ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

7 hours cif su Jalila suka shafe ana tafiya a jirgi sannan suka isa London babban birnin England, Jalila ta gaji sosai tun ana tafiyar ta marmari tazo ta gaji, ta fara yamutsa fuska daga karshe ta kwanta a jikin Jalal tai bacci.

Jalal ya tashe ta suka sakko daga jirgin, yanayin weather garin ce ta tabattar mata lallai ta baro Nigeria, wani irin sanyi ne me ratsa jiki taji yana dukan ta, ta ɗaga kai tana kallon yanayin garin dukda dare ne amma tasan akwai banbanci da gida Nigeria, komai nasu cikin nutauwa da tsari, bayan sun gama clearing komai Jalal ya ja hannun ta sukayi gaba, wajen wata mota suka nufa kafin su karasa inda motar take aka bude motar na cikin motar ya fito.
Mahmud ne mijin Nana yazo ɗaukar su.
Cikin fara’a yace “Sannunku da zuwa bros nasan kun sha hanya, da ganin idon Jalila a gajiye take”

Jalal yace “wallahi kuwa a gajiye take sosai, muje ka kaimu gida seta huta gaba ɗaya”

Seda suka shiga motar sannan Jalila ta samu damar gaisawa da Mahmud har take tambayar sa Nana, dan a gajiye take sosai ga sanyi da a take ji gaba ɗaya ta dunƙule guri ɗaya a jikin Jalal.

Ya kaisu gidan daya kasance nan ne masaukin su, ya kawo musu Abinci daga gidansa sannan yai musu sallama ya tafi.

Jalila dai wanka tayi da ruwa me zafi ta shafe jikin ta da mai tasa ka kayan sanyi dan ta rage sanyin da take ji, shikam Jalal ko a jikin sa dan shi ya saba.

Lumshe ido yaga tana yi alamun bacci take ji

Yace “matar yakamata kici Abinci kafin kiyi bacci”

Tayi miƙa tare da tura baki gaba tace “ni ka nunamin ɗakina bacci nake ji”

“A waje zaki kwana idan baki ci Abinci ba”
Ya takura mata ya zuba Abinci ya zauna ya fara bata a baki, ji tayi gaba ɗaya Abincin babu daɗi, amma ta daure kar Jalal yaji babu daɗi taci kaɗan tace ta ƙoshi, shima be wani ci dayawa ba ya ajiye sukayi shirin kwanciya.
A zaton Jalila Jalal ze saurara mata ganin gajiyar tafiya da suka sha, amma tun a lokacin ya fara nasa honeymoon din, da ƙyar ta samu tai bacci Jalal ya tara mata wata gajiyar da bata shirya mata ba.

Abun mamaki Jalila se juyi tayi taga Jalal baya ɗakin, tsoro ne ya kamata ta tashi zaune tana rarraba ido, can se gashi ya shigo ya dube ta yace

“ba’a yin salla ne? Ko baki san Asuba tayi ba?”

Cikin tsiwa tace “Eh bana yi shiyasa jiya ka….” se kuma tayi shiru, dariya Jalal yayi yace
“ƙarasa mana, ya kika yi shiru?”

Ta ɗan murguɗa baki tace “bazan ƙarasa ɗin ba, Amma dan Allah ina kaje ne? Nifa har na tsorata”

“Sarkin tsoro, naje masallaci ne”

“Masallaci kuma? Dama akwai masallaci a wannan ƙasashen”

“Akwai masallaci hada na juma’a, ai suna da musulmi suma, akwai musulmi sosai a unguwar nan”

Jinjina masa kai tayi ta sakko taje tayi alwala tazo ta tayarda sallar Asuba.

Gari yayi haske sosai amma Jalila ba ta dena jin sanyi ba har yanzu, Yanzu ma Mahmud ne ya kawo musu Abincin safe suka gaisa sannan ya tafi, da Jalila ta fito tana kallon yanayin tsaruwar gidan, ba irin fasalin gidajen mu ne na Nigeria ba, hotunan Hajiya Salma ta gani a falon da su Mahmud tace “Zauje nan gidan Anty Salma ne?”

“Eh gidan ta ne, a nan Ummi tayi jinya ma gidan mijinta ne da ya rasu, Lokacin da yayi jakadanci anan aka bashi wannan gidan”

Jalila ta jinjina kai tace “to yana ga ban ganta ba?”

“ta tafi Maiduguri, Ranar Friday za’a maida Auren ta da Daddy, zata koma can Dubai gurin Daddy”

Jiki a sanyaye Jalila tace “dama dagaskene Daddy ze maida Auren nan? Allah sarki Mummy koya za taji? Dama baka bawa Daddy wannan shawarar ba, da ka bari da kansa in yayi niyya ya maida ita”

“Baby look, Daddy yayi haƙuri a zamansa da mahaifiya ta ni na sani, girma ya fara kama shi ya kamata ace ya huta, Mummy mahaifiya ta ce, Amma Soyayya kawai ta iya amma bata san wani abu respect ba, kuma Ya kamata Daddy ya maida Anty Salma saboda hakan shine dai2, yana son ta har yanzu, ko kin manta tun farko gidan tane Mummy ta shiga ta fidda ita? “

“Hakane Zaujee, Amma kishi babu daɗi, akwai ciwo me raɗaɗi”

“Jalila karki zama me son kai ban sanki da haka ba, Mummy a yanzu bata bukatar a tausaya mata, kamata yayi ta karɓi horo akan abunda ta aikata daga duniya”

“A’a zaujee, Macen da ta rasa soyayya da biyayyar ɗanta ya kamata a tausaya mata, please zaujee ka yafewa Mummy ka bata haƙƙinta na mahaifiyarka”

Ɗan lumshe ido Jalal yayi ya buɗe yace “Jalila a shirye nake da na karɓi mahaifiya ta in danne zuciya ta in manta da abunda ya wuce, Amma Abunda nake nuna miki har yanzu Mummy ba ta ɗau darasi ba, yanzu ina raɓarta zata fara kawo min abubuwa na son zuciya ta tursasni tace se nayi, ni kuma bazan biye wa son zuciyar ta ba, Jalila duk lalacewar ɗa yasan uwar sa, ko lokacin da nake shaye2 ina kaunar mahaifiya ta halayen ta ne bana so, sune suke ɓata min rai, halayen ta ne suka sa nake gudun ta ko inda take bana son zuwa, ko yau Mummy ta dena halayen ta marasa kyau zan mata biyayya, sedai bazanyi biyayya ga abunda nasan ze cutar dani ba”

Jalila ta yunƙura za tayi magana Jalal ya katse ta ta hanyar ɗora yatsan sa akan lips ɗinta yace “bana son jin wata magana, muci Abinci”

Haka Jalila tayi shiru ta kyaleshi.

Seda suka kwana huɗu sannan Jalal ya kai Jalila gidan Nana, babu nisa da inda suke da ƙafa sukaje. Nana tayi matuƙar farincikin ganin su, da ƙyar Nana take tafiya cikin ta yayi nauyi sosai.
Nana tace “Yaya Jalal tun ranar da kuka zo nake zuba ido amma baku zo ba se yau”

Jalal yace “yanzunma ba daɗewa zamuyi ba kuje minti biyar kawai ku gaisa zamu koma gida”

Mahmud yace “Haba dai brother ai ba zamu cinye maka ita ba” yai maganar yana murmushi

Suka dinga hira kaman wanda suka yi shekaru basu haɗu ba. Jalal da kansa ya bawa Mahmud labarin abunda ya faru a Nigeria. Nana ta kaɗu da jin abunda Ilham sukayi ita da Mahaifiyarta, Nana tace

“Allah sarki ashe shiyasa bata son Jalila ta tsane ta, kullum cikin faɗa suke”

Mahmud yace “Ai brother ka Auna Arziki, dama da mamaki ace lokaci ɗaya fa ka canza gaba ɗaya aka kasa gane kanka kasha wahala”

Jalal yace “munsha wahala dai, dani da Jawwad da Jalila, wato idan ina tuna wasu abubuwan da Jawwad yayi min a rayuwa har tunani nake anya Jawwad ba waliyyi bane? Jawwad ya wuce aboki a gurina, jinsa nake tamkar wani ɓangare na rayuwa ta, ya bani gudunmuwa a rayuwa ta, uwa uba matar so ‘yar Aljanna wato wani abun idan na kalle ta har mamaki nake yi a ƙarancin shekarun ta ba kowace ƙwaƙwalwa ce zata iya tunani irin nata ba”

Sun sha hira sosai wuni sukayi a gidan Nana se dare suka tattaka suka koma nasu gidan.

Zuwansu ƙasar nan ba karamin yiwa ma’auratan daɗi yayi ba, suna more soyayya yadda suke so, Jalal ya kai ta gurare da dama na shaƙatawa da buɗe ido, wata irin soyayya yake nuna mata me cike da ban sha’awa, yayin da ita ma take dukkan ƙoƙarin ta gurin ganin ta faranta masa rai, gaba ɗaya sun manta da damuwar da suka baro a Nigeria, babban abunda yake damun Jalila be wuce yadda ba ko yaushe take samun irin Abincin da take so ba.

Kamar yadda Daddy ya faɗa ranar Friday ya maida Auren sa da Hajiya Salma, Mummy tana kwance tana fama da kanta wata ƙawarta wadda tasan wasu a family su Daddy ta kira ta, ta sanar da ita Auren Daddy hada bata labarin abunda Jalal da danginsa sukayi wa mahaifiyar Jalila ai Mummy bata gama jin kanun labaran ba ta ajiye wayar ta miƙe zaune, kamar wata mara hankali ta kuma Janyo wayar ta hau danna lamabar Jalal amma seta tuna ba zata shiga ba tunda baya ƙasar, kenan ta tabbata Daddy yayi aure? Ji tayi numfashin ta yana sama yana ƙasa kaman ze ɗauke gaba ɗaya, ta lalubi wayar ta ta kira likita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button