ABDUL JALAL PART 2

Dan murguda baki Jalila tayi tace
“seda na gaya maka da zafi ai amma ka sha da zafin”
“na matsu in sha ne shiyasa”
“ai gashi nan ka kone, kayi shiru kuma karka kware dai”
Shiru yayi yaci gaba da karbar Abinci kaman wani karamin yaro, yayinda Ilham keta kokawa da tukunya tana kokarin dora tukunya amma tarasa ta ina zata fara dora tukunyar saboda bakin ciki, kafarta se rawa take, saboda wani azababben kishi da taji yana taso mata.
Jalal kaman ba kowa a gurin haka ya cigaba dayiwa Jalila shagwaba tana bashi Abinci har ya gama ci.
Jalila ta kalleshi tace
“dan Allah meyasa kace in ka tafi kar in kira ka for two weeks”?
Dan murmushi yayi yace
“inda zanje aiki babu network ko kin kira baze shiga ba”
A shagwabe tace “Amma meyasa?”
Kafin yayi magana Ilham ta jefowa Jalila tukunyar dake hannun ta, da sauri Jalila ta rike Jalal tana fadin
“subhanallah”
huci Ilham takeyi tana kuka tare da fadin
“Allah ya isa ban yafe miki ba, wallahi sekinga abunda zanyi miki, sena hanaki sukuni da jin dadin rayuwa makira Azzaluma, kika dinga nuna ba wanda kika tsana sama da Jalal dan mugunta kin aure shi, wallahi ciwon son Jalal baze kasheni ba sekin dandani abunda nakeji”
Ta kuma rarumo food flask ta jefowa Jalila, da sauri Jalila ta shige bayan Jalal ta rirrike shi.
A fusace Jalal yace
“ke wace irin mahaukaciya ce haka? Wallahi kika illatamin mata se na daureki”
Daga bayan Jalal, Jalila tayiwa Ilham wani irn gwalo passionately tareda kashe ido cike da neman tsokana tace
“ni nace miki na tsaneshi? in ma na fada a da yanzu na janye”
Wani farinciki ne ya ratsa zuciyar Jalal tundaga sama har kasa da jin abunda Jalila ta fada akansa.
Hannun ta ya rike suka fice suka bar mata kitchen din.
Jalal yace
“kidena biye mata dan Allah, lokaci nake jira itama seta girbi abunda ta shuka, samunki a rayuwata yafi komai dadi a rayuwa ta”
Murmushi Jalila tayi tace
“nikam muje in duba in Maama ta dawo, dan bazan zauna ta nakasta ni a banza ba”
Jin hayaniya ne yasa Mummy ta Farka daga baccin da take ta fito dan ganin meke faruwa, tana fitowa parlor taga Jalal da Jalila yana gyara mata mayafinta, Ilham ta fito daga kitchen ido duk hawaye da katon muciya a hannun ta tana ihu tana
“wallahi sena ga bayanki muguwa makira, yadda kika kunsa min bakin ciki sekin kunshi wanda yafi nawa, saboda makircin ki burin mahaifiyata be cika ba, nikuma ciwon so ya kamani ina ta azabtuwa, wallahi sena tozarta ki”
“wallahi ba’a haifi ‘yar da zata tozarta ni ba, ko ta wulakantani ba, kuma ni makirci ai uwarsa ce ni, nina haifeshi na yanke masa cibi, na goya shi a bayana, ke bari in gaya miki har yanzu ina nan a Jalila na da kika sanni ba abunda ya canza, kuma sedai ciwon son ya kasheki, zan bar Jalal ya auri duk macen da yake so a fadin duniya amma banda irinki, tunda na shiga baki isa ki shigoba wallahi, a baya ma bakiyi nasara ba balle yanzu”
Yadda Jalila ta hakikance yafi komai yiwa Jalal dadi, In dai hakane Jalila ba yanzu ta fara sonshi ba, tunda ba yau ta fara fada saboda shi ba, Jalal yace
“Baby keep quiet, kar ranki ya baci a banza” ya hade rai ya kalli Ilham, gaba daya ya koma Jalal dinsa yace
“idan baki taba ta ba bakya kaunar Allah, mahaukaciya wadda bata san darajar kanta ba”
“Ai babu babban mahaukaci sama da kai, bakaji kunyar yadda kake zakewa saboda mace ba, akan wannan shedaniyar yarinyar, Jalal kayi asara kaji kunya, ka fifita mace akaina, shine kake ciwa Ilham mutunci saboda kake kiranta mahaukaciya, shekara da shekaru tana sonka amma babu tausayin ta a zuciyar ka, kaje ka auri wannan me soyayyen idon” Mummy ce take kumfar baki tana masifa
Wani irin murmushi na rainin hankali yayi, yayin da Jalila ta tsakure guri daya takasa cewa uffan, Jalal ya kalli Mummy yace
“Inason Jalila sosai, kuma kamar yadda ta fada, tunda ta riga ta shiga babu wadda zata biyo bayan ta, wallahi ko Ilham zata haukace bazan aureta ba na tsane ta, tarihi na shirin maimaita kansa Mummy, dama nazo ne dan kiga namijin kokarin da sirikarki keyi akan danki, kuma nason kin gani sedai son zuciyar ki”
“Jalal you have to watch what you are saying, Mummy ce fa, be kamata ka daga mata murya ba, balle ka fadi abunda ze bata mata rai”
“Ohh Sorry dear zan gyara insha Allah” be bar Jalila ta kuma magana ba ya janyeta sukayi waje, yayinda Mummy ta daskare a gurin, Ilham kuwa dora hannu tayi a kanta tana rusa uban ihu.
Suna fita Jalila tace “Jalal meyasa kakemin haka a gaban Mummy, hakan ze kara sawa ta tsaneni ne”
“Jalila wallahi bazanji kunyar nuna miki soyayya ko agaban waye ba, ai ba haramun nayi ba, kuma ina so Mummy taji abunda Hajiyar Daddy taji lokacin da baya sauraren kowa se ita.
“Amma ai ba kai yakamata ka yi ba, komai ya wuce ai, dan Allah Jalal ka dena yiwa Mummy haka mahaifiyarka ce fa, ita ta haifeka, ko yaya she deserves to be respected as a mother”
Jalila kenan dukda abunda yake wa mahaifiyarsa yana jin dadin yadda take nuna damuwarta akan iyayensa
“shikenan naji, amma bazan iya boye soyayyar da nake miki ba ko a gaban waye, muje ki dau trolley dinki, zan tafi airport yanzu”
Koda ta dau trolley seda ya rakata har cikin gidan, yace shi baze shiga ba yasan yanzu suka dawo karya takura musu. Memakon ta tafi tsayawa tayi tana kallonsa
Yace
“ya dai, ki shiga mana”
Dawowa tayi Ta dan langabe kai ta rike hannunsa tace
“bakomai, Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah ya tsare gabanka da bayanka, Allah yabaka abunda kaje nema ya daukaka a harkar aikinka, Allah ya azirtaka da halal ya tsareka da haram, Allah ya wadata ka ya karfafi imaninka, ka kula da kanka kaji, ka dinga cin Abincinka, ka dinga adhkar da sallolinka akan lokaci kaji zaujee na”
Takarasa maganar tareda dan jan dogon hancinsa, Jalal kallonta kawai yake yi, komai nata a nutse ga Addu’oi, yasan da Ilham ya aura baze taba samun haka ba.
Hugging dinta yayi ya kai bakinsa daidai kunnenta yace
“Ameen ya Allah, thank you very much my love, na miki Alkawarin zan kula da kaina, zanyi azkar da sallolina akan lokaci, Kema Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku, Alhamdilillah for having you as my wife, jin wannan Addu’oi seda ga bakin mace tagari, Allah yayi miki tukuici da gidan Aljanna”
Murmushi tayi ta shafa kansa tace “Ameen Zaujee, kaje kayiwa Mummy sallama, sannan kayi hakuri kome zatayi maka, karka fadi abunda ze bata mata rai” jinjina kai yayi ya cikata, taja trolley dinta ta shige.
Tana shiga ta tarar da Nana a parlor, ai da gudu suka rungume juna, Jalila tace
“My Nana kece? Saukar yaushe”?
“Saukar yau mana, dazu Maama sukaje suka dakkoni a airport”
Kara rungume juna sukayi, Jalila tace
“Maama shine baki gayamin zatazo ba”
Maama tace “ai gata nan kin ganta ai”
Jalila tace
“Nana kinga yadda kika zama lukuta kuwa, me kikeci haka wai”
Maama tace
“ku zauna mana se kace kun shekara baku hadu ba”
Ai basu tsaya a parlor ba suka wuce dakinsu na gidan, komai yana nan, taaf da shi ana gyara dakin, suna zuwa Nana ta cire hijjabin jikinta tace
“ga abunda yasani kiba nan, se naga na zama mummuna ko Baby?”
dariya Jalila ta sha cikin Nana ya fito sosai tace
“Allah sarki rayuwa, kaman ba tare muke shiririta a dakin nan ba wai Nana ce da ciki, wallahi ba wani muni da kikayi, kinma fi kyau a haka”