ABDUL JALAL PART 2

Murmushi Ilham tayi tace
“kin kawo shawara Yaseera nagode sosai”
“Amma kije kiyi magana da Umman kiji me zata ce”
Dan zare ido Ilham tayi tace
“wace Umman, wallahi bazata yadda ba tabdijan, tunda naga kowa kansa ya sani nima kaina zanwa fafutuka, ta taba bani labarin inda taje akayi asirin, zan Lalla bata ta kara gayamin yadda abun yake, sena karya asirin dan burina ya cika, nagode sosai yaseera”
Yaseera tace “shikenan Allah ya temaka” daga nan Ilham ta samu relief ta saki jiki suka sha hira.
Kiran sallar Asuba da’akayi ne yasa Jalila ta farka, Addu’a tareda fatan Allah yasa ba mafarki bane, Allah yasa Ummi ce da gaske, ta bude idonta ta juya, kamar yadda ta saba gani wasu shekaru da suka shude,
Da gudu ta sakko daga kan gadon dukda ciwo da kanta yake ta rungume Ummi gam.
Cikin kuka take cewa
“Allah yasa ba mafarki nake ba, Allah in bacci nake Allah kasa in dawwama inayinsa, Allah kasa a jikin Ummina nake, Ya Allah.. Ya Allah…
Ummi tasa hannu ta dago ta, dukda Ummi hawaye take sharewa tace
” Haba Babyna, ba bacci kike ba, nice Ummin kice, kalleni nice”
Kara rungume Ummi tayi dan ji take kaman in tayi wasa Ummi zata kuma tafiya ta batta.
Dakyar Ummi ta lallaba Jalila tayi salla tana idarwa ta kuma kwanciya a jikin Ummi tace
“Ummi meyasa kikaki ki bari in san inda kike, inyu jinyarki da kaina? Na shiga damuwa na shiga kunci, Nayi kuka a lokacin da babu me rarrashi na Ummi, meyasa Ummi?”
Ummi ta numfasa tace “Jalila a lokacin da nake jinya ko kinzo bazan ganeki ba, i partially loose my memory”
Mikewa zaune Jalila tayi tana kallon Ummi, Ummi ta jinjina kai tace
“tabbas Jalila na manta da abubuwa da yawa a wannan lokacin, But Alhamdilillah idan bani na fada ba, babu me gane hakan se su Jalal da suka san nayi, da Mahmud tunda a gidansu nayi jinya”
“yanzu Ummi Yaya Mahmoud ma yasan inda kike amma aka rufeni, shiyasa ranar da ya fara ganina yace nice Jalila?”
“sosai makuwa, sannan duk iya shegen da kika dinga yiwa dana nasani, Inda Allah ya temakeki kema kinyi rawar gani gurin sauya rayuwarsa, Tun kuna kanana na fuskanci Jalal yana matukar sonki, Har Abeenki yace Insha Allah in dai yana raye in har kina son Jalal ze bashi, Abun Allah, Allah ya kaddara ke rabonsa ce, Jalila duk mutumin daze soka tun baka san kanka ba wannan shine masoyi na gaskiya, babu abunda ze sameki ya guje ki”
“Amma Ummi me yasa baki gayamin a baya ba?”
“ta yaya zan gaya miki? Kina fama da rashin ji da tsiwa, a lokacin ma ga abunda kike masa inaga na fada miki, Jalila hatta mafarkin da kike da Jalal nasani, kiyi ta surutai cikin bacci, nidai na dage muku da Addu’a ne”
Dan murmushi Jalila tayi
“tabbas Ummi Addu’a ki bata fadi kasa ba, Amma Ummi na sha wahala wallahi, naga kalubale daban2”
Nan ta labartawa Ummi wasu daga cikin gwagwarmayar da tayi, daga karshe tace
“Ummi da muna mutunci da Mummy sosai, Amma tunda Jalal yafara nuna yana sona ta tsaneni Ummi, kinga cin mutuncin da takemin kuwa?”
“Jalila Kamar yadda Allah ya tsamoki daga cikin kaddara daban2, karkiyi tunanin shikenan, dole ki fuskanci wata kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa da yake sone dan haka ki gode Allah kiyi fatan Allah yasa ki cinye dukkan jarrabawar ki.
Sannan ba abun mamaki bane dan bata sonki, tunda inkika tuna abunda tayiwa kanwarta da suke uba daya, ke a wa daba zatayi miki ba? Tsoronta daya kar a mallake mata da, shiyasa take ganin ke matsala ce a rayuwar danta, duk kirkinki Jalila baze taba yuwuwa kowa ya soki ba, dole wani seya kiki, karki taba tunanin kowa seya soki, wani ze nuna a fuska yana kaunarki, Amma zuciyar sa babu wadda ya tsana kamar ke, sedai Jalila kiji tsoron Allah, yadda kika dauki aniyar sauya rayuwar Jalal karki sa ya kauce hanya, kar son da yake miki yasa kisa yaci gaba da fito na fito da mahaifiyarsa dan bata sonki, ki rike mijinki Jalila, Shi Aure idan ka samu wanda kake so ka iya tafiyar da shi yadda shari’a ta koyar, babu abunda ya kaishi dadi, shiyasa har gobe bazan manta Aliyuna ba”
“kai Ummi ko kunya ta ba kyaji?”
Ummi murmushi tayi tana girgiza kai,.
Jalila ta dan bata rai tace
“ummi Jalal tun kan ya tafi Lagos yace kar in kirashi har sati biyu wai bazata shiga ba, ashe abunda ya shiryamin kenan, dan Allah ki kiramin shi a waya, nasan ke ze daga naki Kiran”
Ummi tace
“A’a abunda yake so shi nake so, dan haka se kiyi hakuri se lokacin da yace, ai gara ya rama shima”
Jalila ta dan sunkuyar da kai tace “Ummi ina son ine nemi afuwar Jalal, tun kafin in san dawainiyar da yayi min dake, ina jin nauyinsa idan na tuna abunda na dinga yi masa a baya, dan ma wani abun baki sani ba”
Hira ce sosai Ummi da Jalila suka cigaba dayi, wani lokacin suyi kuka, wani lokacin suyi dariya, Ummi na ta kara yiwa Jalila nasiha, har gari ya waye yayi haske har kusan goma suna tare, aka fara shigowa duba Jalila, aka tarar Jalila ta ware tanata hirar ta da Ummi.
Warewa sukayi aka cika dakin suna ta hira da Ummi, Ummi se lallaba Su Hanan takeyi, Jawwad ji yake wani bangare na farincikin iyalansu sun dawo, koba komai Ummi ba abar yarwa bace, dan itace uwar rainonsu shida Jawwad, Amma shi kansa Jawwad ya sha mamakin abunda Jalal yayi.
Jalila tayi2 wayar Jalal ta shiga amma taki shiga, ta tura masa messages amma shima babu response, abun ya fara damun ta sosai, Harta E-mail dinsa ta tura masa sakkonni amma shiru.
Jalal kam yana sane yayi mata haka, in bahaka ba yasan halinta ta dinga tuhumar sa kenan, koma taita koke2 se ya dawo, wani lokacin ya kan bude system dinsa ya duba sakkonin Jalila,
“zaujee pick my calls please, i have a lot to say”
ire iren messages din nan dayawa a Gmail dinsa, murmushi yayi yace
“Baby na sarkin rigima, dama akwai ranar da zatazo kidinga nuna missing dina haka?”
Murmushi ya kara yi yace
“Yarinya se na rama tukuna, gara kema ki dana abunda nake ji”
Ya dauki wata wayar tasa daban ya kira Jawwad, yana kira Jawwad ya dauka, suka gaisa Jalal yace
“Jawwad ina matata ne? Fatan tana lafiya?”
“ban sani ba, ai kafini kusa da ita, ka wani kashe waya kana wahalar min da ‘yar uwa”
Jalal yace
“ba ruwanka, kai waya dameka kai da matarka, kawai kuyi kallo, dan Allah Jawwad tana ina me take yi yanzu?”
“Wallahi tana cikin damuwa Jalal, tayi murnar ganin Ummi sosai, Sannan a gaban mutane take kuka tana a baka hakuri, har gurina tazo tana tambaya ta ko ina samunka a waya? Ba yadda na iya ka sanayi mata karya”
Hanan da take gaban Jawwad yana bata Abinci tace
“Jalal ka temaki sister na, ta horu fa, kullum se tayi zancen ka babu Adadi,” Allah sarki Jalal dina, ko yaci Abinci? Ko yayi Adhkar dinsa? Da yana nan dai dai yanzu muke cin Abinci, Allah ya dawomin da shi in bashi hakuri” haduwar ta da Ummi be sa ta manta da kai ba, tana kewarka sosai fa”
Ajiyar zuciya yayi yace
“Allah sarki masoyiyyata wallahi nafi missing din ta, banyi haka dan ta shiga damuwa ba, wannan shine burina, Jalila ta hadu Ummi, bayan Ummi ta warke, nasan Jalila tana sona, Kaman yadda Hanan ke fada ne, tana da taurin kai, bata fiye yadda da abunda zuciyar ta tazo mata da shi ba, Hanan dan Allah ki cigaba da rarrashin ta, in dai na daga wayarta nasan kuka zata yi min, nikuma kukan ta yana tabamin zuciya, naji gobe in Allah ya kaimu zaku tafi garin su Ummi, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya “