ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

“inkowa ya tsaneki ni ina sonki ai, sannan komai baze wuce ba Jalila, Mummy ce silar duk wata mummunar rayuwa danayi, muka rayu cikin damuwa da bakin ciki saboda son zuciyarta, Jalila ban taba tunanin haske ze kuma shigowa ratuwata ba se bayan da kika jajirce a kaina, ko iya kulawar nan da kike bani nasan nasamu sassaucin rayuwa dana fidda ran samu, ki zauna kiyi hira dani, ki bani Abinci, ki saurari damuwa ta, idan raina ya baci ki rarrasheni, wani lokacin kina bani kulawa kaman da da uwa, tun bayan lalacewa ta na rasa wannan kulawar a gurin mahaifiyata da al’umma, wace Alfarma zata nema a gurina inyi mata? “

Kwalla ta taru a idonsa, da alama baya son tuna abubuwan da suka faru, ta kai hannu ta shafa sajensa tace

“Jalal, kowane dan adam kaddararsa a rubuce take kafin a haifeshi, dama can Allah ya kaddara you must go through that situation, koda Mummy ko babu sekayi wannan rayuwar, idan kayi hakuri ka bata matsayinta na uwa, se Allah ya yafe maka kaima, please Jalal forgive your Mum “

” ki kyaleni da maganar Mummyn nan senayi tunani”

Kara marairaicewa tayi tace “please Jalal”

Dan hararta yayi yace “Jalal ko?”

Murmushi tayi tace “Yaya Jalal”

“niba na son wani Yaya Jalal gaskiya, i calls you with different love names, please dukda bani kike so ba, ki dan dinga kirana da suna me dadi nima inji dadi”

Shiruu tayi ba tace komai ba, kasancewar a kwance yake akan cinyarta yasa ya juyo fuskarta tana kallonsa, dan motsa baki tayi amma ta yi shiru

Jalal Yace “Nasan bani kikeso ba, akwai wanda kike so banina ba, kina tausayina ne kawai, Amma please ki gayamin abunda zanji dadi”

Hannu tasa ta Dan shafa sumar kansa tace

“idan nace ZAUJEE yayi?”

Lumshe ido yayi tareda yin murmushi ya maimaita “ZAUJEE, you mean your husband?”

Jinjina masa kai tayi alamar Eh

Jinjina kai yayi yai murmushi yace “I like the Name kwailata”

Ture kansa tayi tace “dagani tunda kacemin kwaila”

Dariya yayi yace “ba zan tashi ba din ai keda cinyar duk nawane, ki shirya nan da next week Insha Allah Daddy ze dawo zamu je gida”

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣6️⃣109

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

Happy marriage lyf to you sister Amina, may yours be among the best.

          _MY FIRST NOVEL _

Mmurmushi Jalila tayi tace

“Masha Allah naji dadi gaskiya, dama bana zuwa ko’ina daga makaranta se gida, gashi an gayyaceni biki ‘yar class dinmu bansaniba ko zaka barni inje?”

Dan hade rai yayi yai mata shiru,

Tace “Kace wani abu mana”

“gaskiya bazaki ba” yaba ta amsa

A shagwabe tace “meyasa?”

Jalal yace

“har yanzu baki kama da me Aure ba, kawai kifita wani ya biyoki no gaskiya ki hakura”

Kara marairacewa tayi tace

“please, Allah tunda nazo gidan nan school kawai nake zuwa, dan Allah ka barni inje”

Makale kafada yayi “yace ni dai A’a”

Ya kalli cikin idonta yace

“Allah me yadda yaso, Baby da dane nace karki fita ko kallona bazakiyi ba, ko baki niyya ba sekin fita dan ki ban haushi ko?”

Shiru tayi ba tace komai ba

Jalal yace

“naji zakije, amma ni zan rakaki kiyi minti goma mu dawo, dan bazaki dade ba, kar inje wani ya kalleki koma wani ya biyoki yace yana so, tunda har yanzu baki gama amsa sunan matar Aure ba”

Dan kallonsa tayi tace

“saboda me? A gaban mutane fa aka daura min Aure”

“eh nasani mana an daura miki Aure, har kikace ba kya son mijin da’aka baki, Amma ai bakiyi daya karatun ba daze maida ke matar Aure, ina da dauriya ko Jalila? Akwai dalilina dayasa na kyaleki kike cin karenki ba babbaka, ina jiran time ne”

Yai maganar yana kashe mata ido daya, sarai Jalila ta gane meyake nufi Amma ta maze tace

“karatu kuma? Wane irin karatu ne kuma haka?”

Jalal yace

“Au baki gane karatun da nake nufi ba?”

Mikewa yayi zaune yace

“bari in fara karanta miki kozaki gane”

Ai zumbur ta mike tsaye ta fice daga dakin, Ba karamin dariya Jalal yayi ba yana son ya zolayeta a irin haka yaga yadda fuskarta ke bayyanar da tsoro”

A zaman su Jalila ta gama fuskantar waye Jalal, mutum ne me matukar son a damu da shi, kulawa take bashi ba ta musamman dan kamar karamin yaro haka yake wani lokacin, ko Abinci ta kawo masa indai bata zauna ta bashi ba, ko ta zauna yana ci suna hira ba baze ci Abincin ba, sannan cikin hikima take canza masa wasu munanan dabi’un nasa zuwa kyawawa, ta tsaya tsayin daka akan kula da ibadar sa da kuma Adduo’i, kulawar da yarasa ce a baya ta taimaka gurin kara dulmiyashi harkar shaye2, Mummy harkar kasuwancinta da son zuciya tasaka a gaba, yayinda Daddy ba mazauni bane, Jawwad kuma ga makaranta ga sauran hidimominsa dukda ya taka mahimmiyar rawa a gurin Jalal, ga kyama da al’umma suke nuna masa saboda yanayi na shaye2 da sauran dabi’unsa, shiyasa abun yayi masa yawa, babu me jansa a jiki yaji matsalolinsa kome yake damun shi, wata shakuwa ce ta musamman ke kara shiga tsakaninsu.

Bangaren Jalal ma babu Abunda ze cewa Allah se godiya, dan ya fidda ran yin kyakywar rayuwa kaman kowa, Amma ba zato ba tsammani dawowar Jalila karo na biyu a cikin Rayuwarsa tazo masa da Haske da tausayawa, a cikin rayuwar Auren nan nasu, dukda kasancewar a baya basa jituwa, Amma ta ajiye wannan a gefe tana ta iya kokarinta a kansa, tana masa biyayya dai2 iyawarta, duk wanda yasan irin rayuwar takun sakar da sukayi a baya, babu me cewa zata iyayiwa Jalal biyayya haka, musamman wanda yasan halinta a bangaren tsiwa da rashin daukar raini, tana zama tayi hira da shi, tai masa nasiha, idan abu ya dameshi ta rarrasheshi hakan ya mantar da Jalal duk wata mummunar rayuwar da yayi a baya.

Tun Yaya mairo tana sintirin zuwa gidansu Jalal akan maganar sa’adah harta gaji ta hakura saboda korar wulakancin da Mummy tayi mata a cewarta

“ta gaji da zaryar da take mata a gida suje can su daidaita”

Ba yadda ta iya haka ta tafi gidan Maama kozata sa baki a sakar mata sa’adah, dan yanzu ko zuwa tayi police station ba’a bari ta ganta, ta kwashe duk yadda akayi ta fadawa Maama,
Maama tace

“to ni Yaya mairo ya kike so inyi?”

Yaya mairo tace

“Dan Allah zainab kisa baki, yarinyar nan Jalila ta gaya masa yasa a sakarmin ‘ya ta dan Allah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button