ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Hajiya Salma ta zauna dani kaman ‘yar uwatta, a gurinta na warke gaba daya, tun ina Asibiti Jalal yaso ya bayyana muku inda nake amma nahana shi saboda ina cikin mawuya cin hali, bayan na warke nai shirin dawowa Nigeria nacewa Jalal bana son kusan inda nake musamman Jalila, idan har Jalila tasan ina raye bazata taba yadda ta zauna a gurin Abban Jawwad ba, nikuma bana son Abunda ze shafi Addinin ta, Yarenta, da Al’adar ta, saboda ni dangina nada banbancin Al’adu da Addini, kuma yin hakan kaman na saba Alkawarin da nayiwa Aliyu ne kafin ya koma ga Allah.

Jalal da mahaifinsa, Hajiya Salma, wanda ya bigeni da Mijin Antyn Jalal me sunan Abeenki su sukamin rakiya har masarautar mu, Abunda ya bani mamaki be wuce yadda masauratar suka karbeni kai tsaye ba cike da kauna da girmamawa, sannan na tarar anbawa mutanen dake gidanmu damar kowa yayi Addinin da yake so ciki hadda musulinci, mahifiya ta ta musulun ta, kakana kuma ya rasu, Yaya na ke mulki yanzu”

Ummi ta kalli Jalila tace “Jalila ban guje ki ba, a duniya ina matukar sonki ke nake kallo in tuna Aliyu, nayi haka ne domin gyaran rayuwar ki, nayi haka don ki tsaya da kafafunki ko ba kowa tareda ke zaki iya rayuwa keka dai, kin koyi darusan rayuwa daban2 da nake ta nuna miki a baya kika kasa ganewa, lokacin da Jalal ya gayamin an daura muku Aure amma kince bakya sonsa, na shiga damuwa sosai, dan tuntuni nake miki Addu’ar samun miji nagari, kuma koda Ina jinya Jalalya gaya wa Hajiya Salma ta gayamin yana sonki, banji ina kin abunba saboda nasan kina son Jalal kema”

Ummi ta kalli Jalila tace

“Jalila tsawon lokacin dana dauka bana tare dake kowane lokaci kina raina ina miki addu’a a duk inda kike, zaki shiga damuwa idan kika ga halin da nake ciki na jinya, Amma Alhamdilillah naji dadin yadda naganki, Allah ya albarkaci rayuwar ku gaba daya”

Daddyn Hanan yace

“Masha Allah, Kinga abunda muke gaya miki tun a wancan lokacin ko ‘yar Baba, yanzu da kin wulakanta Jalal da wani ido zaki kalleshi, ba ke kadai kikayi masa halacci ba, shima yayi miki, da fatan zaki kara rike mijinki ki kula da shi, duk da halayen Jalal na ki, Amma mutumin kirki ne, Abun mamaki duk yadda yake da Jawwad be sanar masa ba, se last month ya fada, watan mahaifiyar ki guda a gidan nan, kuma har can garin nasu muma munje, sannan munje maiduguri ma, Insha Allah a satin nan zamuje dake maiduguri kema ki musu godiya sannan muje kiga ‘yan uwan mahaifiyar ki su ganki, dan munji dadin yadda suka karbemu cikin girmamawa da mutunci”

Jalila kasa magana tayi, yanzu take tabattar tayi wauta, da ta cigaba dayi wa Jalal rashin mutunci da wani idon zata kallesu, ta tuno yadda ta kusa bijirewa Auren, Allah sarki dukda halin bakin ciki data shiga a wasu lokuta a baya, Amma ga karamci da kauna da wasu mutane da bata hada dangi da su ba sukayi mata ba tareda ta sani ba, ga jajircewa da wannan dattawa da kokari da suke tayi a kanta da Mahaifiyar ta Abba da kuma Daddy Hanan.

Mikewa tayi ta tafi gaban Abba ta zube akan gwiwowinta ta riko hannunsa amma takasa magana sema wani kuka da ya sake kwace mata.
Ba wanda beji tausayin Jalila a gurin nan ba dan Hanan da Nana ma kukan suke taya ta.

Abba yace

“Jalila kukan ya isa haka, ai murna yakamata kiyi ba kuka ba, kar kanki yayi ciwo sarkin kuka kawai”

Jalila cikin kuka tace

“Abba narasa me zance, Allah ya biyaku ladan dawainiyar da kukayi dani, Ummi dan Allah ki bawa su Abba hakuri, naso na bijirewa maganar Auren da sukayimin a baya, Abba dan Allah kuyi hakuri ku yafemin, Sannan shima a bashi hakuri abubuwan da nayi masa”

Abba yace

“Ai baki bijire mana Ba Baby na, ba abunda kikayi mana, kinmana biyayya yarinya ce ke me matukar hakuri da biyayya, Allah baze tozarta ki ba Jalila, halinki daya da mahaifinki, sadaukarwa da kawaici Allah yayi masa rahama”

Daddy yace “in ce ko yanzu kina son nashi dai?”

Daga kai tayi alamar eh, seda ta basu dariya, amma babu Alamar Jalila zata sassauta kukan da take yi.

Maama tace
“zanyi Amfani da wannan damar in baki hakuri Maryam, na cutar dake da Jalila a baya, Amma nayi nadama, sharrin shedan ne da kuma zigar ‘yar uwata, Amma daga baya nayi nadama, wallahi samun yarinya me halin Jalila se an tona, bata taba min rashin kunya ba duk abunda nake mata, dan Allah Maryam ku yafemin “

Ummi tace

“Haba Zainab, wallahi kin gama min komai a rayuwa, tunda kika zauna da Jalila kika rike ta, abubuwan da suka faru da ni da ita itace kaddarar mu, kuma ko yanzu Alhamdilillah, karki damu ni ban rikeki da komai ba, Allah ya yafe mana gaba daya”

Suka amsa da Ameen gaba daya, Babu alamar Jalila zata dakata da kukan nan, dan da kyar take jan numfashi ma.

Daddy ya kalli Anty fiddo yace

“fidausi ku kai yarinyar nan daki ta kwanta ta huta, wannan kukan ze iya jamata matsala”

Haka akayi suka kama Jalila zuwa daki suka kwantar da ita, suka kukkuna mata fanka, tana ta sauke numfashi.

Yusuf yayi mamaki, yaji labarin rayuwar Jalila da kuma waye Jalal, tabbas babu wanda ya dace da Auren ta se Jalal.

Seda aka kira likita yayi mata allura tayi bacci dan bata gane waye akanta, dan kukan da tayi ya saukar mata da zazzabi me zafi da ciwon kai.

Ilham ta shirya ta tafi gidan su Yaseera, tana zuwa tayi sa’a yaseera tana nan, suka gaisa da babar su yaseera sannan suka wuce Dakin ta, suna shiga yaseera ta kalli Ilham tace

“Ilham abun har ya kai haka? Kinga yadda kikayi duhu, kin wani rame ko baki da lafiya ne?”

Ilham tace “wallahi Bani da lafiya yaseera, Amma ban damu da rashin lafiyar ba, ina cikin damuwa kuma mafita nake nema cikin gaggawa ko wace iri ce”

Yaseera ta gyara zama tace “ina jinki, nasam dai ta tsuniyar gizo bata wuce koki, akan Jalal ne ya ake ciki? Har yanzu baki hakura ba?”

“ta yaya zan hakura yaseera, kinsan son Jalal ya zame min bala’i?”

“ban gane ya zame miki bala’i ba, ina dama can soyayya ta shiri ce zakuyi dan ya aureki?”

“yaseera wallahi ashe son gaskiya nakew Jalal ban san hakan ba seda yayi auren nan, Yaseera yarinyar nan muguwar player ce, wallahi soyayya suke kamar ya hadiye ta, Yaseera uwar sa fa yake gayawa wallahi ko a gaban waye se ya fada yana son matar sa, Yaseera zan iya rasa raina saboda yadda soyayya Jalal ke kara ruruwa a raina”

“tabdijan Ilham kinga da Jalal yana jin maganar mahaifiyarsa to tabbas zata tirsasashi ya aureki, amma yadda yake din nan a duniyar nan babu me iya raba shi da ita, ni tun a baya na fuskanci abun nan nasu akwai soyayya a ciki, Amma nayi gudun in gaya miki saboda karki ji haushi”

“to yaseera meye abunyi yanzu?”

Yaseera tace “wane kokarin ummanki take akan lamarin”

Dan tsaki Ilham tayi tace “itafa kawai burinta ta dauki fansa, bata tausayawa halin da nake ciki, itama Mummy bata ni take ba, kawai burinta ta raba Auren”

Yaseera tace “to mafita daya ce a yanzu, Amma ban san yazaki kalli abun ba”

“nidai gayamin koma meye zanyi”

“kin san da bakinki kika gayamin asiri baya tasiri akanta, sannan tunda Jalal ya riga ya aure ta nasan sun hada shimfida, abu daya zuwa biyu zakiyi yanzu, ki cigaba da hakuri kiyi duk yadda zakiyi ki tabattar babarsa ta raba auren nan, sannan kije ki karya sihirin da kukayi masa, idan har ya karye zeji maganar mahaifiyarsa, in yaso se kiyi kokarin kiyi wani asirin da duk yadda zakiyi mahaifiyarsa ta tirsasashi ya aureki “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button