ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Nana tace “wallahi Habibi ma cewa yake cikin yamin kyau”

Dan ya mutse fuska Jalila tayi tace

“waye kuma Habibi?”

“mijina mana, ko an gayamiki kowa irinkune? Ana so ana kaiwa kasuwa”

Dariya Jalila tayi tace

“ina wane mu, wannan abu ai se su Hajiya Nana manya, to ya Yaya Mahmud da Anty Salma? Ya kuma England da masu jajayen kunnuwa”

Nana tace “suna lafiya, wannan tambayoyi haka”

Jalila tai murmushi tace

“masha Allah, Nana cikin nan da nauyi kuwa, wallahi yayi miki kyau sosai?”

Hararta Nana tayi tace

“ki bari in yazo kanki seki ji”

Haka Jalila taita tsokanar Nana, Abba yayi murna ganin yadda yaga Yaran nasa kowacce cikin nutsuwarta.

Da daddare ma hira sukaita yi, Jalila ta kunna data taga Jalal online, nan ta manta da batun Nana suka dinga chatting da Jalal har Nana tayi bacci

Jalila ta turawa Jalal “bakajin baccine?”

“banaji, nakasa baccin ma gaba daya?”

“me yasa?”

“Am missing your body warm, that make me fall asleep”

“hmm, Performe Ablution, recite qur’an, and hug your pillow, goodnight ????”

Murmushi ya dinga yi, ya duba agogonsa karfe biyu da rabi na dare, ya tura mata

“ni kike cewa in rungume pillow ko? Zan kamaki ne, let’s meet in your dreams” ya rufe data ya kwanta.

Washegari bayan sun kammala breakfast suka dau haramar tafiya bauchi, tunda gari ya waye take trying lambar Jalal amma taki shiga, har suka tafi bauchi layinsa ya dena shiga.

Har sukaje garin bauchi Jalila ji take kaman bata da lafiya saboda takasa samun Jalal a waya,

“dama da gaske yake semunyi sati biyu ba muyi waya ba?”
A status dinta ta rubuta

“I miss you zaujee”

Se la’asar suka isa, sun gaji sosai, musamman Nana ga tsohon ciki ga gajiyar tafiya, suna fitowa daga Mota taga Yaya Jawwad
“Yaya Jawwad i miss you wallahi, dama zakuzo kuma wannan surprise haka ba wanda ya gayamin”

Jawwad yayi murmushi yace “Ai gara da mukayi surprising dinki, Jalal yasan zamuzo ai shine yayi miki lefi”

Jalila tace “yaya ina Hanan?”
“muje kya gani”

suka rankaya zuwa ciki abunda yayiwa Jalila dadi be wuce tozali da Hanan da tayi ba da nata katon cikin itama da gudu ta rungume Hanan Jawwad yace

“A’a Baby ayi a hankali kar aimana barna mun kara yawa”

Nana ta bude baki tana jinjina kai yaushe Yaya Jawwad yazama mara kunya?

Jalila tace “Allah yabada hakuri, zan kula”

Nan gidan yau dau shewa, hatta Mummy Hanan da daddynta sunzo, Daddy yayi mamaki yadda yaga Jalila tayi kalau da ita, kaman ba ita aka dinga fama da ita tana kukan bata son Jalal ba.

Jalila tace “bari inje inga Innata”

Anty fiddo tace “Inna tana lazimi bata son aje dakinta in tana lazimi se dai anjima” daga nan suka baje suna ta hira.

Nana tace

“ni Yaya Jawwad yabani mamaki, ga yadda yake salihi ga kunya, amma waishi ke cewa za’a musu barna, tab matar Yaya Jawwad da ciki abun mamaki”

Dundu Haanan tayi mata tace

“Nana zan miki rashin mutunci akan mijina, ina ruwanki damu”

Jalila dariya take musu

Yusuf ne ya shigo shima dan gaisawa da su Abba, ya tarar da su Nana a parlor suna ta hira, yaga Jalila tsaf da ita ta dan kara kiba ma, Hanan da take dan danna waya ta dago tace

“waike Jalila daga rabuwarku jiya hada wani status wai you miss him, sarkin gulma ashe kun jone? Kamar bake kika dinga kuka kina ba kya so ba”

Jalila ta Harare ta tace

“da kika ce yanzu ina son abuna ai mutu ka raba” shewa sukayi gaba daya
Nana tace “dan bakiga hotunan da sukeyi a wayar ta ba, soyayya suke sha abunsu, ahh komai lokaci ne hakuri me tadda rabo”

Yaya Yusuf yayi gyaran murya, suka nutsu gaba daya sukayi tsit suka gaisheshi ya wuce.

Anty fiddo tafito tace

“ku taho dakin Daddy akwai magana”

Jalila taji dam “Allah yasa lafiya”

Suka mike suka nufi part din Daddy, Jalila na gwada yadda su Nana ke tafiya.

Suka shiga da sallama, gaba daya iyayen nasu sun hallara, Jalila kanta a kasa ta nemi guri zata zauna daga kan da zatayi ta sauke su cikin idanuwan Ummi da ta kura mata ido.

Zumbur ta mike ta fasa zamana tana kuma zaro idon ta waje.

Maama tace “Jalila ki zauna mana”

Wani irin yawu Jalila ta hadiye tana nuna Ummi tareda dan ja da baya zatayi magana Amma taji numfashin ta na sauka da kyar cikin huhunta ta dena ganin komai se duhu.

Da sauri Ummi ta mike ta karasa inda Jalila take, kafin tayi wani yunkuri Jalila ta silale kasa sumammiya a gurin

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣8️⃣111

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Ummi ta rungume Jalila sosai a jikinta, Jawwad ya dakko ruwa me
Sanyi a fridge aka shafawa Jalila ruwan a fuska, a hankali Jalila ta bude ido tareda jero ajiyar zuciya ta sauke idonta akan Ummi, kara kankame Ummi tayi tareda sake fashewa da kuka.

Maama tace

“Jalila ba kuka zakiyi ba, kamata yayi ki godewa Allah ganin mahaifiyarki da kikayi”

Abba yace

“hakane yakamata ki godewa Allah sannan ki godewa mijinki da danginsa”

Kallon Abba tayi cike da rashin fahimtar abunda yake nufi

Daddyn Hanan yace

“gaskiya kam, mijinki ya cancanci yabo, da shi da danginsa, kuma kafa da kafa zamuje domin nuna godiyar mu da farincikin abunda sukayi”

Sam Jalila bata san inda zancen nasu ya dosa ba.

Ummi ta share hawayen fuskarta tace

“tabbas bayan godiya ga Allah daya nuna muku naku ahalin, zanyi godiya ta musamman bisa Jajircewarku da kulawa da tarbiyya yarinya ta, nagode Allah yasa ku dauka a gidan Aljanna, Jalila bata tana kukan rashin mahaifi ba sanadiyar tarasa wani abu ba nagode kwarai.

Tabbas Jalal yasan inda nake, lokacin dana bar ku nayi sallama domin zuwa garinmu, motar mu ta tsaya domin musulmin cinkinmu su gabatar da salla, bayan nayi salla ne na tsallaka wani restaurant na sai Abinci, na fito zan tsallaka titi mota ta bigeni, mutane suka fara taruwa a gurin, wanda ya bigeni dan sanda ne, dan haka ya nuna musu id card dinsa ya daukeni ya tafi dani.

Ya kaini wani Asibiti na kudi, inda aka tabattar masa dana samu matsala a kashin bayana, sannan nasamu internal injury akaina, lokacin da labarin bata na ya iskeku Jalal ya shiga zuwa offisoshin yan sanda domin an gaya masa dan sanda ne ya bigeni, Allah ya temake shi yasamo wanda ya bigeni yaje har Asibitin da nake, koda yaje yaga halin da nake ciki, yai magana da mahaifin sa akayimin visa zuwa Dubai a wani Asibiti, na dade ina jinya saboda aikin da’akayimin Kashi kashi a bayana saboda matsalar dana samu.
Dana fara samun sauki Jalal yai magana da Hajiya Salma aka maidani Can England gurinta take jiyyata aka cigaba da bani kulawa a can.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button