ABDUL JALAL PART 2

Ta kara kankame shi tareda fadin
“I love you too, Zaujee”
Yadda tayi maganar yaji wani abu ya tsirga tundaga kansa har tafin kafarsa.
“Jalila Do you really mean what you say?”
Jinjina masa kai tayi
“I mean it zaujee, I love you”
Jalal yaja numfashi yace
“Kalamai masu girma dana dade ina expecting a gayamin, gayamin yaushe kika fara sona ne?”
Murmushi tayi tace
“hmm wani dogon zamani da ya wuce, da farko dai na dauka kishi ne da tausayi daga baya kawai aka shammaceni aka jani fagen soyayya”
Dariya Jalal yayi yace “waye ya jaki fagen soyayyar?”
“Mijina mana daya tamkar da dubu”
“dan Allah ki dan kara cewa kina sona mana”
“I love you Zaujee”
Ya dan kashe mata ido yace “dan kara fada mana”
“Anki din bazan sake fadan ba cikani in tafi”
Kara riketa yayi yana dariya, abu kaman wasa Jalila taji Jalal yana neman wuce gona da iri dan haka ta rike hannunsa, tareda kiran sunansa da dan karfi
“Jalal”
Ya bude idonsa yana kallon ta
“Dan Allah ka kyaleni ba fa a gida muke ba”
“Au a daji muke?”
Kaman zatayi kuka tace
“Ina nufin ba’a gidanmu muke ba, Yanzu Ummi zata iya nemana fa”
“Shikenan karkimin kuka Sarkin kuka, Amma Jalila yakamata mu koma gida fa, yaushe zamu koma?”
“duk lokacin da kake so”
Ya dan lumshe ido yace “ko yanzu?”
Jinjina masa kai tayi alamar eh
“Shikenan ki koma ciki, da safe Insha Allah zan shigo in gaida Ummi, ki shirya gobe zamu fita yawo”
“ina zamuje?”
“Allah ya kaimu gobe zaki gani, in kinyi Salla ki hau online”
Hararsa tayi
“bazan hau ba din, kuma ba yawon dazan bika, kusan sati biyu nayi a cikin damuwa da kewar ka, nima sena rama”
“Haba matar kiyi hakuri, banyi hakan da gangan ba, nasan dana bar wayata a kunne, kirana zakiyi tayi kina koke2, nikuma bana son inji kina kukan nan shiyasa, Allah yabaki hakuri”
Mikewa tayi ta dau mayafinta tace
“kaga na tafi seda safe” kafin yayi wata magana tai waje abunta.
Tana zuwa ta tarar Ummi tana sama ita da Maama a dakin Inna, dan haka kai tsaye dakin da sukw ta wuce taje ta tarar da su Hanan sunyi kwadan garri suna ci.
Tana shiga Hanan kalleta tace “lallai matar so, se yanzu?”
Jalila ta harareta tace “ban sani ba”
Nana tai dariya tace “Jalila ina Jan bakin?”
Cikin ko in kula tace “mun shanye abinmu”
Hanan tace “wallahi Jalila baki da kunya”
Jalila tace “har na kaiki rashin kunya, kudena gulmar nan ku maida kai kuci garrin kwakinku”
Nana tace “zakiga mu maida kai muci garri, kema zezo kanki ne”
Jalila tana idar da sallar isha’i tai Azkar, suka fara waya da Jalal.
Duk soyayyar da Jalila tayi Abaya yanzu take tabattar da shirme ce yanzi ta gane menene hakikanin soyayya, yanzu ta gane se yanzu ta shigo fagen soyayya, Jalal yana tarairayar ta da nuna mata tsantsar kulawa.
Da suka gama wayar ma da Jalal chatting suka koma yi, da kyar sukayi wa juna sallama suka kwanta.
Kusan kullum idan yamma tayi, su Jalal se sun dau matansa sunfita yawo.
Jalal seda ya kyale Jalila takara kwana goma da Ummi sannan yace yana son sukoma Gida, Nana da Hanan duk sun riga sun tafi.
Jalila tunda taji yace su tafi tasan ya mata kara, amma seda tayi kuka, ana gobe zasu tafi Ummi ta kirasu ta zauna da su taita musu nasiha a karshe tace
“Jalila ga amanar dana nan, ki kulamin dashi, kiyaye hakkokinsa ki guji abunda ze bata masa rai koya sa shi yin fushi”
Jalila ta dan tura baki tace
“to shi bazaki ce masa ga amana ta ba”?
Ummi tai murmushi “Jalila ai bazaki taba canza hali ba, ni Jalal ne dana dole in jadadda miki ki kulamin da shi”
Jalal ya dinga yi mata dariya, Jalila tace “Ummi wai bazaki bimu mu koma kano ba?”
Ummi tace
“in biku in muku me? Gidan mu zan koma nima, se an kwana biyu zanzo in ga dakinki, nidai fatana Allah ya zaunar mana daku lafiya a daku nan ku”
Sam ba haka Jalila ta so ba, nan da nan ta fara kuka, Gaba daya yanayin Jalal ya sauya ganin yadda Jalila ta fara kuka Ummi tace
“Jalal tashi ka tafi kyleta, gobe insha Allah zaku tafi”
Haka Jalal ya tashi ya tafi.
Washegari gurin karfe sha daya na safe suka baro Bauchi zuwa kano ba dan Jalila taso ba dan sam bata gaji da ganin Ummin nata ba, ta sha kuka sosai kafin su taho.
Bayan Azahar suka isa gida, Jalal ya tafi masallaci Dan la’asar ta gabato, ita kuma Jalila ta shiga gida da kayan su.
Ta bude Dakin ta ta shiga ta tarar da Akwatina a ciki, set uku blue, silver, da purple kowacce uku da kit.
Mamaki ne yakamata tareda tunanin waye ya kawo wannan kayan? Kuma na menene.
Bata taba su ba, ta ajiye kayan da suka dawo dasu, tai salla ta shiga gyaran gida, saboda duk yayi kura kusan wata guda kenan bakowa a ciki, ta share ko ina tai mopping ta wanke toilet da glasses na window harta gama tana tunanin kayan nan.
Seda akayi sallar magariba Jalal ya dawo hannunsa da ledoji, a parlor ya tarar da ita tana kallon zee world
“Waike ba kya gajiya ne, daga dawowarki kin tsiri aiki”
Batace komai ba se murmushi da tayi ta karbi kayan hannunsa
“ina ka tafine haka?”
“na tsaya nayi salla ne, sannan naje nayi mana siyayya abunda zamuci base kinyi girki ba”
Jalila ta dan numfasa tace “Akwatinan me ka ajiye a dakina?”
“Nakine na lefe ko ba suyi miki bane?”
“Amma Jalal….
Yatsan sa ya dora akan lips dinta yace
“Shhhh bana bukatar sharhi, tuhuma, ko godiya, a cigaba da yimin kwalliya kawai, babu bukatar kimin wata godiya dakko plate da cup muci Abinci”
Jiki a sanyaye ta dakko plate tazo ta ajiye ya zazzage ledar kaza ce da dogayen kwalayen madara, ya zuba a plate ya mika mata yace
“feed me”
Gaba daya ya lura a tsorace take da shi yau, da dane da yanzu watakila ta haye cinyarsa tana tsokanar sa, Amma yau ko kusa dashi taki zuwa karshe dai shi ya dinga bata amma taki ci se kyaleta yayi.
Bayan ta idar da sallar isha’i tai wanka ta haye gadon ta tai kwanciyar ta dan tana jin bacci sosai harta fara bacci taji an kunna wutar lantarkin dake Dakin ta, dan rintse ido tayi, sannan ta bude a hankali ta sauke akan Jalal
Murmushi yayi yace “shine yau ko azo muyi azkar din ko? To ni nazo muyi”
Janyo bargo tayi ta shige ta rufe har kanta ta dunkunkune, ba karamin dariya ta bashi ba, ya kashe fitilar ya hau kan gadon yace
“ni kike gudu haka ko Baby?, fitowa zakiyi”
Ya fara kokarin janye bargon nata,
“nifa bacci nake ji ka kyaleni”
Banza yayi mata seda ya cirota daga bargon, gaba daya Jikin ta yayi sanyi,
“Jalila ni kike gudu haka ko? Hada shigewa bargo, ance ana sona amma ana guduna haka akeyi, burina ya cika ummi na ta warke, Baby na ta hadu da Ummin ta, yakamata a tausayamin haka Baby na azabtu fa”
Haka yai ta mata surutai, Bata gama firgita ba seda taji abunda Jalal din ke kokarin yi ya shallake tunanin ta,
Yau dai Jalila baki ya mutu, ko kwakwaran motsi takasa se kuka da kiran Ummi, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunanin ta, seda Jalal fanshe soyayyar sa ta tsawon shekaru.
Kaman ba Jalal din nan me mugun jin kai da hade rai ba.
Bayan komai ya lafa Jalal ya rungume Jalila tsam a kirjinsa yana so yayi magana amma sam yakasa, a hankali taji jikinsa na daukar zafi fiye da kima, ganin yakasa magana yasa shi sakinta ya juya mata baya,
Ji tayi kamar ana girgiza gadon da suke kai, juyawa tayi taga jikin Jalal ne yake karkarwa, ta kai hannunta jikin sa taji kamar wanda aka hurawa wuta bata taba jin jikin dan adam yayi zafin haka ba.