ABDUL JALAL PART 2

“in kin gama ina jiranki a harabar department dinku”
ABDUL JALAL
Ajiye wayar tayi, suka gama lectures sannan ta fito, tana fitowa daga lectures ta hango motarsa, tana zuwa ta bude gaban motar ta shiga ba tareda ta kula shi ba, kallo daya yayi mata yasan ta gaji sosai,
Yace “Sannu” bata amsa ba sema kwanciya da tayi a jikin kujerar ta juyar da kanta daga kallonsa tana sauke numfashi. Dukda daddadan kamshin turaren Jalal da kuma turaren dake ta shi a cikin motar sa, hakan be hanata jin tashin wari sigari kadan2 ba.
Ya kunna motar yafara tafiya can ba tare da kalleshi ba Jalila tace “Jalal ka sha sigari ko?”
Jalal yace mata “Eh na sha”
Tace “Good”
“Amma kadan na sha guda biyu ne kawai fa”
Shiru tayi masa har suka je gida, suna zuwa ma bata bi ta kansa ba tai tafiyarta dakinta tai salla ta huta sannan ta fito ta nemi abunda zata ci, jallof din macaroni tayi, ta zauna tana ci a parlour Jalal ya fito, yana zama ta tashi ta koma daki.
Kasa daurewa Jalal yayi ya tashi ya bita dakin nata, ta harde akan gado tana cin Abincin ta, dan stool dinta na kwalliya ya janyo ya zauna a gabanta ya tsura mata ido.
“kaga ni dan Allah kar kasa in kware, kasani a gaba da kallo, shiyasa na baro maka parlour ni bana son kallo”
“Ai ba wani abun nake kallo ba nima, mezan kalla a jikin kwailar da na dauka a hannuna, na goya a bayana, na dinga jefawa sama ina cafewa, ga Yamin me zan kalla?”
Jalila a ranta tace “Lallai Jalal dan rainin hankali ne ya cini wasa”
Amma ta kara hade rai tace
“to tunda ni kwailace bani da abun kallo meye na zuwa kasani a gaba ka tsiramin ido?”
Ta yunkura zata mike, ya riketa ya zaunar da ita akan gadon yace
“dan kinga ina shiga damuwa in kika dena kulani shiyasa kike ta hademin rai kina wani shareni ko?”
Dagowa tayi ta kalleshi tace “Jiya kayimin shouting dan kawai nace kayi Azkar, kuma kasan bana son shouting, yau kuma ka sha sigari abunda yafi bata min rai, dan me ba zanyi fushi ba? Ko sokake in cigaba da shiga harkar ka kanamin shouting”
Ta karasa maganar tana kara hade rai da dan tura baki.
Hannayenta ya riko yace
“Jalila na sha gaya miki ba lokaci daya na fara shaye2 ba, bazan iya denawa lokaci daya ba, kuma ina kokari sosai in dena, sedai lokuta dayawa inaji kamar zanyi hauka idan ban sha ba, duk da haka ina cigaba ds kokari, ki cigaba da yimin Addu’a, sannan Indai Adhkar ne zamu dinga yi shikenan? “
Zumbura baki tayi tace ” ba shikenan ba da saura”
“me yayi saura kuma?” ya tambaya
Tace “ba kabani hakuri ba fa”
Dan tsura mata ido yayi yana kallon ta, yarinyartarta ta kara fitowa sosai musamman idan tana jin rigima
“Nine zan baki hakurin?”
“Eh kawai ka bani hakuri, ai laifi kayi min”
“idan na ki baki hakurin fa? Ke bakiji kunya ba da kikace in baki hakuri?”
“Kunyar me zanji kuma? Laifi fa kayi min, ko kai agurinka ba komai bane?”
“to shikenan I am sorry, bazan kara ba”
Murmushi tayi tace “Yawwa ko kaifa, Jalal duk lokacin da ka batawa mutum rai ko bani ba Dan Allah ka bawa mutum hakuri, Nagode, yi hakuri, dan Allah, kalmomi ne masu sauki se dai suna da wahala a harshen wasu mutanen, duk mutumin da baya gane kuskuren sa ya nemi afuwa hakan alamace ta girman kai, kumma Allah baya son masu girman kai, dan haka ka ko yarone karami ya in dai ka bata masa babu laifi ka bashi hakuri, bazaka ragu da komai ba”
Yadda ta kwantar da kai take sarrafa harshenta gurin yi masa nasihar ne ya burgeshi.
Amma yace
“Waike bazaki dena kirana da Jalal kai tsaye haka ba, kefa baki da kunya”
“to Yaya Jalal”
Hararta yayi yace “niba yayanki bane ba, ni mijinki ne dan haka bana son wani Yaya da can ma inaji haka kike cewa Yaya Jawwad, amma ni saboda kin rainani wai ABDUL JALAL kai Allah ya yafe miki kwailar Ummi”
Dariya tayi tace
“waye mijin, wai kaine mijina, tabdijan, kuma wallahi niba kwaila bace, kuma Allah ya yafe maka dai, yadda ka dinga cin zalina, dan ma ina rufa maka asiri, amma ka ci zalina da yawa wallahi”
Dariya yake sosai, befi ta kirga sau nawa taga yana dariya haka ba
dariyar tayi masa kyau sosai yace
“kin kyauta zakiyi bayani da manyan baki ne, bani Abincin nima inci tun dazu kamshi ya cikamin hamci”
“wannan dan Abincin, me naci me na baka? Jeka dafa naka wannan nawane, meze sa ma kaci Abinci da kwaila?” ta fada tareda dauke plate din Abincin.
Sakkowa yayi ya zauna kusa da ita yace
“dan sanmin mana, ko kadan ne”
Jalila tace “to tsaya yi spoon daya”
Tana miko masa plate din ya mike yace
“Se anjima kin gama cin naki, sannan a kawomin wayata da’aka kwace, dan nasan ‘yan mata na sun kirani ba adadi”
“har zawrawanka ma sun kiraka ai, ni kayiwa wayo zan rama ne”
Murmushi yayi ya nufi haanyar fita yace “kawomin wayar daki, zanyi wankane”
A dan shirin da suke kwanan nan ta kara fuskantar he’s so simple, yana da wasa da dariya ga shi ya iya tsokana sosai, abunda bata taba zata ba, saboda kusan koda yaushe ransa a hade, babu abokin hira, babu me sauraron matsalolinsa.
Bayan fitarsa taje kitchen ta ajiye kwanon da taci Abinci ta dawo daki ta dakko wayar Jalal domin kai masa wayar a silent take dan haka akwai missed calls dayawa a wayar, ta karo volume din wayar ta shiga dakin nasa da sallama, ya riga ya shiga wanka, tana ajiye wayar, wayar ta fara ringing, Tace Jalal “ana kiranka a waya”
“ki daga mana”
“niba zan daga ba, gata nan dai anmaka miss calls da yawa”
Jalal yace “nina ce ki daga ai, yanzun zan fito, kinsa ina surutu a toilet sekace ke”
Daga wayar tayi tasa a kunnenta tare da fadin “Salamu Alaikum”
Muryar mummy ce ke fadin
“ke ina dana yake? Mara mutunci tun jiya nake kiran sa amma kika hanashi dauka, ki bani zanyi magana da shi mara mutunci”
Jiki a sanyaye Jalila tace “Mummy ina wuni, wayar tasa ce a silent shiya…..
Ke dalla ki rufemin baki, mara mutunci wadda bata san darajar kanta ba, kingama zagun sa da cin mutuncinsa agabana kuma kinkoma kin lallaba kin aureshi kina kokarin rabani da shi, saboda wulakanci tunda ya bar gidan nan koda wasa bezo inda nake ba, to baki isa ba wallahi, kuma ki fara kirga kwanakin barinki gidan nan daf nake da datse auren nan bazan taba kaunarki ba, ki bashi waya zanyi magana da shi”
Tuni hawaye ya jika fuskar Jalila tace “yi hakuri Mummy, wallahi ba laifina bane, nima…
Dayake Mummy a hands free tasa wayar Ilham tana jin maganar dasukeyi, Ilham ta karbe wayar tace” dalla malama tace miki da danta take son tayi magana, ke wace irin dabba ce ne haka? Mara zuciya wadda bata ganewa, uwar mutum tace bata sonki dayake ke jinin maita ce kin like masa, dukiyarsa kike yiwa shiyasa kika hada baki da marikin ki kika aure shi, nasan dai ba wani sonki yake ba dan ba abunda zeyi dake, giyar da yake sha tafiye masa komai mahinmmanci ciki kuwa hadda ke, dan haka ba saurararki zeyi ba”
Jalila ta kawo iya wuya, a ranta tace, idan bataka wa wannan Ilham din briki ba bazata sauraramin ba, so take taji halin da nake ciki a zaman gidan nan dan haka tace
“kinga dan Allah saurara Ilham, ke meye naki a ciki da Mummy muke magana ba dake ba, tunda kin matsu bari in gaya miki yana bandaki yana wanka”
Da sauri Ilham ta kalli Mummy ta Zare ido tace “wanka kuma?”
Jalila tace “Eh mana wanka yake yi”
Karaf a kunnen Mummy, hakan yayi dai2 da fitowar Jalal daga toilet yana goge kansa, karasowa inda Jalila take yayi yasa hannu ya karbi wayar daga hannunta, juyawa tayi zata bar dakin ya riketa, yasa wayar a kunnensa yaji muryar Mummy tana masifa
“kinfadi sako, kuma naji, nasan dani kike, ni kike gayawa yana wanka, aiba se kin gayamin ba, mara mutunci”