ABDUL JALAL PART 2

“Eh dole kace haka mana tunda kai ka aura masa ita, da Ilham ya aura nasan duk wannan bakin cikin da ban ganshi ba, yanzu se ‘yar mulki taga dama tasa baki sannan zezo”
Mikewa Daddy yayi yace “Sekuma kiyi ke ka dai, ni zan wuce gida”
Dauke kai tayi tai masa banza har ya fice daga Dakin
Jalila tace “Zaujee waye ba lafiya ne?”
Dan bata rai yayi yace “wai babar su Ilham, shi kuma Daddy wai inje in duba ta, in duba ta ince mata me? Nima ba lafiyar ce dani ba ai”
“haba Zaujee meye a ciki dan munje mun duba ta? Dan Allah zakayi kuma Mummy zataji dadi, Akwai lada me yawa a ziyarar mara lafiya, karka duba wai tayi maka wani laifi kowani abu ka duba girman Allah da manzon sa, duba mara lafiya umarnin manzon Allah ne salallahu alaihi wassalam, kuma koyi da sunnar sa ne, zuwan ka da rashin zuwan ka baze canza komai ba, Amma mara lafiya zeji dadi kai kuma zaka samu lada”
“idan na dau carbi ma kona karanta Al’qur’ani zan samu lada”
Jalila tai murmushi tace
“Annabi salallahu alaihi wassalam yasan da hakan yace muyi zumunci, kuma yace muje ziyarar mara lafiya, please Zaujee ko minti kadan ne muje a duba ta”
“to naji amma se nayi shawara”
“haba mijin so be kamata kayi jinkiri a aikin lada ba, a temaka zuwa gobe in Allah ya kaimu muje”
“shikenan Allah ya kaimu goben lafiya”
“Ameen ya Allah, ko kai fa har naji dadi”
Mummy duk ta sanar da ‘yan uwa abunda ya faru, ana ta zuwa duba ta, Se bayan isha’i Ilham tazo Asibitin nan, gaba daya ran Mummy ya gama baci, Ilham na zuwa Mummy ta rufe ta da fada
“wai daga gidan ubanwa kike? Tun jiya mahaifiyar ki bata da lafiya amma ba kya gida, ina kika tafi?”
Ko sauraron Mummy Ilham ba tayi ba ta nufi gadon da Umman ta ke kwance, tana zuwa taga yadda kamanin Umman ta suka koma, ja da baya tayi ta fasa ihu tana fadin
“Innalillahi wa inna ialaihi raji’un, munshiga uku, wayyo Allah na umma meya sameki haka? Shikenan komai ya warware a haka zaki zauna kenan? Na shiga uku Umma na”
Mummy tace
“Ilham kiyi hakuri mana, dare ya fara yi ga marasa lafiya kiyi hakuri, likitoci sun bada tasa tasai duk anyi amma sunce basu ga komai ba, ni ban san meya same ta haka ba”
Banza Ilham tai mata ta cigaba da kurwa tana surutai. Wajen goma Mummy ta tafi gida, ta bar kanwar Saudat da Ilham a gurin ta.
Da safe Jalila ta lallaba Jalal suka shirya suka tafi Asibiti domin su duba mahaifiyar Ilham.
Da sukaje Asibitin Jalal ya kira Daddy a waya ya kwatanta masa dakin da aka kwantar ds ita, koda sukaje Daddy yana nan ya kai Mummy be tafi ba.
Mummy na ganinsu ta hade rai kaman bata san wani abu dariya ba, Jalila tana gaisheta amma ta dauke kai.
Jalila ta gaida Daddy sannan suka gaisa da ‘yan uwan Mummy dake dakin
Jalal ya nemi guri ya zauna ya dora kafa daya kan daya ba tareda ya kula kowa ba yace
“Mummy ya me jiki?”
Daga ido Mummy tayi ta kalleshi tace
“Uwar taka ta barka kazo kenan?”
“wa kenan”? Jalal ya tambaya
“Matar ka mana”
Cikin ko in kula Jalal yace
“Badan Jalila ta takura ba babu abunda zesa inzo duba wannan matar wallahi, Allah ne ya tashi kamata shiyasa ya maida ita haka”
Daddy yace
“deeja bana son irin wannan abubuwan, daga zuwa dubiya kin fara surutai ga mara lafiya a kwance”
Daddy na cikin fadan ne Ilham ta shigo dakin hannun ta dauke da ledar pharmacy, tana ganin su Jalila tayi jife da ledar ta nufi Jalila tana zazzaro ido tana magana cikin ihu Jalal yai maza ya mike yasa Jalila a bayan sa
“Wallahi baki isa ba Jalila saboda ke koma meye ya samu mahaifiya ta, wallahi kema bazaki rayu cikin dadin rai ba sekin wulakanta kuma sena ciki burin mahaifiya ta koda hakan yana nufin rasa raina”
Jalila ta fito daga bayan Jalal tace
“Ilham har yanzu baki hankalta ba ko? Abunda ya sameki be zama darasi a gareku ba? Ashe kuwa zaki kare rayuwar ki a wahala, zuwa yanzu ya kamata ki san baki da abunda zaki iyayi ki cutar dani, wallahi Ilham na miki zarra kuma na riga na miki illa, ya rage naku ku nemi yafiyar wanda kuka cutar, ko Allah ya sassauta muku wannan iftila’in, bakar aniyarki da ta mahaifiyar ki ce ta koma kanku, yanzu seki dau damarar zaman jinya, dama shi Allah ba Azzalumin sarki bane”
Cikin ihu Ilham tace “wallahi karya kike kiyi galaba akaina, sena kasheki na kashe Jalal din”
Jalila tace “sedai ki kashe kanki, Allah maji rokon bawa, Allah be bar gwagwarmayar da nayi a banza ba, Allah ya shiryi mijina kuma ina miki albishir da abunda kukayi masa ya bar shi”
Ganin Jalila ta fara daukar zafi yasa Jalal janye hannun matar sa sukayi waje.
Mummy da Sauran ‘yan uwansu da ke dakin kam daskarewa sukayi suna mamakin irin musayar kalaman da suka shiga tsakanin Ilham da matar Jalal me hakan ke nufi?
Mummy tace “Wai Ilham ban gane inda maganganun nan suka dosa ba?”
A fusace Ilham tace “dalla malama khaleni, kece silar komai, kece sanadiyar shigar mahaifiya ta wannan halin wallahi bazan yafe miki ba makira maci amana, kuma wallahi kema sekin ga yadda karshenki ze kasance.
Wata Jaka Ilham ta dakko a cikin jakar ta ta zazzage a gurin, layu ne da wasu tarkacen kayan shirka hada bawan kwai dauke da sunan ABDUL JALAL
Share please
07063065680 What’s App only
Watpad Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????
ABDUL JALAL
Story, writing and edited
By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)
PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????
(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
PART 2
_PAGE 6️⃣1️⃣115
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724
_MY FIRST NOVEL _
Mummy tace “kai gidan Jalal fa nace zaka kaini”
Driver ya ƙara risina kai yace “eh Hajiya shi din fa, Jiya da daddare yazo layin nan shida matarsa, yace inje in kaisu filin jirgi yau, ɗazu na dawo daga kaisu”
Bata tsaya ta ƙarasa ji ba ta koma cikin gida kirjin ta yayi mata nauyi take tambayar kanta
“wace irin tsana Jalal yayi min har yazo layin nan ya tafi be ganni ba, be leƙo mun gaisa ba? Yazo shida matarsa suje gidan su matar sa amma suka kasa shiga su gaisheta, take ta kara jin wata muguwar tsanar Jalila tasan tabbas wannan makircin Jalila ne”
Da ta sake tuna cewar Daddy zeyi aure setaji gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi, tarasa me yake damun ta, kowa ya guje ta ya juya mata baya ciki hada dan cikin ta, ga dukiya tari guda, dukiyar da take ta hari tana kwaɗayi gata nan a jibge amma sam yanzu hankalinta ba’a kan dukiyar yake ba, da anjima kuma idan ta sake tuna irin masifar shaye2 da Jalal yayi, da yadda take riƙe da Ilham kaman ita ta haifeta ta tuna Abunda Saudat ta aikata mata se taji kaman a duk duniya ita ka ɗai aka tsana tarasa me zatayi taji daɗi, bacci ya ƙauracewa idanun ta, bata jin yunwa ma balle tasaka ran zata ci Abinci, idan tasa Abinci a gabanta za taci kuwa ji take babu test babu daɗi, bata da aiki se tunani da koke koke, Ankwace mata miji, wata ta kwace mata ɗanta ɗaya tilo se yadda tayi da shi, gashi ‘yar uwatta data yadda da ita taci amanar ta tayi mata cutarwa mafi muni, ga ba wanda yake son rabarta saboda izzarta da jin kai da wulaƙanta mutane, nan da nan abubuwa sukayi mata yawa, ta fara fama da wani matsanancin ciwon kai da yake sakkowa har wuyan ta ko gani bata iyayi sosai, tunda Daddy ya tafi ko message be mata ba balle ya kira ta, saɓanin da da idan ya tafi se suyi waya sau biyu zuwa uku, yanzu ya tattara ta ya watsar ya shiga harkokin sa da shirye shiryen maida Auren sa.