ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Maama tace

“Yaya mairo idan mukayi haka ai bamu da kunya kenan, ko kin manta irin cin zarafin da kikasa muka hadu muka dingayi mata? Se yanzu zamu nemi Alfarma a gurinta?”

Yaya mairo tace

“Dan Allah zainab ni dai ki roketa a sakarmin sa’adah, wallahi yaron nan da yake ba dan mutunci bane, mahaifiyarsa tana rokonsa a sakarmin sa’adah se cewa yayi, se nayi hawaye fiye da wanda matarsa tayi”

Maama tace

“gaskiya Yaya bazan iya tunkarar Jalila da wannan maganar ba”

Abba ne ya shigo gidan ya tarar da yaya mairo a parlour suna hira, Yaya mairo na gaisheshi be amsa ba yace

“zainab ban gaya miki bana bukatar sake ganin yayarki a gidana ba? Ban hanaku zumunci ba, amma ku hadu a wani gurin, dan bazata dinga zuwa tana rarrabamin kan iyalai ba”

Abba ya dubi Yaya mairo yace

“dan Allah karki kara zuwarmin gida, in bahaka ba zan dau mummunana mataki akanki, ki tashi ki tafi”

Yaya mairo tace “zainab kina kallo mijinki na cimin mutunci?”

Maama tace

“ba cimiki mutunci yake ba, maganar gaskiya ne ai, tunda yace ki bar masa gida kawai ki tafi”

Haka Yaya mairo ta fito tana rusa kuka, ta koma gida ta rasa abunda yake mata dadi, ga Naja ma kwanan ta uku bata gida, ta kirata a waya tace mata

“karta kara kiranta tana cikin koshin lafiya”

Sa’adah kam da taji uwar bari tuni ta fadi inda za’a samu Hannah, akayi nasara kuwa ‘yan sanda sukaje itama suka kamota amma ba’ a saki sa’adah ba ma.

Jalila ta gama shirinta tsaf na zuwa gurin biki, ta dakko Jakarta ta fito, tana fitowa Jalal ma ya fito, ya sanya shadda coffee color, kansa ba hula, ya taje sumarsa ta sha mai, se kyalli take, ga kamshin turarensa ya cika gurin yana kokarin daura wrist watch, Jalila ta kare masa kallo tace

“wow looking so masha Allah” dagowa yayi ya kalleta yana murmushi, karasowa tayi ta karbi agogon ta saka masa, ta shiga daki ta dakko masa hula, tasaka masa sannan tace

“kafi kyau da hula, bari inyi maka hoto”

Jalal yace

“gaskiya sekin biya zakimin hoton”

Jalila tace

“danma zan saka a wayata shine sena biya? To an fasa”

Dariya yayi yace

“hmm ni hotonki a wayata sunkusa dubu, nikuma ko daya nasan baki da shi, bakomai nidai ina sonki my wife”

Jalila ta dan harareshi tace

“ina ka samu hotona har kusan dubun?”

“kina mamaki ne? In mun dawo zan nuna miki”

“to shikenan Allah ya kaimu mu da wo din”

Ta dinga daukarsa hoto, seda sukaci lokaci suna wannan hotunan, sannan sukayi nufin fita, Jalila ta kuma kare masa kallo daga sama har kasa, ta tuna lokacin da yake kan ganiyar shaye2, irin shigar daya keyi, yadda yake magana ga rashin fara’a, ta kalleshi yanzu a hankali ta furata “Alhamdilillah ‘

Jalal yace

“lafiya kuwa kike min kallon kurilla, kinsan fa bana son kallo?”

Dan murguda masa baki tayi tace

“Sena kalla din in yaso a dau mataki”

“haka kikace ko? Zan dau mataki kuwa”

Ta dan laankwasar da kai tace

“kayi kyau sosai, kaman karmu fita a ganka”

Da sauri ya kalleta yace

“do you really mean what you said? kina kishina kenan?”

Dan tabe baki tayi tace “hmm to maybe, Amma kaman ba yau nafara kishinka ba, To ban saniba ko kishin ne koba shi bane”

Wata ajiyar zuciya ya sauke yai murmushi yace

“shikenan muje karki makara, dan 10 minutes kawai zamuyi kuma zamu dan tsaya a wani guri”

Haka suka jera gwanin sha’awa, ya bude mata gaban mota ta shiga sannan ya kunna motar suka fice.

Befi mintuna shabiyar da tafiyarsu ba Ilham tazo gidan, amma me gadi ya sheda mata cewar

“masu gidan yanzun nan suka fita”

Ilham Tace

“megidan shi dawa suka fita”?

Megadi yace

“shida matarsa mana, da alama wani gurin zasu je”

Ilham tace “basu gaya maka ina suka tafi ba?”

A fusace yace

“ke ko dai ‘yar leken asiri ce ke? Nace miki sunfita ubansu ne ni da se sun gayamin ina zasu”

Haka Ilham ta koma gida gwiwa ba kwari.

Koda sukaje gurin biki kallo yakoma kansu, sunyi kyau sosai, a table daya suka zauna itads Jalal,’ yan makarantarsu sukazo suka gaisa, dayake a cikin kawayen Jalila Jalal yafi sanin Zahra ya dan fi sakin jiki da ita, tunda yanzuma kokari yake yana gaisawa da kawayen nata dan kar yayiwa Jalila laifi, bayason taro kuma befiye sakewa da mutane ba, Zahra tace

“Jalila gaskiya ya kamata ayi muku hotuna kaman a saceku a gudu” zahra taita zolayarsu, nan ma hotunan suka sha, maman amaryar tazo wucewa ta tsaya suka gaisa, Jalal yai mata alheri, Jalal kenan zuma ga zaki ga harbi. Seda sukayi kusan awa biyu a gurin, ya bar Jalila ta sake a cikin kawayenta, dan kanta tace ya tashi su tafi gida.

Seda Jalal yafara biyawa ta police station tukuna, suna zuwa suka tarar da Yaya mairo a gurin tana magiyar a barta taga Sa’adah, Jalal kota kanta bebi ba, yayinda Jalila ta gaisheta

Yaya mairo cikin kuka tace

“na gamaki da girman rabbil izzati ki cewa mijinki ko ganin Sa’adah a barni inyi, ina cikin damuwa wallahi”

Jalila ta dafa Yaya mairo tace

“kiyi hakuri Yaya mairo, insha Allah za’a saketa yau din nan ki dena kuka, zesa a saketa”

Jalal daya ga yadda Jalila ke rarrashin Yaya mairo ji yayi kaman ya maketa, wani lokacin halinta daya da Jawwad, komai girman laifin da kayi musu basa riko, ya tuna cin mutuncin da Yaya mairo tai mata a baya, Amma yanzu se lallabata take yi.

Jalal ya gaisa da ‘yan sanda cikin girmamawa sannnan D. P. O yai umarnin a kawo masa su Sa’adah,
Sa’ adah tayi baki kirin ga waga muguwar rama da tayi se uban hakora, Ga Hannah itama har dan gwara Hannah akan sa’adah, seda Jalila ta tsorata da ganin ta.

Hannah seda ta sandare dan mamaki, Jalal ne a cikin wannan shigar manyan kaya na alfarma, yazama wannan kamilin haka? Gefensa ga matarsa Jalila, yarinyar da tafi tsana, lallai Jalila kwararriya ce gurin makirci, tai musu makirci itada Ilham ta aure Jalal

Jalal yace

“Yallabai wannan itace Hannah, ina son a auna ta a tabattar da tanada ciki? Idan tana da shi seta haifeshi ta shayar da shi ta raineshi inya shekara biyar ta bani shi, idan kuma ba ta dashi zanyi kararta a kotu ta nemomin cikina da ta zubar”

Kallonsa Jalila tayi tasan rainin hankali na Jalal zatayi magana ya daga mata hannu, kuka Hannah ta farayi tace

“wallahi Jalal karya nakeyi, bani da komai nayi hakane danka aureni, dan Allah karka yi min haka, zaka tozartani inkamin haka”

Jalal yace “kina gudun tozarci ni kika tozartani a gurin iyayena, idan har karya kike alfarma daya zanmiki, kije dubai gurin mahaifina ki bashi hakuri ki karyata kanki”

Cikin kuka tace

“na shiga uku Jalal, ina naga kudin zuwa Dubai, kayi min rai dan girman Allah”

Jalila ta kalli wani dan sanda tace

“yallabai Sa’adah bata da lafiya ne naga ta rame sosai? Dan Allah Jalal a saki sa’adah tunda ta nuna inda Hannah take kaman bata da lafiya”

Wani dan sanda yace

“to kusan hakan, tana nan a tsare bata samun shan magungunan ta, ankira likita ya dubata maganinta na kanajamau da bata shane yasa yafara nunawa, amma an bata wani, sannan bazamu saketa ba saboda ta hada kai da wannan kawar tata Hannah sun damfari wani Alhaji makudan kudade, dan haka zamu gurfanar da su a kotu”

Ba Jalila ba hatta Jalal da Yaya mairo seda suka sandare a gurin, Yaya mairo ta dora hannu aka tace

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, sa’adah maganin da kike sha tsawon shekaru kikecemin na gyaran jikine dama na wannan cutar ne, Allah ya wadaranki Sa’adah ni Allah yasa baki gogamin ba bansaniba, abun naki hada damfara kai Allah ya wadaranku wallahi banyu dace ba nikam, daga ke har kanwarki da dan uwanku bana zabe, dan uwanku na prison saboda sata, ke karuwanci da damfara, kanwarki shaye2 da karuwanci nashiga uku ni mairo, Allah ya tsinemuku gaba dayanku ‘ya’ yan jaraba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button