ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣0️⃣113

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Da sauri ta janye hannunta daga jikinsa, da kyar ta mike zaune ta janyo rigarta ta saka, a hankali ta sakko daga kan gadon, dan duk wata gaba ta jikin ta ciwo take mata, ta kunna switch haske ya gauraye dakin gaba daya, ta kalli inda Jalal yake har yanzu karkarwa yake kamar wanda ake girgizawa, a hankali ta tako ta zauna a kusa da shi ta dan dora hannunta a goshin sa zafin karuwa yake fiye da farko, a hankali tace
“Jalal meyake damunka ne?”
Shiru yayi be ce komai ba, gaba daya jijiyoyin kansa kaman an kumbura su har jijiyoyin fuskarsa seda suka tashi, ta tashi ta debk ruwa a container da towel me kyai ta dinga tsoma towel din a ruwa tana shafa masa tareda karanto duk addu’ar da tazo bakin ta, bude ido yayi yana kallon ta, seda gaban ta ya fadi ganin idon sa yana caccanzawa kaman yadda ta taba gani yayi kwanakin baya, salati ta dingayi
“Jalal ko Daddy zan kira ne?” girgiza mata kai yayi ya mayar da idonsa ya lumshe, MP ta dakko ta kunna karatun Alqur’ani ta dora akan mirror.
Ta cigaba da shafa masa ruwa, a hankali jikin sa yafara sanyi ya fara sauke ajiyar zuciya alamar bacci ya dauke shi, seda ta tabbtar yayi bacci ta mike ta tafi toilet dan gyara jikin ta, ji take kaman zata fadi gaba daya jikin ta babu kwari, ga ciwo da jikin ta yake mata, ta gargasa jikinta da ruwan dumi ta fito ta canza kaya, ta koma gurin Jalal ga mamakinta taga ya mike zaune amma har yanzu idonsa wani iri, takarasa gabansa tace
“Sannu ya jikin naka?”
Kallon ta yayi yai shiruu kaman wanda akayi wa dole yace “zan sha giya”
“giya kuma? Amma kasan gidana ba club bane ko?”
Kokarin mikewa ya keyi tai sauri tace “tsaya ina kuma zakaje? Bari in dakko maka ai inada ita”
Ya nemi guri ya zauna, ta fita ta dakko zamzam ta dawo ta tarar ya kashimgida idonsa a lumshe tace
“bude bakinka” ba musu ya bude ta fara zuba masa zamzam din nan me dauke da tofin Al’qur’ani a ciki ya dinga sha ba tareda yasan menene ba, seda ya shanye shi tsaf kawai yafara Tari abu kaman wasa ya dinga tari kaman ze shide, zuwa jimawa kuma yafara amai, wani irin abu yake amayarwa baki kirin me kauri, tun Jalila na iya gogewa ta gyara gurin harta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, ta koma gefe ta zuba masa ido tana hawaye.

Seda Jalal ya kusa fita hayyacinsa gaba daya, ya dinga aman nan ba kakkautawa, sedai in yayi yayi, ta goge, yayi awa yana aman nan baya hutawar minti biyar beyi wani aman ba.

Ba Jalal ba hatta Jalila ta galabaita, ga wahalar da ta sha a hannun Jalal shikuma ga wannan rashin lafiyar, da aman ya dan lafa masa ta dakko zuma ta dinga bashi da spoon yana karba.

A hankali ta kira sunan sa “Zaujee” juyo yayi ya Kalle ta idonsa ya koma normal yace “Na’am my love”

“ya jikin naka? Kana jin wani aman ne?”
Girgiza mata kai yayi yace

“A’a bana jin aman yanzu”

“Masha Allah, yanzu yakamata kaje kayi wanka”

Ya Kalle ta ya dan kashe mata ido yace “wankan me zanyi?”
Jalal kenan yana fama da kansa amma tsokanar Jalila yake, ta tura baki tace
“nima ban sani ba”
Murmushi yayi yai kokarin mikewa amma yaji jira yana dibarsa, ya dake ya dafa bango, cikeda damuwa Jalila tace

“Zaujee anya bazamu tafi Asibiti ba kuwa? Na tsorata da abunda ya sameka fa”

“ba se munje ko’ina ba aina warke, karki damu zan shiga inyi wankan im fito”

Haka ya dake ya nufi toilet, Amma gaba daya jinsa yake wani iri garin yana juya masa, kan ya fito Jalila ta tattara kayan da ya bata da amai ta tafi toilet din parlor ta wanke su tas, ta canza bedsheet ta dakko masa wasu kayan, ta kunna burner ta saka turaren wuta saboda karnin aman da yayi, Jalal ya jima a toilet be fito ba, dan yana shiga toilet din yaji wani aman, ya kunna shower yadda Jalila bazataji karar aman da yake ba, gaba daya tausayin ta yake ji, be so wannan dare yazo musu a haka ba, wannan karon hadda jini a cikin aman da yayi.

Jin shirun yayi yawa yasa Jalila tazo kofar toilet din tai knocking tare da fadin
“Zaujee ya na jika shiru ne? Lafiya dai ko?”
Ya galabai ta amma cikin karfin hali yace

“lafiya kalau, kiyi kwanciyar ki yanzu zan fito”

Maimakon ta kwanta guri ta samu ta zauna a bakin gado tana jiran sa, seda aka jima sannan ya murda kofar toilet din ya fito jikinsa daure da towel, da sairi ta nufo shi tace

“Jalal Allah yasa ba aman ka kuma yi ba, gaba daya kammaninka sun canza dare dayan nan baka ga yadda ka rame ba”

Dan Murmushi yayi mata yace “Ashe haka ake sona aka damu dani, nace karki damu ban kuma aman ba ai, wanka nayi na fito”

Haka ta kyaleshi ba dan ta yadda ba, ya tsane jikin sa ya dauki jallabiyar da ta dakko masa ya saka, ya haye kan gado amma ga mamakin ta ya kai hannu ya kashe MP din da amon karatun Al’qur’ani ke tashi.

Kallon sa tayi cike da mamaki tace

“ya haka kuma? Meyasa ka kashe?”

“Naki nake son ji, ke zaki karanta min da sautin muryarki me narkamin zuciya ya sani nutauwa har inyi bacci”

Jalila idon ta har mannewa yake saboda tsabar gajiya da baccin da take ji, Amma haka Jalal ya kwanta a jikin ta, ta fara rero karatun Al’qur’ani cikin suratul Ibrahim da muryarta me dadin sauraro, ta nayi tana shafa sumar kansa.
lumshe ido yayi yana sauraron ta, bacci ne ya dauke Jalal, Abunda ya firgita Jalila be wuce ganin hayaki na fitowa daga hancin Jalal ba.
“Innalillahi wa inna ialaihi raji’un” shine abunda Jalila keta nana tawa, ta shiga jero dukkan Addua da ta zo bakin ta, shikam Jalal kara kankame ta yayi yana baccin sa.
A hankali hayakin ya dena fita, mamaki ne ya cika Jalila, ta yaya Hayaki ze dinga fitowa daga jikin dan adam haka? Tana cikin tunanin ne bacci barawo yayi awon gaba da ita ba tareda ta shirya hakan ba.

Ko da Asuba Jalal ne ya tasheta daga bacci, da kyar Jalila ta iya tashi tai salla, da ta idar da sallar ko Addua ba tayi ba ta kwanta akan sallaya ta cigaba da bacci, seda Jalal ya dawo ya same ta akan dadduma a kwance tana bacci, carbin hannun ta ya zare wanda hakan ya sata bude ido Jalal yace
“kin kwanta a kasa se wuyanki yayi ciwo ko? Tashi muje ki kwanta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button