ABDUL JALAL PART 2

Jalila tace “babu matsalan komai Maaama, lafiya kalau muke zaune”
“dama an gaya miki, zaku zauna lafiya komai ze wuce, Ya shaye2 kuwa yanayi har yanzu kokuwa?”
Jalila tace “A’a Maama, baya shaye2 yanzu ya dena”
“ki ga yamin gaskiya Jalila, karki kare shi”
“Maama da gaske nake, baya shan komai yanzu”
Maama tace “Alhamdilillah, ki cigaba da hakuri dai, kinsan ita rayuwar Aure gaba dayanta hakuri ce, sannan ki toshe kunnenki akan abunda mahaifiyarsa zatayi miki koma take miki, ni kaina akan Auren nan bakiga bacin ran da mukayi da ita ba, hatta harkar business da muke yanzu ta yanke ta a tskanin mu”
Jalila tace “Ke Maama meye naki a ciki, da zata yimiki haka? Ranar daza’a akawoni ma bakiga yadda ta dinga muzanta Auren ba, shiyasa a tsorace nake da Auren nan”
“karki damu, ki kwantar da hankalinki, komai ze wuce, zataji kunya ne a gaba kaman yadda nima naji”
“Haba Maama wannan wace irin magana ce, meye wani jin kunya, dan Allah kidena wannan zancen, Yawwa Maama nifa shekaranjiya Su Naja sunzo gidan nan, Jalal yasa ‘yan sanda sun kama su, na tambayeshi dalili yace babu ruwana narasa ya zanyi”
“rabu dasu Jalila, yaya mairo ta kirani a waya ta zageni tsaf, aina dawo daga rakiyar su, tana’ yar uwata amma tana min zagon kasa da hassada a rayuwa ta, dana zauna nayi tunani dukkan shawarwarin data dinga bani a baya, tasa nake aikata wasu abubuwan turin jeka ka mutu takemin, Jalila nayi dana sanin abunda nayi miki keda mahaifiyarki tsawon shekaru, dan Allah ki yafemin”
Jalila tace “Maama dan Allah ki dena wannan maganar, komai ya riga ya wuce fa”
Suka cigaba da hira, Jalal yazo ya samesu yace
“Maama, Abba yace ki fito ku tafi dare yayi”
Har bakin mota suka rakasu, sukayi musu sallama sannan suka dawo cikin gida.
Koda suka koma Jalila ta duba kayan da su Maama suka kawo mata, fruits ne da kayan chocolate, ta zuzzuba a fridge.
Jalal yace
“My wife zomuje muyi Adhkar mana, zan kwanta”
Hararsa tayi tace “tab bazanzo ba, sedai karka yi” ta gudu dakinta, murmushi kawai yayi ya girgiza kai.
Ilham fa tayi rama sosai tayi duhh saboda bacin rai, Ummanta tace zatayi wani abu akan lamarin Auren an amma taji shiru, babu alamar samun wata baraka a Auren, ba wanda yaji kansu, dama bata ta Mummy, Mummy se aukin masifar, Amma babu wani yunkurin daukar Action da tayi, gashi wasa2 soyayya da kishin Jalal na neman ya kwantar da ita rashin lafiya, ba shiri ta shirya ta tafi gida gurin ummanta, koda taje gidan bata nan, dan haka tanemi guri ta zauna tana jiran dawowarta.
Tayi kusan awa guda sannan Umman tata ta dawo, tana dawowa ta tarar da Ilham din a kwance kaman gawa, a dan tsorace tace
“ke Ilham lafiya kuwa na ganki a kwance?”
Ilham ta dan yatsina fuska ta tashi zaune tace
“To umma ba dole ki ganni a kwance ba, Wata nawa da yun Auren Jalal amma har yanzu banga matakin da kika dauka ba, kamar ma baki damu daki dau fansar ba, kuma ni wallahi Umma nagane son gaske nake wa Jalal wallahi, ko bacci bana iyawa”
Umman tace
“tabdijan ashe baki da hankali, sena makeki keda son gaskiyar, kin san irin fadi tashin da nake kuwa? Har kike fadan kinfara masa son gaskiya? Kinsan me fadawa soyayya da Jalal da kikayi yake nufi? Rushewar burinmu na daukar fansa, da farko munyi sake yafada soyayya har yayi Aure, kekuma kina kokarin rusa komai da kanki, ai idan har son Gaskiya kikewa Jalal hakan yana nufin bazakiyi abunda ya dace in rama abunda uwarsa taimin ba”
Ilham tace “Amma Umma ban san ya’akayi nafara son Jalal haka ba, wallahi ina sonshi, soyayyarsa bazata hana in cika miki naki burin ba amma…….
Cikin tsawa ta katseta
“rufemin baki wawiya kawai, tun yaushe nake jiran ganin kokarin da zakiyi hakan ya tabatta, amma ba wani katabus da kikayu, sakacinki yasa har yayi Aure, na tattara abunda nake dashi na bawa malamai amun aiki akansa daga shi har matar tasa, ba ruwana ni daukar fansa ne a gabana”
“Amma umma duk abunda kikayi masa be isaba? Naga ma bashi yayi miki ba fa, fadanku keda Mummy ne meye nasa a ciki? Wallahi bazan iya dena son Jalal ba, bansan ya’akayi nafara yi masa wannan son ba, nikam zan dau matakin karshe da zanbi in mallaki Jalal”
“Aikuwa abunda baze taba faruwa ba kenan, indai bazaki auri Jalal dan burina ya cika bane to wallahi babu ke ba aurensa, dan na bada damar in haukatarwa ce ta kama, a haukata shi, shaye2 ya ninka na da har se ya haukace inga yadda khadija zatayi”
Ilham tayi murmushi tace “Ayya umma kin riga kin makara wallahi, yadda kikace bazan samu Jalal ba indai ba burinki ne ze cika ba, kema ina miki Albishir da cewa indai yana tareda wannan mayyar yarinyar, babu me iya cutar dashi, tunda akayi Auren nake kasa kunne amma babu wanda yaji kansu, na ziga Mummy har na gaji amma babu wani kwakwkwaran mataki data dauka, Umma wallahi na gaji sannan na karaya, mu zubar da makamanmu tun……..
“Ke rufemin baki, ko in tattakaki, bana yafiya, ko zan yafe komai banda cin Amanar da khadija tayi min, in kin gaji ki kyaleni ni zan karasa aikina da kaina”
Ilham tace “kiyi hakuri Umma, zan cigaba da tayaki Allah ya cika mana burinmu, Sannan zanyi kokarin na cire shi a raina, inyi tunanin yadda burinki ze cika”
Saudat ta rungume Ilham tace “Yawwa yar halak, haka nake son ji”
Ilham kam goge hawaye tayi dan tasan babu ta inda zata dena son Jalal.
Yaya mairo sam hankalinta yaki kwanciya, tayi zarya station harta gaji amma anki bata Sa’adah, ita kuma Sa’adah taki fadar inda Hannah take, wanke kafa tayi ta tafi gidan su Jalal.
Bayan taje sun gaisa da Mummy, yaya mairo tace “Dan Allah zuwa nayi in nemi Alfarma, kisa baki danki yasa a sakar min yarinya ya, daga zuwa gidansa yasa an kamata, wai seta fito da wata, kuma tace bata san inda take ba, amma yayi mirsisi yaki sawa a saketa, naso inje gidan nasa da kaina amma ina tsoron karnima a kamani “
Mummy tace
“to ni mekike so inyi? Ina yarinyar ku yake Aure kije kisa ta saka shi a saketa mana, tunda yana jin maganar ta fiye dani”
Kuka Yaya mairo ta saka “wallahi ni bani da wata alaka da wannan yarinyar, dan Allah kisa a sakarmin ita ko bacci bana iyawa wallahi”
Tausayi Yaya mairo tabata dan haka A dan wulakance Mummy ta dauki wayarta ta kira Jalal
Seda ta kira sau kusan uku sannan ya daga, daya daga ma shiru yayi bece komai ba
Mummy tace “Jalal kana jina?”
“ina jinki mana, meye faru?”
Girgiza masa kai Jalila tayi muryarta kasa2 tace “greet her, Ka gaisheta mana”
Kamar wanda akayiwa dole yace “barka da yamma”
Kasa magana Mummy tayi, anya kuwa Jalal ne?
Mummy tace “Jalal ne?”
“wai baki san wa kika kira bane?”
“A’a ina son tabattarwa ne, nace yarinyar daka sa aka kama, ‘yar uwar Jawwad ga mamanta anan tana Kuka, ina neman Alfarma dan Allah a saki yarinyar nan”
“bani da wani abu dazan miki alfarmarsa, ita kuma ki gaya mata hawaye yanzu ta fara, seta zubar da hawaye kwatankwacin wanda tasa Matata ta zubar saboda abunda suka dinga yi mata itada yaranta, koma yafi hakan,’ yarta kuma baza’ a sake ta ba setayi abunda nace, Hope i make myself clear”
Daskarewa Mummy tayi a zaune, Jalal kuma ya kashe wayarsa,
Jalila kaman zatayi kuka tace “Jalal abun nan dakake yi, jamin bakin jini kake da tsana a gurin ‘yan uwanka da sauran mutane, kuma be kamata ka kasa yiwa Mummy Alfarma ba dan Allah komai ya wuce mana”