafe kansa da hannunsa kan gadon ta hau tana magana “ka gayamin ko baka da lafiya?”

Hannu tasa ta janye hannunsa daga kan nasa, ji tayi jikinsa ya dau zafi sosai

“Jalal meyake damunka ne?” yanayin yadda ya bude idonsa ya kalleta ya mayar ya rufe tagane a buge yake, juyawa tayi bayan gadonsa taga guntayen sigari da ya shanye, ga dogayen kwalaban giya da ya shanye.

Tuni idonta ya ciko da hawaye tace “giya Again, Jalal why? Meyasa haka? Kacemin zaka dena kuma kawai inga haka why Jalal?”

Da kyar yake iya bude idonsa, sunyi jawur kaman an hura garwashi, cikin maye yake kokarin yi mata magana amma yakasa.

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724

???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣4️⃣107

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Gaba daya jikinta yayi sanyi ta tsaya tana kallonsa, juyawa tayi ta koma daki ta barshi a parlourn, se bayan ta tafai yaji gaba daya jikinsa yayi sanyi, yake tambayar kansa meyasa yayi mata shouting? Laifin me tayi masa? Gaba daya se yaji ransa ya baci. Ya tashi ya bi bayanta, amma ya tarar ta rufe kofarta sannan ta kashe futile, haka ya hakura ya koma dakinsa.

Washegari bayan tayi salla, ta shiga kitchen ta hada breakfast, kafin ya tashi har ta kammala abunda zatayi tai ficewar ta.

Naja ce ta shigo gidan ko sallama babu sekace korarriya, Yaya mairo ta kalleta tace “ke meye haka ko sallama babu”?
Dan guntun tsaki Naja tayi tace “wallahi matsiya ciyar yarinyar nan ta cuceni, da yanzu ina Abuja ina hutawa, Amma gashi ba Auren, kuma duk samarin nawa sun gudu ga talauci ya isheni”

Yaya mairo tace “kema ke kika cuci kanki, shaye2 Naja, na miki fada har bansan adadi ba, ga wannan abun kunya da kikayi, ba dan Allah ya rufa asiri ya zube ba da shikenan, kinjamin masifa”

“Amma da ya aureni aida zan dena, wannan bakar shegiyar ta zalunceni ita da Allah makira, kuma itama tayi Aure sun barni a titi”

Yaya mairo tace “Aure kuma, wata aura?”

Naja tace “Agurin daurin Auren aka bawa wannan dan shaye2 sadakarta, Jalal suke ce masa ko Jamilu oho dai”

Sa’ada da tun dazu ke kwance na danna waya ba tace uffan ba se yanzu, ta kalli Naja tace “Ke bana son shirme, da gaske Jalal ta aura”

Cikin tsiwa Naja tace “Bansani ba tunda baki yadda ba meye na son se kin tabattar aikin banza kawai, na tsani inyi magana a karyatani”

“Sorry ba karyataki nayi ba, amma waya gaya miki?”

Cikin kosawa Naja tace “Zancen duniya yana buya ne? A anguwarsu naji, har gidan seda aka kwatanta min, shi aka Aura mata, Ai Allah ya kara, Allah yasa yayi mata dukan da seya kashe ta”

Yaya mairo tace “Ameen dai Naja, Ai Allah ne yasaka miki ya hadata da dai dai ita, yayi ta cin kaniyarta”

Kallonsu kawai Sa’ada take da sun san me Jalila ke nufi a rayuwar Jalal da basuyi wannan maganar ba.

Tashi tayi tsam tabar parlourn ta koma dakinsu ta dakko waya ta kira Hannah.
Seda ta kusa katsewa sannan Hannah ta daga Sa’adah tace
“ke Hannah, wai kina inane?”
“kamar ya ina ina? Kefa na Gaya miki Jalal yasa ‘yan sanda su nemoni, ina Abuja se ya huce zan dawo, daga nan na kara shirin tinkarar sa, dan koda tsiya sena cika burina”

“ke dalla banza kina can kina garanci to yayi Aure”

“ke saurara, kamarya yayi Aure? Ya Auri wa? Mutumin da ko budurwa bashida?

Sa’adah tace ” sadakar mata aka bashi a bati, wannan Jalilan dai ita aka bashi sadaka”

Cikin tsawa Hannah tace “Impossible how? Ta yaya? Ke waya gaya miki? A ina kikaji?”

“Yanzu Naja tazo tana zancen, tace haf gidan da yake ta sani”

Hannah tace “please help me, kije ki tabattar min dagaskene, karki sa jinina ya hau bayan karyane”

Sa’adah tace “ke nikike so inje gidansa in yana nan fa, kinsan ba cukakken hankali ne da shi ba, tijara zemin a bainar nasi”

Hannah ta marairaice tace “please Sa’adah ki temakamin, i dan zancen nan ya tabatta sena kusa hauka wallahi, ke dole ma in zo kano ayita ta kare, dan girman Allah Sa’adah ki samomin sahihancin maganar nan”

“karki damu zan duba miki Insha Allah”

Hannah tace “Yawwa kawata ki temaka, dole in tattaro kayana in dawo, dama tazo min da zan nunawa yarinyar nan ta tari aradu da kai”

Sa’adah tace “a da baki nuna mata ta tari aradu da kai ba se yanzu, da ta baku mamaki keda Kanwarsa, kuna nan kuna wahala ta aureshi ta barku”

“haba Sa’adah kefa kikace sadakarta a ka Bashi, ta yaya kike tunanin ze so matar sadaka, kyaleni da shi kawai”

“Hannah wani tabbaci kike da na cewa shi baya sonta, ke kina tunanin za’ayiwa Jalal auren dole a yadda yake ne”

Hannah tace “ke mu bar maganar naan ji nake zuciya ta kaman ta faso kirjina saboda takaici, duk abunda kika gano kimin bayani”

Sa’adah tace “shikenan zanyi kokarin bincika miki”

Sa’adah takoma parlour tace “Naja nikam inane gidan yarinyar nan, inason inje inga kwakwaf, daga nan inci mata mutunci”

Naja tace “kyaje ta bakanta miki rai, kin san ba mutunci ta cika ba”

Sa’adah ta lallabata ta gaya mata kwatancen gidan Jalal.

Koda Jalal ya tashi ya tarar harta tafi school, se yaji babu dadi dabe ganta ba, sedai tayi girkin breakfast ta ajiye masa, yayi breakfast yayi wanka ya fice.
Jalila na daf da kammala lectures message ya shigo wayarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button