ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Hamma tayi tareda yin miki cikin muryar kasala da jin bacci tace
“Zaujee ya jiki?”

“Aina warke ni, kece baki da lafiya tashi muje ki kwanta”

Mikewa tayi Jalal ya rike ta ya cire mata hijjabin, har kan gado ya kaita ya kwantar da ita, tana kwanciya bacci ya kuma dauke ta, zama Jalal yayi ya kura mata ido, gaba daya tausayin ta ya kama shi, ta sha wahala sosai, dan murmushi Jalal yayi yace

“Babyn Ummi ta girma, Allah karka bani ikon cutar da wannan baiwar taka ko da kiftawar ido”

Ya rungume ta a jikin sa yana shafa gashin kanta.

Ilham kam kwanan ta biyu bata gida, ta cewa Mummy za taje gidan su, Amma ba gidan ta tafi ba gurin malamin da umman ta kwatanta mata, can boarder tsakanin Nigeria da kamaru, a can ne malamin da ya yiwa Jalal Asiri yake, taita bugun cikin umman nata tana bata Labari, ta shirya ta tafi.

Mummyn Jalal tana zaune tana breakfast aka kira ta a waya, daga wa tayi tareda yin sallama
“salamu Alaikum dan Allah Hajiya khadija ce?”

Mummy tace “eh nice”

“Dama Umman Ilham ce aka wayi gari takasa tafiya, bakin ta ya karkace an kaita Asibiti amma babu kowa a gurin ta”

“Subhanallah, ina Ilham din?”

Me kiran wayar tace “Ilham bata nan”

Mummy tace “shikenan nagode”

Gaba daya jikin Mummy rawa yake yi, ta tafi part din daddy bacci yake ko farkawa beyi ba ta tashe shi.

Daddy ya tashi yace “deeja lafiya kuwa? Yana ganki a haka?”

Cikin damuwa tace “Daddy, Saudat na Asibiti wai ba ta iya tafiya bakin ta ya karkace”

“Subhanallah wani Asibitin ne?”

“Nima ban sani ba sedai muje mu gani”

Haka suka shirya suka tafi gidan Saudat daga can aka gaya musu Asibitin da take suka tafi.

Koda sukaje Asibitin idonta biyu an sama ta ruwa, bakin ta ya karkace se zubar da yawu take, fuskarta duk ta kumbura, ta kara duhu kafafun ta kamar an shanye, gaba daya halittun ta sun sauya kamar ba ita ba.

Khadija na ganin ta ta fa she da kuka tana fadin “Saudat meye sameki haka? Garin yaya haka ta faru dake?”

Babu baki sedai ido da take binsu da shi, Mummy tai kuka har idon ta yayi jawur. Daddy ne ya dinga rarrashin ta
Yace
“Wai ina Ilham ne?”
Se a lokacin Mummy ta tuna bata ga Ilham ba, waya ta dakko ta kira Ilham, ta kira ya kai sau biyar sannan ta dauka
Mummy tace “Ilham kina ina ne?”

“ina gidan mu mana”

A fusace Mummy tace “karya kikeyi, gamu a Asibiti tare da Mahaifiyar ki an kwantar da ita ba lafiya”

Da sauri Ilham tace “na shiga uku, Meya same ta?”

“ban sani ba, gidan ubanwa kika tafi”

Kuka Ilham ta fara yi tana fadin “shikenan na makara, dan Allah meya same ta?”

“in kinzo kya gani”

Se shadaya na safe Jalila tai juyi ta farka daga bacci da sauri ta sakko daga kan gado tana fadin
“Subhanallah” Jalal baya dakin ya fita
Toilet ta tafi tai wanka tai brush, ta fito ta gyara gadon sannan ta fito parlor.

Koda ta fito Jalal yana danna waya ya dago ya kalle ta yayi murmushi, seda ta dan tsorata da ganin Jalal, ya rame sosai idonsa yayi zuru zuru, Jalal ya taso ya riko hannun ta zuwa kan kujera, ya zaunar da ita yace

“good morning my Angel, ya jiki?”

Dan murmushi tayi tace
“Lafiya ta kalau ai kai zanyi wa ya jiki?”

“Kin tabattar lafiyar ki kalau?” yai maganar yana kashe mata ido.

Tura baki tayi

“ni cikanizaka canza min magana, baka tashe ni ba gashi rana tayi bamuyi breakfast ba, ya kake ji a jikin ka yanzu ka rame sosai wallahi, na damu sosai da halin da ka shiga jiya”

Jalal yace

“gani nan dai wallahi Jalila ji nake kaman bacci nayi na tashi, gani nake duk abunda ya faru a baya kamar a mafarki, kamaman an sauke min wani nannauyan abu da yake rinjaya ta a kaina, ko kuma dutse haka nake ji”

Jalila ta rike hannunsa tace

“Jalal yakamata mu tashi tsaye anema maka magani, nifa jiya hayaki na gani yana fitowa daga hancin ka fa”

“Hayaki kuma?” ya tambaye ta

“Eh hayaki, hayaki nagani yana fita daga hancin ka jiya kana bacci”

Jalal ya kyalkyale da dariya yace

“i see that you enjoyed yesterday night, bacci ya miki dadi in ba haka ba ta yaya hayaki ze fita a hanci na, mafarki kikayi”

Jalila kaman za tai kuka tace
“Jalal ba fa abun wasa bane”

Ya dan Harare ta yace
“bazaki dena cemin Jalal ba ko?”

“Yi hakuri bazan kara ba, Amma ka dau magana ta da mahimmanci”

“Jalila ki kyaleni da maganar na, yanzu na dafa tea na siyo bread bari in dakko muyi breakfast”

Riko hannun sa tayi tace

“To ko Asibiti muje a dubamin kai, ka rame da yawa jiya ka sha wahala sosai, ni nayi mamaki ma da ka iya tashi har kake harkokin ka”

Dan noke kafada yayi kaman wani karamin yaro yace

“Kece likita na ai, ni ba Asibitin da zanje lafiya kalau nake jin jikina, bayan abunda ya shiga tskanin mu ji nake kaman nasamu wani immunity ne daga gareki, gayamin meye sirrin”

Hannayen ta biyu tasa ta rufe fuskarta tace

“dan Allah ka dena wannan zancen, ni ka dakko mana kayan breakfast din ni yunwa nake ji”

“Dole inyi wannan zancen, Jalila ba haka naso daren jiya ya zo mana ba, Amma babu yadda muka iya da kaddara, A koda yaushe kokarin ki shine ganin kin tabattar da farinciki a cikin rayuwa ta, dukda yanayin da kika kasance a jiya be hanaki nuna tausayi da jin kai a gareni ba, Jalila ” ya karasa maganar da kiran sunan ta, ta dago ta Kalle shi

“Allah ya saki a madaukakiyar Aljannah, kada Allah ya kawo second din dan zan cutar da ke a rayuwa ta, ina kaunar ki Jalila”

Ta amsa da “Ameen”

Ya kai bakinsa kunnen ta yace

“you deserve a gift from me in return of what you gave me yesterday”

Idan har ta biye wa Jalal ba zasu karya ba, gashi yanzu sha biyu saura, ba shida niyyar sassauta kalaman da yake zubowa, ture shi tayi ta mike taje ta hado kayan breakfast ta ajiye a gabansa.

Haka sukayi breakfast cike da nishadi da kaunar juna.

A haka cikin hirar ta su, Jalila take bashi labarin irin miyagun mafarkan da ta dinga yi akan sa a lokutan baya.
Jalal ya sha mamaki yace

“that’s why I said our souls are destined to be together, ke garkuwa ce ga ABDUL JALAL”

Wayar sa ce ta fara ringing, ya sa hannu ya dauka
Muryar Daddy yaji dan haka ya kara nutauwa suka gaisa.
Daddy yace

“Jalal muna Asibiti fa”

“Asibiti kuma Daddy waye ba lafiya?”

“maman Ilham ce, bata da lafiya sosai bata san waye akan ta ba, yakamata in ka samu lokaci kuzo ku duba ta”

Jalal yace

“Allah ya bata lafiya Amma bazan zo ba”

Daddy yace “Jalal meya sa kake hakane? Narasa me baiwar Allah nan tayi maka ka tsane ta, rashin lafiya ce kuma bata wuce kan kowa ba, At least in kazo ka duba ta mamanka ma zata ji dadi, tunda muka zo ta kasa sakewa tana ta kuka ne”

“Daddy idan fa nazo bani zan bata lafiya ba, kuma bani na dora mata ba, meye dole sena zo, nima bani da lafiya fa, dan Allah kayi hakuri kayi mata sannu Allah ya sawwake”

Jalal ya kashe wayar sa, girgiza kai Daddy yayi yace

“Allah ya shirya”

Mummy dake gefe tace “Kaima kasan baze zo ba, da dai kanwar uwar Jalila ce ze tafi ko bangon duniya ne a kafa, ai na riga nasa masa ido yaje yayi abunda ya ga dama tunda bani da mutunci a idonsa, na barwa Jalila shi dadi mata yaje yai duk abunda yake so kafin in waiwayeshi”

Daddy yace

“deeja bana son wannan maganganun da kike yi fa, ina ruwan Jalila a cikin wannan abun? Naga tun kafin ya auri Jalila basa wani jituwa da Ilham da mahaifiyar ta, kuma in kikayi hakuri watakila kiga yazo, amma be kamata komai Jalal yayi ki dora alhakin akan matarsa ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button